21/12/2022
Bayan dogon hutun da ya dauka na shekaru hudu, jarumi sharukhan zai sake bayyana a masana'anatar da sabbin fina-finan sa da zasu fita.
Tun a shekarar 2018 da film din sa na zero ba'a sake ganin fuskar jarumin a wani sabon film ba, inda masoya da magoya bayansa s**a matsu da sake kallon film din sarkin Bollywood din.
A yanzu haka dai jarumi sharukhan nakan aiki akan film din phathaan wanda zai fita a ranar 25 ga watan janairun shekara ta 2023.
A yayinda yake zantawa da manema labarai sharukhan yace baiyi nufin daukar dogon hutu har na shekara hudu ba, ya tafi ne da niyyar ya huta na shekara daya, amma sakamakon annobor corona da kuma dokar kulle data biyo baya ya sanya hutun nasa yayi tsayi, yace wannan zaman da yayi ya bashi damar samun wadataccan lokaci tare da iyalan sa da kuma yayan sa.
Daga karshe jarumin yayiwa masoya kallon fina-finan sa albishir da cewa ya dawo da karfin sa tare da fatan yin abunda zai faranta zukatan masoyan nasa.
Amina Muhammad Adam