Najashi kabir Mu'azu

Najashi kabir Mu'azu Religion is the most vital to come first in any situation. Alhamdulillah for been Muslim

05/03/2024
Kishin kasa a musulumci
05/03/2024

Kishin kasa a musulumci

Yan kwalta asan nayi
05/03/2024

Yan kwalta asan nayi

ALHAMDU LILLAH
AN SAMI YIN SULHU, ƘARƘASHIN JAGORANCIN INUWAR HAƊIN KAN MALAMAI DA ƘUNGIYOYI,
PROFESSOR BARODO
SHAIK ABDULWAHAB
PROFESSOR SALISU SHEHU
PROFESSOR BABANGIDA
PROFESSOR SA'IDU DUKAWA.
DR MUAZZAM KHALID BUK
DR ENGR BASHIR HANAN
SHAIKH SHEHU MAI HULA
S**A WAKILCI SAURAN MALAMAI,
ALLAH YA SAKA MUSU DA ALKHAIRI

19/01/2024
04/01/2024

Allah Muna rokonka ka rufa Mana asiri duniya da lahira

06/10/2023

WAIWAYE ADON TAFIYA (29):
Daular Ubaidiyyah ( Faɗimiyya)

Daular Ubaidiyya ita ce daula mafi girma a cikin daulolin shi'a a tarihi, ta kafu ne a shekara ta 297 A.H a ƙasar Tunusia ,wannan daula ta mulki kimanin ƙasashe 13 a yau. Waɗanda s**a jagoranci assasa wannan daula su ne ƴan shi'a Isma'iliyya* karƙashin jagorancin wani mutun da ake kira Abu Abdullah Asshi'i. Bayan ya ci nasara akan daular Aghaliba da take wannan yakin sai ya gayyoto Ubaidullah wanda yake amsa laƙabin Almahadi da ya zo ya karɓi ragamar wannan daular a matsayinsa jikan Annabi (SAW) daga ƴarsa Faɗima k**ar yadda yake riyawa, a bisa hakane wannan daula take ansa sunan daular Faɗimiyyah, a yayin da manazarta da yawa tun a wancan lokacin suke ƙaryata wannan nasaba wanda a bisani suke danganta ga sarkinta na farko wato Ubaidullah, inda suke ke kiranta da Daular Ubaidiyyah.

A karkashin wannan daula an samu sarakuna guda 14, guda 8 dukkanin rassan ƙungiyar Isma'iliyya sun yarda da imamarsu, a yayin da a ragowar s**a samu saɓani a junansu tsakanin masu iƙrari da kuma masu musuntawa.

Mafi shaharar waɗannan sarakuna a cikin wannan daula su ne :

1- Ubaidullah Al'Mahdi: Asalin sunan shi Sa'id bin Husain bin Ahmad bin Abdullah bin Maimun Alqaddah, kakanninsa Abdullah da Maimun su ne s**a assasa kungiyar Isma'iliyya asalinsu kuma majusawa ne, sun yi hakane ba don komai ba sai don rusa musulunci. Sa'id ko Ubaidullah Al'Mahdi shi ne sarkin farko a wannan daular shi ya karasa daulolin Aghaliba da Adarisa a arewacin Africa, ya ɗora daularsa akan turba ta aƙidar Isma'iliyya wadda take cike da shirka da kafirci, ya kuma yi ƙoƙarin ɗora mutane akan wannan hanya wanda sak**akon haka ya kashe mutane da yawa tsakanin malamai da salihai da mutanen gari.

2- Muhammad Al'ƙa'imu Bi Amril Lah: sarki na 2 bayan mutuwar mahaifinsa ya shahara da zagin Annabawa a fili da kuma kira ga cewa mahaifinsa shi ne Ubangiji, da kafircinsa ya yi yawa mutane gari s**a yi masa tawaye inda malamai da yawa s**a shiga cikin wannan boren aka dade ana fafatawa ƙarshe dai ba a yi nasara akansa ba, shi ɗin k**ar yadda malamai suke faɗa ya fi mahaifinsa sharri.

3-Ma'ad Al'Mu'izzu Li Dinillah: Sarki na 4 a wannan daular a lokacinsa ya yi nasarar mamaye ƙasar Masar tare da mayar da ita babbar hedkwatarsa, hakanan shi ya assasa birnin Alƙahira a ƙasar Masar, shi ne kuma ya gina masallacin Al'Azhar wanda yake haɗe da makaranta domin karantar da aƙidar Isma'iliyya da yaye masu yaɗata a duniya, ya kuma assasa bukukuwa iri-iri daga cikinsu harda bikin mauldi.

4- Nizar Al'Azizu Billah: Sarki na 5 a lokacinsa ya ƙara faɗaɗa daular inda ya mamaye yankin Sham da kuma yankin Hijaz a tsibirin larabawa, ya kuma ƙara kafa daular da tsarata.

5- Al'Mansur Al'Hakim Bi Amirillah: Sarki na 6 a wannan daula, a lokacinsa daular ta kai ganiyyarta, wannan sarki yana da abubuwan ban mamaki kusan za a iya k**anta shi sosai da sarki Nero ko sarki Caligula a daular rumawa. A ƙarƙashe- ƙarshen zaminsa ya yi da'awar cewa shi ɗin Allah ne, wanda ya samu mabiya da ake kiransu Adduruz har yau kuma sunan suna bauta masa. Ya kuma yi yunƙurin tono gangar jikin Annabi (SAW) daga Madina domin dawo da ita Masar inda yake, sai dai ba yi nasarar hakan ba.

