Imam karafi sani

Imam karafi sani ANNABI NE MAFITA
(3)

30/01/2025

Malam Jafar Adam πŸ’₯ ???

29/01/2025

Yana Daga Sharuddan ƊariΖ™ar Tijjaniyya
Sallah a Jam'i.

29/01/2025

WaΙ—anda s**a yi rajista na darasin Content Creation (Social Media Management) Insha Allahu yau zamu fara gabatar da karatu.

Wannan Program din zai koyar da mutane yanda ake mu'alama da social media a ilmance harma da hanyoyin samun kuΙ—i a internet, zamu koyi Content Creation da dama wanda zasu mana amfani a mu'alama mu yau da gobe

Koyarwan zai kasance a manhajar Telegram Channel da misalin karfe 9:00pm zuwa 10:00pm na dare a ranakun litinin zuwa juma'a.

Ga wadanda s**a rijista damu zasu tura receipt of payment nasu ga wannan 08032693340 (Whatsapp Only) da cikakken sunan sa.

Don haka ga masu bukatan yin rajista kafin wani lokaci zamu biya ta wannan link din
βœ… https://paystack.com/pay/0sfcj-wlgc

Allah ya amfanar damu baki daya. Amiin

Babangida Alhaji Maina
CEO/MD Fityanu Media

28/01/2025

SHEIKH (Prof.) IBRAHIM AHMAD MAQARY (R) Yana Cewa: "MANZON ALLAH(S.A.W) Ba Irinmu Bane, Domin Da Kansa Yake Cewa. 'Ayyukum Ka Hai'atiy ???

Ma'ana: Wanene Ke Da Structure Irin Tawa???".

To Kuma Gaba 'Daya Wadanda S**a Kafirce Ma Annabawansu Sun Kafirce Ne Saboda Sun 'Dauka Kuma Sun Ce Annabinsu Mutum Ne Kamarsu...",

'Yan'uwa Mu Kula... A Kula... ANNABI Ba Irinmu Bane.. Halitta Ne Wanda a Hadisin Bukhari Aka Ruwaito Cewa:

Lokacin Da SAYYIDUNA ALI(R.A) Ya Hau Kan Kafadarsa Lokacin FATHU MAKKAH Sai Da Ya Ga Kamar Zai Iya 'Dauko Taurarin Sama,

Ku Duba Tsawon Ka'aba Amma SAYYIDUNA ALI(R.A) Yana Hawa Kafadan ANNABI(S.A.W) Ya Ciro Wadannan Gumakan Kuma Ka'aba Kowa Ya San Tsawonta Dai... A Nutsu/Kula Dai".

LA ILAHA ILLALLAH........

ALLAH YA 'KARA TSARE MANA IMANINMU, YA 'KARA MANA 'KAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W) AMEEN

Shugaban majalisar malamai ta Nigeria Kuma malamin da babu Irinsa a Africa (Za'a Iya kiransa da Imamu Siyudi na Biyu)Ya ...
27/01/2025

Shugaban majalisar malamai ta Nigeria
Kuma malamin da babu Irinsa a Africa (Za'a Iya kiransa da Imamu Siyudi na Biyu)
Ya rubuta Littafan musulumci kusan Dari Biyar

Allah ya Kara lfy

27/01/2025
27/01/2025

Sheikh Prof. Ibrahim Maqari Hfz πŸ’―

26/01/2025
25/01/2025

Muna addu'an Allah ubangiji madaukakin sarki ya sakawa kowa da mafificin alkhairi. Amiin

25/01/2025

Karkuyi Fada da Kowa, Karku Zagi Kowa, ko Dukanku Akayi Karku Rama Kune Zakuyi Nasara.

~Shehu Ibrahim Inyss

24/01/2025

Darika Vs Izalah πŸ’₯

22/01/2025

Zamu bude "Online Class" wanda zamu koyawa mutane yan' uwan mu masoya yadda ake amfani da "Social Media" a ILMANCE.

