19/07/2024
KARFIN ZUCIYAR UWA A KAN ƳAƳANTA
Wato ita uwa, karfin zuwa da aka bata, karfin zuciya da dauriya da aka bata, kaso mafi yawa duka an bata ne akan ƴaƴan ta ba akan taba,
Da juriyar ta, da rikicin ta, da nacin ta, suna bayyana ne akan ƴaƴan ta,
Idan da yanzu zaka gamu da mace a hanya tana tafiya, haka kawai Bakasan taba Batasan kaba, ka rufeta da duka zata fita da gudu tana kururuwa amma in ɗanta karufe da duka ba zata gudu ba, jama'a munfahimta,
Haka kawai tana tafiya ka wanke ta da mari za tayi ihu ta nemi ɗauki wataƙil ta ruga da gudu amma in ɗanta ka taɓa tsayawa za tayi, saboda karfin zuciyanta akan ɗanta ba daidai bane da akan kare kanta,
Koh kaza ce, ƴaro ɗan shekara biyu da yake rarrafe zai iya korar kazar daga inda take kuma ta gudu, amma in ƴanƴanta ne ko Ubansa Bazai koreta ta gudu ba, hakane ko ba haka ba, hakane,
Idan ƴaƴanta ne, idan ƴaƴanta ne ko babansa bai isa ya koreta ta gudu tabar ƴaƴanta ba, amma in itace tsuran ta yaro mai rarrafe zai koreta kuma ta gudu,
Wannan haka tinkiya take, haka kariya take, haka a kuya take, haka saniya take,.
Idan barewa taga abinda zai farauce ta zaki, da gudu take fita iya ranta amma in ɗanta zaibi tsayuwa take ko zai kasheta, itafah uwa haka take, da haka kuma kaga ka girma,
Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah