Jama,atu online

  • Home
  • Jama,atu online

Jama,atu online صلى الله عليه افضل سلاةوسلم

09/01/2025

Maulana Sharif Sani Janbolo R,A

•Sakon Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo{RTA} Zuwa Ga Dalibai Dasauran Mabiyansa Na Duniya Bakidaya👇👇 "Kada Wanda Yasak...
25/12/2024

•Sakon Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo{RTA} Zuwa Ga Dalibai Dasauran Mabiyansa Na Duniya Bakidaya👇👇

"Kada Wanda Yasake Yayi Raddi Don Wani Ya Zageni Kok*ma Yafadi Wata Magana Maras Dadi Akaina, Duk Wanda Yayi Raddi Saboda An Zageni Wallahi Banyafemasa Ba! Kuma Baya Cikin Masoya Na! Kubarsu Kawai Daman Ni Nafi Zogale Zaguwa, Kuma Da'ace Zagi Yana Fitowa Ajikin Wanda Ake Zaga Bansan Adadin Wanda Za'a Gani Ajiki Na Ba.

Amma Idan Annabi(SAW) Aka Taba Kok*ma Wani Yafadi Magana Maras Dadi Akansa Ina Goyan Bayan Kufito Kukaryatashi Kowanene! Sannan Kufadi Girma Da Matsayin Annabin Don Zuciyarsa Tayi Bindiga Ta Fashe💔

Wannan Shine Kiran Baba Sidi Kuma Muna Fatan Munji Zamuyi Amfani Dahakan, Kada Wani Yazigaka Kok*ma Don Kaji Wani Yafadi Magana Maras Dadi Akansa Kace Zakayi Raddi, Idan Kayi Hakan Kaji Abunda Sidin Yace👂 Allah Yabarmu Da Annabi(SAW)

KYAWAWAWAN SUNNONIN ANNABI MUHAMMADU SAW💗 RANAR IDI1. Wankan edih2. Cin abinci kafin zuwa masallacin edih3. Sayya farare...
09/04/2024

KYAWAWAWAN SUNNONIN ANNABI MUHAMMADU SAW💗 RANAR IDI

1. Wankan edih
2. Cin abinci kafin zuwa masallacin edih
3. Sayya fararen kaya
4. Sayya turare
5. Zuwa masallaci a kafa
6. Addu'a yayin tafiya masallaci
7. Ba'a nafilah a masallaci edih
8. Chanza hanyar zuwa data dawo yayin zuwa masallacin edih
9. Kai ziyara ga yan'uwa a ranar edih
10. Yawaita gaisuwa kamar haka taqabbanallahuu minna wamin k*m
11. Yin raka'a biyu bayan saukowa edih.

Katai maka ko kitaima kasanar dawani karka bar/ karki bar wannan sako a wayarku domin duk wanda yayi nuni da kyakkyawa yanada kamasho kamar yadda wanda yayi hani da mummuna yana da kamasho.

Allah ya karbi Ibadun Mu yasa Mu acikin yantattun bayin sa ALFARMAR ANNABI SAW💗

08/04/2024

Wai meye yan uwanmu musulmai s**ayi ne ake musu bakin zalunci a kaduna?

•Wai Mene Gaskiyar Maganar Dawasu Suke Cewa Kai Ba Sharifibane? Wannan Wata Tambayace Dawani Yaiwa Sheikh Sharif Sani Ja...
05/04/2024

•Wai Mene Gaskiyar Maganar Dawasu Suke Cewa Kai Ba Sharifibane?

