Jaridar Ji da Gani

Jaridar Ji da Gani Wannan Bahaushiyar Jarida tana bada labarun cikin gida da wajen Najeriya.

DAN TAKARAR MAJALISAR JAHA A JAM'IYYAR NNPP, YANI WATSI DA DAN TAKARAR JAM'IYYAR SU YA NUNA GOYON BAYA GA DAN TAKARA JAM...
23/01/2023

DAN TAKARAR MAJALISAR JAHA A JAM'IYYAR NNPP, YANI WATSI DA DAN TAKARAR JAM'IYYAR SU YA NUNA GOYON BAYA GA DAN TAKARA JAM'YYAR APC A JAHAR TARABA.

A jiya ne dan takarar dan majalisar jaha a jam'iyyar NNPP wato Hon. Stephen Othaniel yakai ziyarar goyon baya ga dan takarar Sanata Alh. Sani Danladi na jam'iyyar APC a jahar Taraba a gidansa dake birnin Jalingo.

Hon. Stephen ya shugabanci wata tawaga dayace daga mazabar su ta Karim I dake karamar hukumar Karim Lamido, ya siffanta Alh. Sani Danladi a matsayin wanda babu k**ar shi, daga bisani yakara da cewa bazasu sake su sake zabar wasu da basu iya shugabanci ba. Sa'annan s**a tabbatar da goyon bayansu dari bisa dari.

A daya bangaren idan mai karatu bai manta ba, jam'iyyar NNPP tana da dan takara Sanata wato Hon. Aminu Abdu Liman wanda rahotanni da dama s**a tabbatar da cewa Jam'iyyar ta karbi kudinshi kimanin naira million sha biyar domin bashi takara harma shugabancin jam'iyyar ta kasa da kanta ta bashi tutun jam'iyyar a wani taro da tayi a garin Bauchi, amma duk da hakan baisa wasu yan jam'iyyar ciki harda yan takara suna nuna goyon bayansu ga wani dan takara ba, duk da cewa hakan ya sabawa dokar jam'iyyar siyasa a kowani mataki.

1. Wasu tambayoyi da suke yawo a kwakwalar mutane sune, shin jam'iyyar a matakin Jaha basu amince da tutar da shugabancin jam'iyyar ta bawa AA Liman din a garin Bauchi bane, idan ta amince to mai yasa bata ladabtar da wannan dan takara nasu da yayi babban sabo ba, tunda laifin babba ne da baya bukatar jinkiri a jam'iyance.

2. Wata alaka jam'iyyar take dashi dashi wannan dan takara na APC Sani Danladi wanda a baya akwai zarge-zarge dayawa na cewa kacokan jam'iyyar a aljihunsa yake bayan kuma shi badan jam'iyyar bane, tunda ana zargin cewa shi ya hana jam'iyyar bada tiketin Sanatan was wasu yan takarkaru masu karfi.

3. Wani mataki jam'iyyar zata dauka akan yayanta da suke mata zagon kasa.

4. Yaya dan takarar yakeji idan yaga yan jam'iyyar sa suna marawa wani baya bashi ba.

Wadanda tambayoyi da mak**antan su, wakilan Jaridar Jida Gani zasuyi kokarin tuntubar Shugabancin jam'iyyar dashi kanshi dan takarar Sanatan da aka bawa tiketi wato AA Liman.

Kuci gaba da bibiyar mu domin kawo muku rahotanni daban daban.

19/01/2023

*MAFARAUTAR SUN KOMA*

Daga: Muawuya Dalhatu

Wassu Mafarauta Biyar Sun Yi Tafiyar Shekaru Uku Zuwa Garin Mu Don Su Taimaka Mana a Wasan Bana.

Amma Jagorar Su da Mutum Uku Sun Koma Bayan Sun Fahinci Wassu Daga Cikin Manyan Maluman Mu, Sarakunan Mu Da Manyan 'Yan Siyasar Mu Kai Harma Da Wassu Magobayan Su, Sun Shagalta da La'antar Juna, Tsine Ma Juna, S**ar Juna Da Kuma Yi Wa Juna Habaici ko Izgili Musamman a Shafukan Sada Zumunta Da Lasifika.

Jagorar Mafarautar Yace Kun Gwada Hakan a Wasannin 2007, 2011, 2015 da Kuma 2019 Amma Ba Ku Samu Sak**ako Mafi Kyawu ba . Shin Ku Na Tsammanin Maimaita Tsohon Tsari Zai Ba Ku Sabon Sak**ako Mafi Kyawu Ne A Wasan Bana? Kun Fi Kowa Raw Materiyal da 'Yan Wasa Amma Baku Da Tsarin Sarrafa Su.

Ya Kara Da Cewa ƙarin Matsalar Ku A Bana Kuma Shine Kusan Kowa A cikin ƴan Siyasar Ku Yana Da Farashi, Kananan Kuma Sun ce Ba Wanda Za Su Yi Wa Aiki Kyauta Bana (Zabe Ne Kawai Kyauta).
Yuyuyun Ku Kuma Sai Kun Lallaɓa Su Za Su Karbi Katin Zaben Su, Ku Lallaɓa Su Don Su Fita Zaben, Sa'anan Kuma Sai Kun Yi da Gaske Su Hada Kuri'un Su Waje Guda.

Haka Kuma Manyan Ku Sun Fi Maida Hankali Akan Abinda Ku Ke Da Shi Fiye Da Abinda Baku Da Shi Wanda Kuma Shi Ku Ke Ikirarin Nema Kullum.

Jagorar Mafarautar Ya Ce Taimako Baya Tasiri a Inda Ba Sirri, Tsari Da Kuma Kare Mutuncin Juna.