4 Week Course On SOCIAL MEDIA MANAGEMENT mai taken (hanyoyin inganta tsarin yada da'awah 2025) wanda kamfanin Fityanu Media zata dauki nauyin koyarwa tare da hadin gwaiwa (Partner) na wasu kamfani da s**a hada da:

- Alfijir News,
- Arewa Media Writers,
- Sufi Media Connect, da
- Sautul faidha Social Media,

zamu gabatar da tutorial insha Allah.

Kana hawa social media amma baka taba yin ko'ina irin course na social media ba, wannan kuskure ne babba ya zama kana abunda bashi da manufa kenan a rayuwar ka.

Yin abu kafin sanin sa shine mafi kwau a rayuwar dan'adam, course na social media zai taimake ka sosai a rayuwar,

Zamu fara training a ranar 27th January, 2025 - 27th Rajab, 1446Ah, kayi register kafin lokacin

Masu sha'awan yin register training ga link
βœ… https://paystack.com/pay/0sfcj-wlgc

Akwai tutor kwararru a kowanne bangare.

Allah ya amfanar damu baki daya, tabbatar mana da alkhairi. Amiiiin Yaa ALLAH

15th January, 2025
Babangida A. Maina
Founder MD/CEO Fityanu Media

22/01/2025

A ranar 21 ga Janairu, 2025, majalisar dokokin Iraki ta amince da gyare-gyare ga Dokar aure a kasar, wanda majalisar ta mika fatawa ga maluman kasar. Don bada fatawa.

Masu s**a sun bayyana cewa wannan gyare-gyare na iya halatta aure ga yara mata masu shekaru kasa da 9 a wasu mazhabobin addini. Asalin dokar da aka kafa a shekarar 1959 ta sanya mafi karancin shekarun aure ya zama shekaru 18, don kare hakkokin mata da kuma tabbatar da hadin kai a cikin tsarin iyali. Sai dai, gyaran da aka yi yanzu ya ba wa malamai damar bin ra'ayoyin addini wanda hakan ka iya rage shekarun aure zuwa kasa sosai.

Masu goyon bayan wannan dokar, musamman 'yan majalisar dokokin Shi'a masu ra'ayi na rikau, sun ce gyaran ya dace da ka'idojin Musulunci kuma zai rage tasirin al'adu na Yammacin duniya. Sai dai, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da masu fafutuka sun nuna damuwa sosai, sun ce, wannan doka zai iya jefa rayuwar yara mata cikin hadari, tare da tauye hakkokinsu.

Wani dan gwagwarmaya, Intisar al-Mayali, daga kungiyar kare hakkin mata ta Iraqi Women's League, ya bayyana cewa wannan gyara zai kara yawan auren wuri, yana karya hakkokin yara tare da lalata tsare-tsaren kariya da s**a shafi saki, kulawar yara, da gadon dukiya.

Zaman majalisar da aka amince da wannan gyara ya kasance cikin rudani, inda aka samu korafe-korafe kan yadda aka gudanar da taron. Wasu 'yan majalisa sun yi ikirarin cewa ba a cika ka'idojin taron ba, amma duk da haka Kakakin Majalisar, Mahmoud al-Mashhadani, ya yaba wa gyaran dokokin, yana mai cewa matakan suna inganta adalci.

Wannan matakin ya jawo fushin kungiyoyin kare hakkin mata da yara, wadanda s**a bayyana dokar a matsayin koma baya mai girma ga hakkin mata da yara a Iraki. Lauya Mohammed Juma ya ce: "Wannan yana nufin karshen hakkokin mata da yara a Iraki."

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da al'ummar kasa da kasa na ci gaba da bibiyar lamarin, suna kira ga gwamnatin Iraki da ta sake nazarin wannan gyara don kare makomar mata da yara mata a kasar.

Address

Bakin Kasuwa
Chafe
632101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam karafi sani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Imam karafi sani:

Videos

Share