17/12/2023
TARIHIN IZALA DAGA KAI HAR WUTSIYA 5.
3.1 GUMI DAGA AKIDA SAHIHA ZUWA KAFA IZALA.
Sheikh Abubakar Mahamud Gumi ya rubuta littafinsa ' Al-Akida Al-Sahihah ' a 1972 ya bawa Mallam Galadanci wanda memba ne a kungiyar malaman jami'a dake Kano don yin tishin nazari sannan ya kai shi Syrian publisher dake Saudi Arabia don buga shi.
Ya tattauna Dukkannin kalubalan da yake da su aka Dariku da sufaye a cikinsa. kamar su ; Haduwa da Annabi Sallahu Alaihi Wasallam da karyar wata addu'a daga wajansa, ya musanta yin katabus da sufaye zasu yi a ranar kiyama, buga mandiri cikin Masallaci.
A dai cikin littafin ya karya maganar Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ya wanzuwa a raye yayi tarayya da wani mutum har ya ba shi wani zikiri ko salati. Sannan ya musanta cewa karanta Salatil Fatih yana daidai da karanta kur'ani sau dubu shida.
Hallau ya tattauna akan Bidi'a, ya ayyana ta a dukkan wani aiki da sunan musulinci da ya sha-bam-bam da kur'ani da koyarwar Annabi.
Sheikh Abubakar Mahamud Gumi bai buga littafinsa don al'umma baki daya amma bayan tafiyarsa Saudi Arabia dalibinsa Isma'ila Idiris ya soma karantar da shi hakan ya haifar da ka-ce-na-ce a gidajen yada labarai , jagororin Dariku su ka soma kare darikunsu ta wannan hanyar da rubuce-rubuce dukkan su Tijjaniya da Kadiriya sun yi rubutu misali daga cikinsu Malam Nasiru Kabara da Malam Sani Kafinga in da s**a zarge Wahabiyanci wanda bai fahimci sufanci ba.
Wannan rikicin ne ya raba Gumi JNI in da kungiyar sufaye s**a mamayeta , sannan ya fuskanci yunkurk kashe shi a Kano da Jeddah.
Rikici tsakanin Gumi da Dariku ya sake zafi bayan kafa wata sabuwar kungiya mai suna ' Jama'at Izalat Al-bidi'a Wa Iqamat As-sunnah ' a harafance J.I.B.W.I.S a takaice IZALA a Jos cikin 1978 karkashin Malam Isma'ila Idiris.