Wannan Wata Tambayace Dawani Yaiwa Sheikh Sharif Sani Janbulo Kano, A Wani Gidan Radio Lokacinda Akai Wata Fira Dashi📻

Sai Baba Sidi Yabashi Amsa Kamar Haka👉 "To Ina Ruwan Wani Da Nasabar Wani? Ni Daman Banine Nace Ni Sharifibane, Ba Fitowa Nayi Inacewa Ni Sharifine! Ni Sharifine!! (Sunanne Yazo Ahaka)

Ni Kawai Abunda Nake Kururuwa Kullum Akansa Shine~ Atashi A*o Annabi(s.a.w) Kuma Adainamasa Kishiya, Sannan Ina Kirada Agirmama Mahaifan Annabi(s.a.w) Da Iyalan Gidansa Harma Da Manyan Masoyansa(Sahabbai)

Kuma Mai Tambaya Inaso Kagane Cewa Annabi(s.a.w) Yace " Duk Wanda Yaimin Karya(Shi Ba Dan Gidanabane(Ahlil Baiti) Yace Shi Sharifine, To Yatanadi Mazauninsa Acikin Wutar Jahannama".

To Donhaka Ni Idan Naiwa Annabi Karya Dan Wutane, To Kuma Idan Nafadi Gaskiya Wani Yakaryatani Shik*ma Dan Inane?"

Wannan Itace Karshen Amsarda Baba Sidi Yabawa Wanda Yaimasa Wannan Tambayar, Sannan Itace Amsa Gaduk Masu Irin Wannan Tambayar, Saboda Nasan Bashikadai Bane Akwaisu Dayawa.

🤲Ya Allah Kakarawa Maulaya Kusanci Da Annabi🤲

© MudaMudassir Dan Jaridan Annabi

Muna SonkaMuna Alfahari DakaiMuna jinka a zuciyoyinmuSaboda Manzon Allah SAW.
29/03/2024

Muna Sonka
Muna Alfahari Dakai
Muna jinka a zuciyoyinmu

Saboda Manzon Allah SAW.

Waye Sayyidina Aliyu ( RA ) عَلِيّ بْن أَبِي طَالِب; ?Dan kabilar (Banu Hashim Bakuraishe) Mahaifinsa; Abu Talib ibn 'Ab...
29/03/2024

Waye Sayyidina Aliyu ( RA ) عَلِيّ بْن أَبِي طَالِب; ?

Dan kabilar (Banu Hashim Bakuraishe) Mahaifinsa; Abu Talib ibn 'Abd al-Muttalib Mahaifiyarsa; Fatimah bint Asad.

Sayyadi Aliyu Radiyallahu Anhu, shi ne Aliyu Dan Abu-Dalib, babansa Abu-Dalib dan-Uwan mahaifin Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama ne, k*ma shine mijin Fatima Radiyallahu Anha diyar Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama.

Shi ne Khalifa na hudu daga jerin Khalifofin Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama, yana daya daga cikin wadanda akayi wa bushra da Aljannah.

Sayyadi Aliyu dan-uwan Annabi ne k*ma surikinsa ne. Ana masa kinaya da Abul-Hassan ko Abut-Turab. Mahaifiyar sa ita ce Fatima Diyar Asad dan Hashim.

Sayyadi Aliyu Jarimi ne, Mai fahimtar Al-Kur’ani ne da Sunnah, Adali ne, Mai Zuhudu ne, Mai Ilimi ne k*ma ga kunya, Aliyu nada Hikima da Fasaha, Allah yakara masa Rahama. Amin.

FALALAR SAYYADI ALIYU RADIYALLAHU ANHU

Hadisai sun inganta daga Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama, a cikin falalar Sayyadi Aliyu kamar Haka:

1. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Duk wanda na zamo shugabansa k*ma majibincin lamarinsa to, Aliyu ma shugabansa ne. (Ibn Maja 4/335)

2. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Lallai babu mai son Aliyu sai mumini, k*ma babu mai kin Aliyu sai Munafiki. (Ibn Maja 98)

3. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Aliyu daga gareni yake nima daga Aliyu nake. ( Tirmuzi 2931)

4. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: kallon Aliyu ibada ne. (Tarikh al- Khulafa p171).

5. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama yace: Matsayin Aliyu a gurina kamar matsayen Haruna ne ga Annabi Musa (Bukhari da Muslim)

6. Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama ya daura shi akan gadonsa lokacin Hijira zuwa Madina k*ma ya danka amarnar ajiyar kuraishawa a hannun sa.