Muka ce da Jagorar Yayi Hakuri Tunda Ya Riga Ya Shigo Ga Kuma Wasa Saura Kiris. Sai Yace Dole Zai Koma Tunda Mun Mishi Alkawarin Zamu Sauya Tsari Amma Kuma Ya Samu Akasin Haka.

Jagora Yace Ya k**ata Ku Gane Cewa Mutane Basa Karɓan Gaskiya Daga Wanda Ya Fusata Su Amma Su Na Iya Karɓan Kudi Daga Wanda Ya Cutar Da Su Kuma Su Biya Mishi Buƙata.

Ita Siyasa Ai Kamar Wasan Kwallo Take Ko Noma. Ko Baka Da Kyakkyawan Niyya Zaka Iya Yin Nasara Matuƙar Akwai Kayan Aiki da Tsari.

Ita Siyasa Ba Magana Ba Ce Ta Halal Da Haram Kawai Ba. Tunda Ko a Sallah Ba Dukkanin Abinda Ya Halatta Muke Aikatawa Ba Bare Kuma a Siyasa Irin Ta Amurka Wanda Ba Ruwanta da Shekaru, Aqida Ko Ladabi.

Har Ila Yau Jagorar Baiyi Shiru Ba Yaci Gaba Da Cewa Kuma Ta Yaya Matasa Za Su Fahince Ku Tunda Ba Kuma Bari Aka Kammala Shari'un Da S**a Shafi Zabukan Fidda Gwani A Kotunan Koli Ba, Ba Ku Bar Matasa S**a Saurari ƴan Siya Ba, Baku Bar ƴan Siyasa S**a Gama Yakin Neman Zabe Ba (Kai Wassu Ma Basu Fara Ba Fa), Su ka Nuna Bajintan Su, Su Ka Fitar Da Manufofin Su. Su Ka Kuma Bawa Mutane Abinda Allah Ya H**e Mu su ba.

Mutum Dayan Kuma Yace Bazai Koma Ba Zai Zauna Ya Nemi Kuɗin Shi Kawai Kamar Yadda Sauran Baki Da ƴaƴan Su Su ke Nema a Garin Mu.

Mafarautar Dai Sun Koma Amma Sun Mana Alkawarin Za Su Ke Mana Fatan Alheri A Comment Daga Garin Su.

Muawuya Dalhatu
Malami a Jami'ar Tarayya ta Wukari dake, Jahar Taraba.

Hoto mai magana: Hotunan wurin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Lebour Party, Peter Obi kenan daga fil...
07/12/2022

Hoto mai magana: Hotunan wurin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Lebour Party, Peter Obi kenan daga filin wasa na Jolly Nyame anan garin Jalingo.

Salamu Alaikum, muna iya daukacin al'ummar dake bibiyar wannan shafin fatan alkairi, sannan muna masu baku hakuri kasanc...
20/10/2022

Salamu Alaikum, muna iya daukacin al'ummar dake bibiyar wannan shafin fatan alkairi, sannan muna masu baku hakuri kasancewa an Kwan biyu baku jimu ba hakan ya faru ne sabida wasu yan gyararraki da mukeyi da wannan muke muku albishir cewa da yardan Allah zamu dawo bada jimawa ba, kuma muna tafi da ingantattun labarai da wasu shirye shirye masu kayatarwa.

Mungode.

Gwamnan jahar Taraba ya nada Shugabanin kananan hukumomin Jahar na rikon kwarye. A yau ne gwamnan hajar Darious Dikson I...
24/08/2022

Gwamnan jahar Taraba ya nada Shugabanin kananan hukumomin Jahar na rikon kwarye.

A yau ne gwamnan hajar Darious Dikson Ishaku ya rattaba hannu akan Shugabanin rikon na kananan hukumomin guda 16 Wanda s**a haka da;

Hon. Ammazalla John, Kurmi LGA
Hon. Jugulde, Sardauna LGA
Hon. Aminu Danbaba, Bali LGA
Hon. Ismaila, Ardo Kola LGA
Hon. Aminu Hassan, Jalingo LGA
Hon. Bala S Bako, IBBI LGA
Hon. Stephen, Wukari LGA
Hon. Niamel Tudun, Yorro LGA
Hon. Musa Abashi, Ussa LGA
Hon. Paul Dogoh, Gashaka LGA
Hon. Daniel Zading, Lau LGA
Hon. Dan Asali Biru, Gassol LGA
Hon. Barr. Shehu Vocks, Karim/L LGA da
Hon. Nicodemus, Donga LGA

A kwannanan ne gwamnan ya rushe Shugabanin kananan hukumomin sak**akon karewar wa'adinsu.

Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!Rubutawa...
21/08/2022

Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!

Rubutawar Dakta Auwal Mustapha Imam

Wani Malamin Jami'a Dakta Auwal Mustapha Imam yayi rantsuwar cewa matukar gwamnati bata biyasu albashin su na wata shida ba to zaibar aikin jami'a. Kamar yadda ya bayyana a shafin shi na Facebook k**ar haka; 👇

PhD ne da ni, duk Arewa ni kaɗai na ƙware a arean da na ƙware. Ina koyarwa a jami'o'i guda biyu na gwamnatin tarayya. Wasu jami'a'o'in na buƙatar aiki na.

Muna da damar aiki mai kyau a ƙasashe da yawa da ake mutunta ilimi, amma muka zaɓi mu dawo gida saboda babu isassun Malamai. Ana biyanmu abinda ba ya iya ɗaukar nauyin hidindimunmu.

Gwamnati ta yi alƙawura na inganta rayuwarmu, amma an gaza. Mun shiga yajin aiki domin nema wa kawunanmu mafita, amma gwamnati na barazanar ƙin biyanmu albashinmu da aka riƙe na wata shida.

