
22/12/2024
Dry socket (ko kuma albeolar osteitis) yana faruwa bayan an cire haƙori idan jinin da ya kamata ya toshe wurin cire haƙorin ya zube ko bai samu damar yin toshewa ba, wanda ke barin kasan kashin haƙori da jijiyoyi a buɗe. Wannan yana haifar da zafi mai tsanani, kumburi, da kuma wari a bakin.
Abubuwan da ke iya haddasa shi sun haɗa da shan sigari, rashin tsaftar baki, da amfani da strow. Magani ya haɗa da rage zafi, tsaftace wurin da aka cire haƙorin, da kuma amfani da magungunan toshewa(dressing )
Idan kana jin alamar dry socket, ka gaggauta ganin likitan haƙori don samun kulawa ta dace.
RDth. NAFIU GARBA.