7. Sayyadi Aliyu ya yi Jihadi tare Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama don daukaka Addinin Allah, k*ma ya halacci duk yakunan Annabi banda yakin Tabuka.

Bayan tsawon Rayuwa a cikin Imani, Sayyadi Aliyu Radiyallahu Anhu, yayi Shahada

Ma'anar Sharifta shine ɗaukaka!Shi kuwa ilimi daraja ce daga Allah!!Ɗabi'u masu kyau sune musulunci!!!Duk nasabar ka ida...
29/03/2024

Ma'anar Sharifta shine ɗaukaka!
Shi kuwa ilimi daraja ce daga Allah!!
Ɗabi'u masu kyau sune musulunci!!!

Duk nasabar ka idan aikin ka ya jinkirta to babu shakka ba zatai maka rana ba, kabar tina alaƙar ka da wane a'ah kafi maida hankali akan shi wanen mai yayi ya samu kusanci da Allah har kake sha'awar raɓa kanka dashi ko kake alfahari dakai jinin sa ne, na san wani Sharifi da ya damu da Annabi ﷺ sosai k*ma yake kokarin koyi dashi da tsayawa akan shari'a.

Tarin ilimi bashi bane a'ah, aiki da ilimin shine ainihin haƙiƙar fa'idar ilimin da k*ma amfanin sa, malamai da yawa sun kasance fajirai saboda rashin aiki da abinda s**a sani na ilimi, dan haka Annabi ﷺ yace mana ku roƙi Allah ya baku ilimi mai amfani, k*ma ku nemi tsari daga ilimin da bashi da amfani, nasan wani malami da kullum furuncin sa akan Annabi Muhammadu ﷺ ne, ba zaka taɓa ji yana zagin wani ko raddi wa wani ba, shi barshi akan koɗa Shugaban Halitta.

Ɗabi'u masu kyau sune suke nuna ainihin addinin musulunci, k*ma sune abu mafi nauyi a mizanin mumini, mai kyawawan ɗabi'u yana riskar darajar wanda ya raya dare yana bautar Allah k*ma ya yini yana azumi, mutum mai kyawawan ɗabi'u babu shakka mutum ne mai daraja da haiba a cikin mutane k*ma mutane zasu ji daɗin mu'amala dashi a ko yaushe, nasan wani mutumin kirki a zamani na mai kyawawan ɗabi'u.

Barka da Shan ruwa Masoyin Annabi ﷺ Sharif Sani Janbulo Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, ya kara maka kusanci da Sayyidina Rasulullah, ya cika maka burin ka na alkhairi.

JAMA'ATU MEDIA

❝Daga Son Allah da Annabi ﷺ Sai Kuma Iyaye Babu Wani Malamin ka da Yafi Baban Ka, Ba Wani Shehun Ka da Yafi Baban Ka, Iy...
25/03/2024

❝Daga Son Allah da Annabi ﷺ Sai Kuma Iyaye Babu Wani Malamin ka da Yafi Baban Ka, Ba Wani Shehun Ka da Yafi Baban Ka, Iyaye a Gaba Suke

وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا

Fardu Aini ne Kowa Ya tashi Ya Kare Haqqin Annabi ﷺ Ba Fardu Kifaya bane, Haka Kuma Malamai Suma Dole Suyi ba Maganar Aqida Malam, tunda Ba Aqida a Cikin Kalmar Tauhidi, Babu Aqida a Cikin Sallah, Azumi, Zakkah Amma Ka Isa Kace Ba Annabi Muhammad ﷺ a Cikin Wadannan Ibadun?

Idan An Kauda Aqidun Gaba daya Ba Za'abi Annabi ﷺ ba Kenan? Annabi bazaima Rana ba Kenan Sai da Aqida? Ita Aqidar Meye Ranar ta In bata Kare Fiyayyen Halitta ba? Bata da Wani Rana...