Ga wannan mawaƙin waƙa kawai ya iya, ba ya amfanar da Nijeriya to kowace hanya, amma a jirgin ƙasar mu ake ɗaukar sa. Mu kuma da muke bauta wa ƙasar mu, mun zama abin wulakantawa.

Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!

AN SAKE JOLLY NYAME An saki tshohon Gwamnan jahar Taraba Rev. Jolly Nyame daga gidan kurkuku, bayan shafe shekaru da dam...
08/08/2022

AN SAKE JOLLY NYAME

An saki tshohon Gwamnan jahar Taraba Rev. Jolly Nyame daga gidan kurkuku, bayan shafe shekaru da dama a gidan kurkuku. A shekarar 2018 ne mai shara'a Adebukola Banjoko ta fara daure Jolly Nyame bisa samunsa da kayi da sace wasu kudade a lokacin da yake gwamna a Jahar Taraba, daga bisani kuma a shekarar 2020, kotun kololuwa ta tarayya ta tabbatar da shara'ar karamar kutun sannan ta tabbatar masa da daurin shakaru 12 a gidan gyaran hali.

A ranar 14 ga watan 4 na wannan shekara ne gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta yafewa Jolly Nyame da wasu mutane da kotu ta daure bisa, amma ba'a sako suba a wancan lokacin sabida ba'a gama cike wasu ka'idodi ba.

MATSALAR GARKUWA DA MUTANE (Kidnapping) A JALINGO DA KEWAYE; SHIN AKWAI MAFITA? Ra'ayin wani Ma'aikacin Jaridar Ji Da Ga...
04/08/2022

MATSALAR GARKUWA DA MUTANE (Kidnapping) A JALINGO DA KEWAYE; SHIN AKWAI MAFITA?

Ra'ayin wani Ma'aikacin Jaridar Ji Da Gani

Matsalar kidnapping dinnan kusan kullum sai anyi shi a Jalingo sai dai kawai idan abin bai shafi na kusa dakai bane, abin har yazama new normal. Ita kuma gwamnati bata damu da tayi wani abu akai ba, su kuma community sun zubawa gwamnati ido duk da cewa ana kokari amma ai kokarin bai isa ba, a duk lokacin da kuke da matsala irin wannan tsayawa zakuyi ku nemi mafita, k**ar dai yadda Bahaushe yake cewa ne "Sai da dan gari ake cin gari" dole idan kunaso ku samu mafita kubawa jami'an tsoro hadin kai, duk wadda ake zargi a mikashi hannun jami'an tsoro ba tare da an duba ko dan wanene ba, mutum ko shine jauron gari mai unguwa ko wanne shi idan an zargin shi dole a gayawa jami'an tsoro domi susa ido akanshi.

Ba karamar illa wannan kidnapping din ke jawowa ba, a duk lokacin da akayi kidnapping din mutum aka sako shi yadawo gun iyalanshi a lokacin da iyalan ke murna ni kuma abubuwa biyu ne ke zuwa mini a rai;

Na farko dole zai samu matsala ta gefen lafiyar shi, domin dawuya ya dawo daidai yadda yake ada, koda ma zai dawo tofa, sannan da wuya ba'a samu matsalar lafiyar kwakwalwa ba, tunda da wuya mutum yadawo ba tare da yarika muggan mafarki ba, da kuma razana bacci kuwa dole sai an dauki lokaci kafin ya dawo daidai.

Na biyu shine gefen tattalin arziki, duk mutumin da akayi kidnapping dinshi dinnan kafin a sake shi dole sai anbiya wasu makudan kudade, kuma duk yadda arzikin mutum yake idan aka biya kudin fansa dole zai dauki lokaci kafin tattalin arzikin shi yadawo, wani ma baida shi family ne suke hadawa, kenan abin kowa yake shafa ta yadda idan aka biya kowa sai yaji a jika, wasu dole sai an saida kadara, nasan wadda aka saida gadon shi kafin aka biya masa wannan duki. To duk baza mu fahimci illan data mana ba sai lokacin abin ya wuce tukun.

Shin akwai mafita?

Babu wata matsala data taba samun wata al'umma kuma aka samu mafita ba tare da, sun tsaya da addu'a sannan s**abi da aiki ba, dole sai an cire tsoro kuma an mika duk wani bara gurbi ga jami'an tsoro.

Gwamnan jahar Taraba ya cika shekaru 68 a yau.A yau Gwamnan Taraba Arc. Darius Ishaku ya cika shekaru 68 a duniya.Gwamna...
30/07/2022

Gwamnan jahar Taraba ya cika shekaru 68 a yau.

A yau Gwamnan Taraba Arc. Darius Ishaku ya cika shekaru 68 a duniya.

Gwamnan wadda ke takarar Sanata a Taraba ta kudu ya cika shekaru 68 da haihuwa inda dan takarar Shugaban kasa, Gwamnoni da manya manyan Nijeria s**a rubuta mishi sakon murnan bazde dinshi a kafofin sada zumunta daban daban.

YANDA MINISTAN SUFURI ENGR. MUAZU JAJI YA BADA MUKAMI DAYA GA MUTUM BIYU A LOKUTA MUBANBANTA.  A farkon wannan wata ne k...
28/07/2022

YANDA MINISTAN SUFURI ENGR. MUAZU JAJI YA BADA MUKAMI DAYA GA MUTUM BIYU A LOKUTA MUBANBANTA.

