01/01/2024
FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU A SABUWAR SHEKARAR 2024
Ya ku `yan uwana yan Najeriya,
Ina cike da farin ciki a yayin da nake wa Ilahirinmu, matasa da tsofaffi maraba da shigowa sabuwar shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Dole ne mu daga Hannuwanmu sama mu gode wa Allah madaukakin Sarki saboda albarkar da Ya yi wa kasar mu da kuma rayukan mu a cikin shekarar da ta gabata wato shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.
Ko da yake Shekarar da ta gabata na kunshe da kalubale da dama, amma duk da haka an yi abubuwan alheri masu yawa, Ciki har da mika mulki daga tsohuwa zuwa sabuwar gwamnati cikin lumana, wadda hakan alama ce da ke nuna irin gagarumin cigaban da demokaradiyarmu mai shekaru ashirin da hudu a jere ta samu
Shekara ce wacce ku al’ummar wannan kasa mai Albarka kuka amince min da in jagorance ku, kan bayyanannen kudiri na yin gyara ga kasar nan, da yin garambawul a fannin tattalin arzikinta, da inganta tsaro a iyakokin kasarmu da farfado da masana`antun mu, da inganta noma, da cigaba na bai-daya, sannan in dora kasa a tafarkin cigaba mai dorewa ta yadda mu da `yan baya za mu yi alfahari da ita.
Aikin gina ingantacciyar kasa mai dauke da al’ummar da take kishin kowanne dan kasa, shine makasudin tsayawata takarar shugaban kasa. Kuma shine taken yakin neman zabena wato SABUNTA-FATA-NA-GARI a kansa kuka zabe ni a matsayin shugaban kasar mu don na tabbatar da shi.
Daukacin abubuwan da na gudanar a Ofis, k**a daga matakan da na dauka, da tafiye-tafiye na zuwa kasashen waje tun daga ranar ashirin da tara ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da shirin da uku duk na yi su ne domin amfanin kasar mu da cigabanta.
A cikin watanni bakwai da s**a gabata na gwamnatin mu, na dauki wasu tsauraran matakai da s**a zama tilas domin ceto kasar mu daga mummunan yanayi. Daya daga cikin wadannan matakan shine cire tallafin mai wanda ya zama wani nauyi ko tarnaki ga kasar nan na tsawon shekaru arbain da biyu, da kuma cire damar da wasu `yan tsirarru suke