09/09/2023
YASHA ADDU'A DAGA BAKIN DA BAYA KUSKURE - (Sallahu alaihi Wasallama) 💚
Watarana Manzon Allah yayi karatu kowa ya tafi wajen neman sa, wasu kuma sun tafi gona, sai Abu Huraira (r) ya rage a zaune, sai Manzon Allah (SAW) yace Ya Abu Huraira yaya kowa ya tafi nema, wasu sun tafi gona Kaikuma baka tafi ba, menene matsalar? Sai Abu Huraira yace Ya Rasulullah, akwai abinda yake damuna tsawon lokaci, idan kana mana karatu ina fahimta sosai, kuma har inaji kamar nima zan iya karantarwa, amma da zaran ka gama ka tafi to Shikenan ka tafi da fahimtar nawa, saboda babu abinda nake iya tunawa, tabbas lamarin yana damuna kuma yana tayarmin da hankali matuƙa, wannan shine abinda ya zaunar dani domin na gaya maka Ya Rasulullah (SAW)!
Sai Manzon Allah (SAW) yace masa matso, sai Abu Huraira ya matso, sai Manzon Allah ya dafa ƙirjinsa yace Ya Ubangiji ka bawa Abu Huraira fahimtar Addini, ka zaunar masa da iliminsa, kasa ya zama me fahimta, kuma ka Albarkaci abinda ya koya kuma ya koyar, sannan kayi masa nisan kwana, Allahu Akbar.
Abu Huraira bai sake mantuwa ba, kuma bai bar duniya ba sanda yafi kowa ruwaito hadisan Manzon Allah, sannan kuma yayi nisan kwana sosai, kuma Sahabbai s**ace idan yana karantar dasu sai suga kamar Annabine yake koya musu karatu saboda tsaban yadda yake koyi da Manzon Allah (SAW), daga ƙarshema sanda yazama idan Annabi bayanan kokuma zaije wani uzuri sai yace ai kuna da malami shine Abu Huraira, Ya Ubangiji kayi mana ilimi me amfani kuma kasa masa Albarka, sannan kada ka kashemu har sai ka yarda damu. Kada ku manta kuyimin sharing, sadakane gareku!
Bilal Omar Baba Gombe ✍️