A farkon wannan wata ne kafar sada zumunta na Facebook ya cika da taya murna wa Abdulazeez Mafindi yadda mutane s**a tayashi murnan cewa Ministan Sufuri Engr. Muazu Jaji ya nadashi a Matsayin shugaban ma'aikatanshi, duk da irin wannan dunbin mutane da s**a taya wannan murna baisa shi Ministan ya karyata bada aikin wa Abdulazeez Mafindi din ba koda kuwa ta fejin shi na sada zumunta ne, kenan wannan yana nuna cewa nadin gaskiya ne ba jita jita bane.

Kwasan sai aka sakejin shi Ministan ya sake nada Dr. Abubakar Dantsoho har ilayau a Matsayin shugaban ma'aikata k**ar dai yadda ya nada Abdulazeez Mafindi dn, batere ya an banawa al'umma soke shi wannan nadin na farko ba.

Duk da cewa takardan daukan aikin (Appointments) duka biyu baiyi yawo k**ar yadda rubuce rubucen jama'a ya bayyana ba, sai dai ai shirun budurwa na'am ne.

Zuwa yanzu mutane sun gagara fahimtar wanne daga cikin wadanda aka bawa mukamin na boge, ko Kuma dai Ministan ya janza hukunci ne daga baya. Kodai rashin chantantar shi na farkon ne ta bayyana bayan an bashi mukami.

Munyi kokarin tuntubar Ministan domin jin yadda abin yake amma ya cutura.

Sen. Bwacha ya nada Malamin da Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar a Matsayin Darektan Kamfe. Malam Abdulrahma...
25/07/2022

Sen. Bwacha ya nada Malamin da Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar a Matsayin Darektan Kamfe.

Malam Abdulrahman Dahiru Jen shine Malami kuma shugaban Komitin marayu da Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar daga shiga harkokinta dare da jagorancin Sallah a masallacin ta dake Unguwar Barade Jalingo a ranar 14 ga watan shida bisa ga zargin shi akan hada kai da kuma marawa Sanata Emmanuel Bwacha baya a Siyasar Taraba.

Abin tambaya anan shine, shin daukan Malamin a Matsayin Darektan Kanfe zai taimakawa Sanata Emmanuel Bwacha gurin samun kuria'ar Musulman jahar ko a'a.

A Jahar Taraba dai siyasar addini ne kai tsaye yayi k**ari, kusan za'a iya cewa anja layi a tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci sai dai yan kadan daga cikin mabiya addinan guda biyu.

Ku cigaba da bibiyar mu domin kawo muku ingantattun labarai da rahotanni.

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta bayyana ranar 31 ga watan Juli a matsayin ranar da zata rufeyin rijistar zabe....
25/07/2022

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta bayyana ranar 31 ga watan Juli a matsayin ranar da zata rufeyin rijistar zabe.

Hukumar ta bayyana cewa, daga yanzu za'a cigaba da gudanar da yankan katun zaben ne daga karfe 9 na safe zuwa karfe 5 na yamma, haka zalika ta bayyana cewa ranar Asabar da Lahadi suna cikin ranakun da za'a rika gudanar da rijistar.

Hukumar tayi kira ga wadanda basu riga sunyi katin ba da suyi gaggawar zuwa yankan katin kafin lokaci ya kure, domin babu tabbacin sake kara wa'adin ranakun rijistar.

Kamar yadda aka sani ne, ana gudanar da rijistar katin zaben ne a ofishin INEC din na kawace karamar hukuma.

Ɗaya daga Cikin waɗanda aka sace a jirgin ƙasan Kaduna - Zuwa Abuja ya Kuɓuta.Elkalil Muhammad yace;Alhamdulillah!Bayan ...
25/07/2022

Ɗaya daga Cikin waɗanda aka sace a jirgin ƙasan Kaduna - Zuwa Abuja ya Kuɓuta.

Elkalil Muhammad yace;

Alhamdulillah!

Bayan watanni 4 Allah ya kuɓutar da Barrister Hassan Othman daga hannun Kidnappers. Kamar yadda kuka gani a cikin faifan Video da s**a fitar jiya, Barrister Hassan yana daga cikin waɗanda aka ba dama yayi Jawabi.

Kawo yanzu bamu san yadda akayi Barrister Hassan ya kuɓuta ba. Muna roƙon Allah ya kuɓutar da sauran Ameen.

Jerin sunayen yan takarar gwamna da hukumar zabe ta jahar Taraba ta kafe. Sunayen sun hada da;1. Sen Emmanual Bwacha  (A...
23/07/2022

Jerin sunayen yan takarar gwamna da hukumar zabe ta jahar Taraba ta kafe.

Sunayen sun hada da;

1. Sen Emmanual Bwacha (APC)
2. Yahaya Mohammed Sani(NNPP)
3. Kefas Agbu (PDP)
4. Philip Munlip (LP)
5. Dr David Charima (AAC)
6. Ibrahim Sani (NRM)
7. Haniel Henry Banti (APP)
8. Manu Fedemure Sunday (APGA)
9. Adda Gideon Wunuji (APM)
10. Wasa Josiah Wukari (PRP)
11. Bala Kabiru (Boot Party)
12. Adamu Bello (Zenith Labour Party)
13. Hamman Mohammed Mbali (Accord party)
14. Aminu Ibrahim (ADC)
15. Saadu Abubakar (YPP)
16. Mustapha Hamman Abubakar (ADP)
17. Gambo Abubakar Sadiq (AA)
18. Baido Danladi Tijo (SDP)

Zan iyacin zabe a Taraba koda dan uwana Kirista na dauka a matsayin mataimaki ba Musulmi ba.  Sen. Emmanuel Bwacha dan t...
22/07/2022

Zan iyacin zabe a Taraba koda dan uwana Kirista na dauka a matsayin mataimaki ba Musulmi ba.

Sen. Emmanuel Bwacha dan takarar gwamna a Jam'iyyar APC a Taraba ya bayyana cewa zai iya daukan wanda ba musulmi ba a matsayin mataimaki kuma yaci zabe.