Duk Wanda Aqidar Sa Ba Wajen Annabi ﷺ Zata Kai Shi ba batai masa Rana ba, Dan Duk Wanda Kake tsammani da Girma Zato Ne, Idan Ba Zato Bane Ina Ayar? Ina Hadisin? Ina Aka Nuna? Ni Annabi Na Zato Ne???❞

يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ شَاهِدًا وَمُبَشِّرًا وَنَذِيرًا

وَدَاعِيًا إِلَى اللَّهِ بِإِذْنِهِ وَسِرَاجًا مُّنِيرًا

وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ بِأَنَّ لَهُم مِّنَ اللَّهِ فَضْلًا كَبِيرًا

- Shariff Sani Janbulo (H)

Allah yakarawa Annabiﷺ Daraja
22/03/2024

Allah yakarawa Annabiﷺ Daraja

Ma'anar Sharifta shine ɗaukaka!Shi kuwa ilimi daraja ce daga Allah!!Ɗabi'u masu kyau sune musulunci!!!Duk nasabar ka ida...
21/03/2024

Ma'anar Sharifta shine ɗaukaka!
Shi kuwa ilimi daraja ce daga Allah!!
Ɗabi'u masu kyau sune musulunci!!!

Duk nasabar ka idan aikin ka ya jinkirta to babu shakka ba zatai maka rana ba, kabar tina alaƙar ka da wane a'ah kafi maida hankali akan shi wanen mai yayi ya samu kusanci da Allah har kake sha'awar raɓa kanka dashi ko kake alfahari dakai jinin sa ne, na san wani Sharifi da ya damu da Annabi ﷺ sosai k*ma yake kokarin koyi dashi da tsayawa akan shari'a.

Tarin ilimi bashi bane a'ah, aiki da ilimin shine ainihin haƙiƙar fa'idar ilimin da k*ma amfanin sa, malamai da yawa sun kasance fajirai saboda rashin aiki da abinda s**a sani na ilimi, dan haka Annabi ﷺ yace mana ku roƙi Allah ya baku ilimi mai amfani, k*ma ku nemi tsari daga ilimin da bashi da amfani, nasan wani malami da kullum furuncin sa akan Annabi Muhammadu ﷺ ne, ba zaka taɓa ji yana zagin wani ko raddi wa wani ba, shi barshi akan koɗa Shugaban Halitta.

Ɗabi'u masu kyau sune suke nuna ainihin addinin musulunci, k*ma sune abu mafi nauyi a mizanin mumini, mai kyawawan ɗabi'u yana riskar darajar wanda ya raya dare yana bautar Allah k*ma ya yini yana azumi, mutum mai kyawawan ɗabi'u babu shakka mutum ne mai daraja da haiba a cikin mutane k*ma mutane zasu ji daɗin mu'amala dashi a ko yaushe, nasan wani mutumin kirki a zamani na mai kyawawan ɗabi'u.

Barka da Shan ruwa Masoyin Annabi ﷺ Sharif Sani Janbulo Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, ya kara maka kusanci da Sayyidina Rasulullah, ya cika maka burin ka na alkhairi.

Khalifa Habeebu Rasulullah II
Thursday, 21st March 2024.

BAREWA TAKAWO KARA WAJEN ANNABI (SAW)Wata rana Manzon Allah (SAW) yana tafiya a bayan garin Madina, sai ya ji an kira sh...
17/03/2024

BAREWA TAKAWO KARA WAJEN ANNABI (SAW)

Wata rana Manzon Allah (SAW) yana tafiya a bayan garin Madina, sai ya ji an kira shi,