6- Ma'ad Al'Mustansiru Billah: Sarki na 8 kuma wanda ya fi daɗewa yana mulki domin sai da ya yi shekara 60 akan mulki, hakanan lokacinsa ya shahara da wata gagarumar yunwa da aka yi tsawon shekara 7 wanda sai da ta kai mutane suna farautar yara da mata suna cinyewa !! A lokacinsa wanann daula ta fara rauni, inda bayan rasuwarsa kan shi'a Isma'iliyya ya rabu gida biyu wanda har yau a haka suke.

7 -Abdullah bin Yusuf Al'Adid Li Dinillah: Sarki na ƙarshe a wannan daula a lokacinsa ne sultan Salahuddin Al'ayyubiy ya ruguje daular gaba ɗaya ya kuma kawar shi'anci a ƙasar Masar a shekara ta 567 A.H bayan ta shafe shekaru 262.

Wannan daula saɓanin sauron daulolin musulunci da aka yi a tarihi ba ta da wani tarihi na jihadi da yaɗa musulunci ko ba shi kariya, sai dai ƙoƙarin kashe musuluncin da ta yi ta hanyar ƙaƙaba wa mutane aƙidu na maguzanci da sunan soyayya ga Ahlul Baiti, tare da gaggauta kisa ko dauri ga duk wanda zai ƙalubanci hakan. Hakanan wannan daula ita ce ta fara assasa bautar kabari da sunan cewa kabarin waliyyai ne, hasalima yawancin kabarurrukan da ake dangantasu ga iyalan gidan Annabta a ƙasar Masar a yau duk sune s**a ƙirƙire su ba su da asali, bugu da ƙari wannan daula ta yi shuhura sosai wajen ƙarfafa yahudawa da kiristoci akan musulmai ta hanyar ba su manyan muƙamai da damammaki a cikin gwamnati, hakanan a dalilin sakacinta da kuma haɗin bakinta birnin ƙudus ya faɗa hannun turawan crusader har tsawon shekara 90, ta kuma sake haɗa kai da su inda saura ƙiris Masar suɓuce hannusu amma a lokacin Salahuddin Al'ayyubiy ya hana faruwar haka, wanda daga baya ya yanke hukuncin rushe wannan daular domin da hakane zai iya ƙwato birnin ƙidus ya kuma kori waɗannan yan k**a wuri zaunan.

Wannan shine a taƙaice game daular Ubaidiyya ga wanda yake son ƙarin bayani zai duba comment ɗin farko.

_______________________

* Isma'iliyya ƙungiyace ta shi'a da s**a rabu da shi'a masu limami 12 a limami na 7 , suna da wuce gona da iri har ta kai masu limamai 12 ma kafirtasu suke saboda da zaƙewarsu, a gaba za mu yi tsokaci akan su Insh'Allah.

Dattaijon ArzukiAlaramma malam sa'idu Yankaba
24/09/2023

Dattaijon Arzuki
Alaramma malam sa'idu Yankaba

24/09/2023

Aramma malam sa'idu
Maja bakin sheikh jaafar

14/09/2023
14/09/2023
14/09/2023
14/09/2023
DAGA CIKIN LABARIN NI'IMAR ALJANNAManzon Allah (SAW) ya ce: "Wani mutum cikin ƴan aljanna ya nemi izini wajen Allah (SWT...
13/09/2023

DAGA CIKIN LABARIN NI'IMAR ALJANNA

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Wani mutum cikin ƴan aljanna ya nemi izini wajen Allah (SWT) cewa: yana son zai yi noma! Sai Allah ya ce masa: "Kai kuwa me za ka yi da noma? Ashe ba na ba ka duk abin da ka ke buƙata ba?". Sai ya ce: "Gaskiya ne ya Ubangijina. Ka ba ni komai. Amma ni dai in zai yiwu, a ba ni dama in yi noma saboda ina sha'awar hakan". Sai Ubangiji ya ba shi dama. Sai ya je ya yi shuka. Kafin ya ƙifta ido sai shukar ta tsiro ta girma ta yi yabanya har ta kai lokacin girbi. Sai Allah ya ce masa: "Ya kai ɗan Adam! Ga buƙatarka nan an biya maka. Lallai kai ɗan Adam ba wani abu da zai ƙosar da kai" A daidai nan ne sai wani mutumin ƙauye ya ce: "Ya Manzon Allah! Duk yanda aka yi wannan mutumin Baƙuraishe ne ko mutumin Madina! Sune ƴan birni masu dogon buri. Mu mutanen ƙauye ba ruwanmu" Sai Manzon Allah (SAW) ya tuntsure da dariya.

"Na rantse da wanda raina ke hannunsa da a ce ba kwa yin zunubi, da Allah ya kawar da ku, sannan ya maye gurbinku da waɗ...
13/09/2023

"Na rantse da wanda raina ke hannunsa da a ce ba kwa yin zunubi, da Allah ya kawar da ku, sannan ya maye gurbinku da waɗanda za su dinga yin zunubin sannan su nemi gafarar Allah sai ya gafarta musu"

In ji Manzon Allah (SAW)

11/09/2023

Muna matukar kaunar Yan uwa musulmi.
Haka Kuma Muna tsananin kyama da kin kafirrai a ko Ina suke

06/09/2023
Free hand sketch by me
20/04/2021

Free hand sketch by me

Ya Allah ka yaye mana mufisar da take bibiyar mu .Ya hayyu ya qayyum
12/02/2021

Ya Allah ka yaye mana mufisar da take bibiyar mu .
Ya hayyu ya qayyum

28/11/2020

Ya Allah kayi mana arzuqi mai albarka da yalwa wanda ze amfanemu dunia d lahira

Address

Gwarzo

Telephone

+2348142270253

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Najashi kabir Mu'azu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Najashi kabir Mu'azu:

Videos

Share

Category


Other Media in Gwarzo

Show All

You may also like