Sen. Bwacha ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da yan jarida, yace shi zai iyacin zabe koda bai dauki musulmi a matsayin mataimaki ba amma amma baiyi haka ba.

Da yake maida martani akan ko yadace Sen. Bola Tinibu ya dauki Sen. Kashim shatima a matsayin mataimaki duk cewa a akwai Kiristoti da s**a chanchanta?

"Bansan dalilin shi na yin haka ba Watakila idan ya dauki Kirista bazai ci zabe bane, amma ni nasan ko ban dauki Musulmi ba zan iyacin zabe amma banyi haka ba" cewar Senata Bwacha.

Wannan furuci da Bwacha yayi ya jowo cece kuce musamman a kafar sada zumunta yayinda wasu ke cewa kwatakwata bai k**ata yayi wannan furucin ba a matsayin shi na Wanda yake neman bayan musulmai, in da wasu kuma ke cewa dama tun fil'azal shi Bwacha ya zani Musulmai wannan furucin ma na boye ne ya fito fili.

Shin wadannan kalamai zai taimakawa shi Emmanuel Bwacha ko kuma zai kara mishi bakin jini?

Ku cigaba da bibiyar Jaridar Ji da Gani domin cigaba da kawo muku sharhin yau da kullum.

Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP a Jahar Taraba ya ziyarci mahaifarsa.Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP Col. Agbu Kef...
16/07/2022

Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP a Jahar Taraba ya ziyarci mahaifarsa.

Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP Col. Agbu Kefas yakai ziyara mahaifarsa dake karamar hukumar Wukari a yau.

Abu Kefas yakai ziyarar ne tare da ɗunbin magoya bayansa, a yayinda ya samu tarba daga shugabanin Jam'iyyar na ƙaramar tasa.

An Buƙaci Jam'iyyar APC ta kasa data kori wani jigo mai suna Chief David Sabo KenteShuwagabannin Jam'iyyar APC na Gundum...
15/07/2022

An Buƙaci Jam'iyyar APC ta kasa data kori wani jigo mai suna Chief David Sabo Kente

Shuwagabannin Jam'iyyar APC na Gundumar Kente dake karamar hukumar Wukari sun bukaci Jam'iyyar APC ta kasa data kori daya daga cikin ƴaƴanta Chief David Sabo Kente sabida zargin yiwa jam'iyyar zagon ƙasa.

A wani wasika da shuwagabannin s**a rubuta dauke dasa hannun mutum 19 cikin 24 na shuwagabannin Jam'iyyar sun zarge shi da assasa fitina da zuwa wasu ƴan Jam'iyyar domin su bijire mata.

"Munyi mamaki matuka, cikin hawaye muke mun gagara fahimtar Chief David Sabo Kente duk da yadda PDP taci mishi mutunci APC ta karɓe shi hannu bibbiyu shine yanzu yake mata zagon ƙasa". Cewar Shugabanin Jam'iyyar.

"David Sabo Kente ya gagara muna kiyayarsa ga dan takarar mu na Sanata a Jam'iyyar APC Danji SS, hakan ta kaishi ga yiwa mai gidanshi Darious Ishaku aiki domin ganin ya kada APC a zaɓe mai gabatowa. Cewar Wasikar.

Zuwa yanzu dai ana jiran irin hukuncin da Jam'iyyar zata dauka akan shi jigon nata, shin zatayi fatali dashi ko zata karbi korafin.

Kuci gaba da bibiyar Jaridar JI da Gani domin kawo muku ingantattun labarai.

HASKE TV Gidan talabijin na ƴan kasuwa ta farko a Jahar Taraba.Daga: Zaharadden IbrahimKo shakka babu rashin ingantattan...
11/07/2022

HASKE TV
Gidan talabijin na ƴan kasuwa ta farko a Jahar Taraba.

Daga: Zaharadden Ibrahim

Ko shakka babu rashin ingantattan kafafen watsa labarai na zamani yana taka rawa wajen danne haƙin talakawa, rashin cigaba da taɓarɓarewar ko wacce kasa, yanki ko Jaha, zamu yarda da haka ne idan mukayi duba da jahohin da jahar Taraba s**a samu ƴanci tare kai harma da waɗanda ta rigaye su. Tun bayan kafa jahar da wajen shekaru kusan 31 babu wata kafar talabijin mai zaman kanta a jihar wadda zata rinka duba matsalolin al'umma da koke koken su domin isarwa gwamnati da shugabanni, sarakuna dama wakilai daga kana Jaha har zuwa kananan hukumomi.

Har ila yau, jahar Taraba Jaha ce dake da tarin kabilu mabanbanta amma rashin kafar da zata bayyana al'adun su yasa dayawa ba'a sansu a duniya ba sai ɗaiɗai ku da ƴaƴan su s**a shahara, akwai dayawa daga ƴaƴan jahar dake da fusahar kira sosai, a tunbatse take da manazarta, ciki harda Ma'waka, tabbas jahar tana da jarumai a fagen wasan kwaikwayo, kwararrun ƴan ƙwallon ko wace iriya kuwa, ba'a barta da baya ba gurin wurin samun kwararru ta bangaren na'ura mai ƙwaƙwalwa, akwai dimbin ƴan kasuwa, ƴan boko, gaggan ƴan Siyasa, Allah ya albarkaci jahar da manoma dama makiyaya.

Bakayi karya ba idan kace babu kallar abinda zaka nema a wannan Jaha ta Taraba ka rasa, sai dai babu wani bijire da zata haska wadannan albarkatun saboda rashin samun gidan talabijin ta zata haska su.