“Ya Manzon Allah (S.A.W), Ya Annabin Allah !!!”
Sai Manzon Allah (SAW) ya duba baya bai ga
kowa ba, sai ya k*ma jin kiran, sai yabi inda
sautin yake fitowa, da ya isa wajen sai ya
iske wata barewa a daure, a gefe k*ma ga
wani Balaraben kauye yana kwance yana
barci.
Sai Barewa tace da shi “Ya Rasulullahi,
wannan mutumin ya farautoni alhali ni ina
da'ya'ya guda biyu a wancan kogon dutse,
ka taimaka min ka sake ni naje na shayar da
su nono sannan na dawo”.
Sai Annabi yace"anya kuwa zaki dawo?"
Sai Barewa tace"idan har ban dawo ba, Allah
yai min azabar da zai yiwa mai cin
Rashawa".
Sai Annabi ya kwance ta tafi.
Da Barewa ta cika alkawari ta dawo, sai
Annabi ya kama'kafarta yana ƙoƙarin
daureta da igiya, sai Balaraben Kauye ya
farka daga bacci.
"kai ne fansar uwata da ubana ya Manzon
Allah, nine na farauto ta ko kana da
bukata?".
Inji Balaraben kauye.
Sai Annabi yace"na'am ina da bukata"sai
Balarabe yace"na baka ita Ya rasulullah".
Sai Annabi (S.A.W) ya sake ta, ta koma
wajen'ya'yanta.Tana tafiya tana cewa"Na
shaida babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah, na k*ma Shaida Annabi Muhammad
Manzon Allah ne."

Jama'a idan muka duba zamu ga
abubuwan da wannan kissa take koyarwa
kamar haka:
1. Cika alkawari.
2. Tausayin uwa akan'ya'yan ta.
3. Neman halal ta hanyar farauta.

Daure Ka Rubuta Amin Matukar Ka Karanta
Saboda bamusan tawa Za'a Kar6a Ba.

اللهم صل على سيدنا محمد

AMEEEN YA ARHAMAR RAHIMEENA YA HAYYU YA QAYYUM ♥️🙏♥️

- Duk wuya ina nan ban motsi daɗi nake nema!- Sallama da ƙarawa Baba anata shan fama!- Rabbana ya ida ma da nufi bara na...
17/03/2024

- Duk wuya ina nan ban motsi daɗi nake nema!
- Sallama da ƙarawa Baba anata shan fama!
- Rabbana ya ida ma da nufi bara nazo yima!
- So nake a loda min in faɗa indaina lalaci!

- Bege Rahimahullah.

Zuciya Tana Matukar Sonka Idanuwa Suna Mararin Ganinka Annabi Muhammaduﷺ🥰
16/03/2024

Zuciya Tana Matukar Sonka
Idanuwa Suna Mararin Ganinka
Annabi Muhammaduﷺ🥰

Maulanmu Sidi kenan  Shugaba  Kungiyar Jama'atu Ahbabu RasulullahAllah ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana
11/03/2024

Maulanmu Sidi kenan Shugaba Kungiyar Jama'atu Ahbabu Rasulullah

Allah ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana

•Shin Kuntaba Halartar Taron Mauludin Annabi(SAW) Mai Taken👉Bangajiyar Ayyamu Wudil? Tarone Wanda Ake Gabatar Duk Shekar...
08/03/2024

•Shin Kuntaba Halartar Taron Mauludin Annabi(SAW) Mai Taken👉Bangajiyar Ayyamu Wudil?

Tarone Wanda Ake Gabatar Duk Shekara Agarinsu Marigayi Umar Abdul'aziz Baba(Fadar Bege) Wanda Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo Yake Jagoranta Tareda Rundunar Sha'iran Jama'atu Dama Sauran Masoya Annabi(SAW)

Insha Allahu Abana Taron Zai Kasance Kamar Haka:

Rana: Asabar Maizuwa 28/Sha'aban/1445H Daidai Da 9/March/2024.

Wuri: Kofar Fada Cikin Garin Wudil, Bayan Babban Masallacin Juma'a Na Garin Wudil.

Wannan Sakon Gayyatane Kaitsaye Daga Baba Sidi Zuwa Ga Masoya Annabi(Wadanda Allah Yabawa Ikon Zuwa) Musamman Local Government Dasuke Kusa Da Wudil Dama Sauransu, Duk Muhadu Don Taya Junanmu Murna Da Sada Zumunci Bakidaya, Allah Yasa Ayi Damu Amin.

Jama'atu Media Kano Zonee

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama,atu online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jama,atu online:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share