Bollowar Haske TV ya farantawa ƴaƴan jahar matuka domin suna da tsammanin zata kashe musu ƙishirwan da yajima da busar musu da makogoro.

Sai dai hanzari ba gudu ba, k**ar yadda muka sani ne, mafi akasarin gidajen talabijin na ƴan kasuwa suna samun cigaba ne ta hanyar tallace tallace da sanarwa ko cigiya da ƴan kasuwa, ƴan Siyasa, masu gudanar da buki dama sauran su suke kawowa kuma su biya, rashin yin haka yana matukar durkusar da gidajen talabijin na ƴan kasuwa sosai sabida ba karamin kudi ake sawa a kasuancin ba.

Kenan matukar munaso mu nishadanta, mu fadaku kuma mu ilmantu to yazama wajibi mu tallafawa wannan gidan talabijin domin su tafiyar da kusuwancin su yadda ya k**ata.

Muna fata gidan talabijin na Haske TV zai kashe mana kishin ruwan mu a jahar Taraba, ta yadda duk zamu gansu da shirye shiryen da zasu rika kawo mana.

Shugaba Buhari ya canzawa Engr. Muazu Jaji wurin aiki. A yau Laraba majalisar zantaswa tayi zaman ta na mako-mako inda t...
06/07/2022

Shugaba Buhari ya canzawa Engr. Muazu Jaji wurin aiki.

A yau Laraba majalisar zantaswa tayi zaman ta na mako-mako inda ta sauyawa Karamin Ministan ayyuka Muazu Jaji wurin aiki daga ma'aikatar ayyuka zuwa na Sufuri.

A watannin da s**a gabata ne dama shi Shugaba Buhari ɗin ya naɗa Engr. Muazu Jaji a matsayin karamin ministan ayyuka.

Tun bayan dashi Ministan Sufurin Rotimi Amaechi ya ajjiye mukaminsa na ministan sufuri domin neman shugabancin kasar a inda yasha kaye a hunun Bola Ahmad Tinibu da kuri'u masu dinbin yawa.

Muazu Jaji ya fito ne daga babban fadan Jaha wato Jalingo ina yake cin shiyar Taraba tun bayan sauke Engr. Saleh Mamman dashi shugaba Buharin yayi sak**akon rashin tafiyar da aiki yadda ya k**ata.

Gwamnan jihar Taraba ya amince da rushe shugabanin kananan hukumomi. Gwamnan jihar Taraba Arc. Darious Ishaku ya amince ...
03/07/2022

Gwamnan jihar Taraba ya amince da rushe shugabanin kananan hukumomi.

Gwamnan jihar Taraba Arc. Darious Ishaku ya amince da rushe shugabanin kananan hukumomin jahar Taraba bayan da wa'adin su ya ƙare a ranar 3/7/2022. Sannan ya bukace su dasu mika harkokin kananan hukumomin ga shuwagabannin ma'aikatun su kafin dawowar shi jahar.

Sanarwar da fito ne dauke dasa hanun Iliya Bekyu Akweh, babban Sakataren watsa labarai na gwamnan jahar.

Daga: Malam Malam Zaharadden Ibrahim Bayan rubutu da Ramiyu A. Jalingo yayi mai sosa zuciya akan maganar wanann bawan Al...
16/06/2022

Daga: Malam Malam Zaharadden Ibrahim

Bayan rubutu da Ramiyu A. Jalingo yayi mai sosa zuciya akan maganar wanann bawan Allah mai Kawu Malami da yake sa'naar garuwa (Watar vendor) bayan yana da Degree fanin Agricultural Engineering, mutane da yawa sun nuna tausaya.

Mun tattauna domin muga ta wace hanya zamu taimake shi daya baya muka yanke shawarar karbar Account Number dinshi domin akwai mutane da s**a nuna sunaso su taimaka masa.

Ga account Number dinshi k**ar haka.

Account Name: Kawu Malami
Account Number: 6171350240
Bank Name: Fidelity Bank

Allah ya bada ikon taimakawa.

Domin karin bayani zaku iya kiran shi ta wannan lamba.
08039732142

ABUN TAUSAYI😭Daga: Ramiyu A. Jalingo.Wannan bawan Allah da kuke gani a hoto sunan shi Kawu Malami, dan karamar hukumar M...
16/06/2022

ABUN TAUSAYI😭

Daga: Ramiyu A. Jalingo.

Wannan bawan Allah da kuke gani a hoto sunan shi Kawu Malami, dan karamar hukumar Misau ne da ke jahar Bauchi, wanda ke sana'ar tura ruwa a amalake a nan garin Jalingo. Hakika akwai abubuwa masu sosa zuciya a labarin wannan bawan Allah. Mun hadu da shi a bakin kasuwar Jalingo a sana'ar sa ta saida ruwa, inda amalankensa ta mangaji tayar motar wani bawan Allah har tayar ta fashe, ganin yadda ya shiga tashin hankali wannan bawan Allah mai tausayi yace ya yafe masa, zai je ya canja tayar, amma yaje ya nemo masa vulcanizer, take ya nemo aka canja tayar mai motar ya biya har ma ya kara masa da kyautar N500, ganin wannan kyautatawa da mai motar yayi yasa aka fara hira a kan rayuwa, inda a nan muka fahimci ashe wannan mai ruwan graduate ne, Degree yake da shi a Agricultural Engineering.

Da farko mun so muyi tantama a kan hakan, duk da yanayinda kasar nan take ciki mutum kan iya sana'ar yasar shadda ma don ya rufawa kansa asiri, sai dai daidaikun mutane ne zasu iya yin hakan da degree. Da farko k**ar ba zamu yarda da zancen sa ba, amma bayan doguwar tattaunawa mun fahimci Kawu gaskiya ya fada, kuma mun bincike shi sosai, ya hadamu da yan garin su da suke tura ruwa tare, da ma 'yan uwan sa a can gida, inda aka tabbatar mana Kawu mutumin kirki ne, wanda ba karatun boko kawai ba, har na addini yana da shi dai-dai gwargwado, yana kuma da aure har da 'ya'ya. Daga karshe muka nemi amincewar sa cewa zamu dau hotonsa mu yada ko wani a Bauchi ko wata jahar daban zai taimake sa, kuma ya amince har ya hada mu da 'dan uwan sa da ya dau hotunan takardunsa ya turo mana.

Abun lura a labarin Kawu shine, duk da shi ba mutum ne mai mutuwar zuciya, da kuma girman kai ba, amma munaga ya cancanci sana'ar da tafi saida ruwa a amalanke, kuma shi kansa yace yaso ace wata sana'ar yake koda tuka Keke Napep, to amma bai samu wannan damar ba, don ba kowa bane zai dau dukiyar sa ya bawa bako. Amma dai gaskiya akwai takaici, kuma ya bayyana akwai dubban mutane k**ar shi, amma taimako da tallafawa marasa karfi su tashi yayi karanci a yankin da yafi fama da talauci da rashin abun yi (Arewa). In har Kawu zai iya tura ruwa don ya rufawa kansa asiri, akwai wayanda ba zasu iya ba, sannan a cikin haka ake samun masu sauya tunanin su zuwa aikata laifuka da zasu hana kowa sakat a kasa.

Akwai bukatar gwamnati da masu hanu da shuni su taimaki irin wayan nan, in aiki ya samu fa lillahil hamdu, in kuma jari ne a bawa irin wannan don su tashi. Saboda haka kofa a bude take ga masu niyar taimakawa, musamman a can jahar sa Bauchi inda yace dole ce ta sa shi baro gida, a taimaka masa da jari don ya dogara da kan sa.

Ga lambobin sa da na makusancin sa.
Kawu Malami
08039732142
08084804104

Dan uwan sa!
Al-mansur Muhammad
07038569066

Yan sanda a Jihar Taraba da ke Najeriya sun k**a wani mutumin da suke tuhuma da laifin hada bama-bamai.An k**a mutumin n...
15/06/2022

Yan sanda a Jihar Taraba da ke Najeriya sun k**a wani mutumin da suke tuhuma da laifin hada bama-bamai.

An k**a mutumin ne a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol ta jihar a ranar Laraba.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an gano wasu kayayyakin hada bam a gidan mutumin, wanda ya mayar masana'anta.

An kuma gano wasu bindigogi da harsasai a gidan.

Jami'an 'yan sanda sun ce mutumin dan asalin Jihar Zamfara ne, kuma ana tsare da shi a shalkwatar 'yan sandan da ke Jalingo.

An kai wani jerin hare-hare da bama-bamai a watan jiya a cikin Jihar ta Taraba.

Kakakkin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin da k**a wanda ake tuhumar.

Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar da wani Malami mai suna Abdul-Rahman Dahiru Jen daga shiga harkokin kungiy...
14/06/2022

Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar da wani Malami mai suna Abdul-Rahman Dahiru Jen daga shiga harkokin kungiyar da jagorancin Sallah a masallacin ta dake Unguwar Barade Jalingo.

Duk da cewa kungiyar bata bayyana dalilin ta na dakatar dashi ba amma rahotanni sun nuna cewa dakatarwar yana da alaka da abinda ya shafi siyasar addini dake gunana a Jihar Taraba.

Zuwa yanzu wakilin mu yana kan tattara bayanai.

Ku bibiyi Jaridar Ji Da Gani domin kawo muku cikakken rahoto akan lamarin.

YANZU YANZUBola Ahmed Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na Jam'iyyar APC a matakin Shugaban kasa. Tinibun wanda ya lashe...
08/06/2022

YANZU YANZU

Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na Jam'iyyar APC a matakin Shugaban kasa.

Tinibun wanda ya lashe zaben da kuri'a 1271 akan takwarorin sa sha hudu wanda s**a haɗa da mataimakin shugaban kasa maici a yanzu Yemi Osinbanjo, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, Shugaban Majalisar dokoki Ahmed Lawan, Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da sauransu k**ar yadda zaku iya gani a hoton dake ƙasa.

Sanata Ikenya ya fice daga Jam'iyyar PDP. Tsohon ministan ruwa kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Taraba a Jam'iyyar ...
06/06/2022

Sanata Ikenya ya fice daga Jam'iyyar PDP.

Tsohon ministan ruwa kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Taraba a Jam'iyyar PDP Sen. Joel Danlami Ikenya ya fice daga Jam'iyyar PDP.

A wasikar daya rubutawa shugaban jam'iyyar PDP na gundumar Jibu dake karamar hukumar Wukari, Ikenya ya bayyana cewa ficewarsa daga PDP abu ne daya shafe shi, daga bisani ya sake wallafawa a shafinsa na Facebook cewa ya fice ne saboda matsalolin dake Jam'iyyar.

Daga bisani tsohon Sanatan ya godewa magoya bayansa da waɗanda suke bashi shawara.

Farfesa Sani Muhammad Yahaya ya lashe zaben fidda gwani na Jam'iyyar NNPP a Jahar Taraba. Dan takarar gwamnan jihar Tara...
06/06/2022

Farfesa Sani Muhammad Yahaya ya lashe zaben fidda gwani na Jam'iyyar NNPP a Jahar Taraba.

Dan takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam'iyyar NNPP Farfesa Muhammad Sani Yahaya ya lashe zaben fidda gwani na Jam'iyyar NNPP a yammacin yau Litinin.

Sani Yahaya wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa NNPP a satin data gabata ya lashe zaben da kuri'a 464 akan takwarorin sa biyu wato Philip Johnson daya samu kuri'u 19 da kuma Al'amin Saleh daya samu kuri'u 8.

KASUWANCIN R&A (R&B) INVESTMENTWata kasuwancin data shafi duk wani mazaunin Jalingo. A rana mai k**ar ta yau 5-6-2021 wa...
05/06/2022

KASUWANCIN R&A (R&B) INVESTMENT

Wata kasuwancin data shafi duk wani mazaunin Jalingo.

A rana mai k**ar ta yau 5-6-2021 wato shekara daya kenan cip-cip wani shahararren dan kasuwa a garin Jalingo wato Alhaji Malam Ramadan Inuwa (Ramadan investment) ya fito ya bayyanawa duniya cewa zai fara mayarwa da abokan kasuwancin shi kuɗaɗen su da s**a zuba hannun jari dasu amma ba tare da ya kara musu da riba, sabida abinda ya kira da dukushewar kasuwancin da sukeyi.

"Mutane da dama sun saka hannun jari sosai amma daya bayan daya zamu mayarwa kowa da kudinsa ba tare da an cuci kowa ba" cewar Alhaji Ramadan din.

Duk da cewa Shugaban R&A investment din yayi wannan furuci amma damar maido da kudin bai samu ba wanda har yanzu da muke tattara wannan rahoto bamu samu dalili akan haka ba.

Wakilin mu ya tabbatar mana da cewa duk da rashin dawo da kuɗin da ba'ayi ba, shi Alhaji Ramadan din ya sake kiran abokan kasuwancin nashi dasu sake saka kuɗin su domin samun riba, wanda bincike ya tabbatar da cewa mutanen da s**a saka kuɗin su a dawowar na biyu sun ninka wadanda s**a saka na farko domin an tabbatar musu da cewa yanzu kasuwancin ya dawo sabo fil.

Kasuwancin R&A investment ya duƙufar da tattalin arzikin Jalingo sosai ba kaɗan ba, domin ya shafi manyan yan kasuwa, ma'aikatan karamar hukuma da ɗinbin yan siyasa.

Binciken ya tabbatar da cewa dayawa daga cikin yan kasuwa da wanann kasuwanci ya rifta dasu sun bar kasuwar wasu sun koma tuƙin mashin mai kafa uku, wasu kuma sun hakura da kasuwancin. A bangaren yan siyasa kuwa data rintsa dasu wasu basuyi takara ba a wannan karon wasu kuma sunyi amma basuyi tasiri ba saboda rashin isassun kudi a hannu.

Bincike ya tabbatar da cewa, cikin kowani jerin gidaje 5 a garin Jalingo akwai akalla mutum daya cikin gidaje biyu da kasuwancin ya rufta dasu.

Za'a ma iya cewa kusan dukkan yan Jalingo abin ya rufta dasu saboda ko mutum bai yiba, wani cikin danginsa yayi, ko aboki/kawa, abokin kasuwanci, makota koma dai ya bada bashi amma ta rutsa da wanda ya bawa bashin.

Zuwa yanzu da muke tattara wannan rahoto ba'asan inda shi shugaban kamfanin R&B investment wato Alhaji Ramadan Inuwa yake ba.

Farfesa Sani Muhammad Yahaya fice daga Jam'iyyar APC ya koma NNPPDan takarar gwamna a jami'ar APC kuma tsohon shugaban j...
03/06/2022

Farfesa Sani Muhammad Yahaya fice daga Jam'iyyar APC ya koma NNPP

Dan takarar gwamna a jami'ar APC kuma tsohon shugaban jami'ar jihar Taraba Farfesa Sani Yahaya ya fice daga Jam'iyyar APC, daga bisani ya koma NNPP kuma ya sayi takardar takarar gwamna a Jami'ar.

A wasikar daya aikawa shugaban gundumar su na jam'iyyar APC ya shaida masa cewa ya yanke hukunci ne bayan kiraye kiraye daya samu daga masoyansa na jam'iyyar APC kan abinda ke faruwa a jami'ar APC a jahar Taraba.

Uwar Jam'iyyar APC ta kasa ta nemi hukumar zaɓe data sanya jihar Taraba cikin jerin jahohin da s**a gabatar da zaben kat...
30/05/2022

Uwar Jam'iyyar APC ta kasa ta nemi hukumar zaɓe data sanya jihar Taraba cikin jerin jahohin da s**a gabatar da zaben kato bayan kato.
A wata wasika data fito daga ofishin jam'iyyar APC ta kasa dauke da sa hanun Shugaban jam'iyyar na kasa Sen. Abdullahi Adamu da magatakardan jam'iyyar Sen. Iyiola Omisore sun nemi hukumar zaɓe mai zaman kanta wato INEC ta sanya Jahar Taraba cikin jerin sunayen jahohin da s**a gabatar da zaben kato bayan kato.

"Muna dana sanin sanar da wannan hukuma cewa wasikar da muka aiko na jerin sunayen jahohin da zasu gabatar da zaɓen kato bayan kato ba tare da saka jahar Taraba ciki ba, hakan ya faruwa sabida ajizanci na ɗan Adam"

"Muna kuma sanar daku yanzu cewa jahar Taraba na daga cikin jerin jahohin da s**a gabatar da zaɓen fidda na kato bayan kato, da tsammanin cewa zaku amince"

Cewar Wasikar.

Abinda daruruwan mutane ke tambaya shine shin Uwar jam'iyyar APC da aminci da Emmanuel Bwacha a matsayin dan takara kenan duk da cewa sauran yan takarkarun sun shigar da korafi?

Address

Jalingo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Ji da Gani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Ji da Gani:

Share

Category