Zamfara Post

Zamfara Post Barka Da Zuwa Zamfara Post Inda Zaku Samu Labaran Duniya da Wasanni Tare da Labaran Nishaɗantar daku

ALLAH SARKI: Wata mahaifiya ta rungume ɗanta bayan an ƙaddamar da su a matsayin sabbin jami'an tsaron 'yan sandan Nijeri...
24/01/2025

ALLAH SARKI: Wata mahaifiya ta rungume ɗanta bayan an ƙaddamar da su a matsayin sabbin jami'an tsaron 'yan sandan Nijeriya.

Tarzoma ta Barka a Babban ofishin Hukumar ZAROTA ta karamar hukumar Mulkin Gusau, inda wasu bayanai ke cewa jami’an huku...
16/01/2025

Tarzoma ta Barka a Babban ofishin Hukumar ZAROTA ta karamar hukumar Mulkin Gusau, inda wasu bayanai ke cewa jami’an hukumar wani abu ya shiga tsakaninsu da masu Achaba inda har wuyan dan Achaba ya karye.

Bawan Allah Ance wannan shine sojan da ya kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan Halilu Sububu, da wasu gaggan yaran ɗan bind...
15/09/2024

Bawan Allah

Ance wannan shine sojan da ya kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan Halilu Sububu, da wasu gaggan yaran ɗan bindigar a Zamfara.

Suna daga cikin yan ta'addan da s**a addabi al'ummar jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa.

An tabbatar da jarumtar wannan matashi, domin an tabbatar harda hannu yake k**a ƴan bindiga.

Muna roƙa masa Allah ya kare shi a wannan aiki da yake yi. Ya kuma ƙara bashi nasara da sauran jami'ai abokan aikinsa.🤲

El-Hamees Mohammed

Ko kun san cewa Halilu Sububu Buzu, ɗan ta'addan da ya gamu da ajalinsa a hannun jaruman sojojin Najeriya a Zamfara, shi...
13/09/2024

Ko kun san cewa Halilu Sububu Buzu, ɗan ta'addan da ya gamu da ajalinsa a hannun jaruman sojojin Najeriya a Zamfara, shi ne uban gidansa Bello Turji? Wannan wata alama ce dake nuna cewa kwanakin Turji sun kusa ƙarewa. Mu ci gaba da yi wa sojojin mu addu’a domin ci gaba da samun nasara.

19/08/2024

Shugaban Kasa Tinubu ya mai da tallafin man fetur

Allah yasa haka ya zama silar samu sauki 🤲

BABBAR MAGANA: Young Sheikh Ya Jagoranci Źanga-Źangar Lumana A Garin ZariaA yau Alhams 1 ga watan Agusta 2024 matashin M...
01/08/2024

BABBAR MAGANA: Young Sheikh Ya Jagoranci Źanga-Źangar Lumana A Garin Zaria

A yau Alhams 1 ga watan Agusta 2024 matashin Malamin musuluncin nan, Young Sheik ya jagoranci źanga-źangar lumana a garin Zaria. Inda ya yi kira ga gwamnati da ta mayar da tallafin man fetur tare kuma da kawo karshen ťà''aďdanci,

Abincin da take ýunkuri rabawa wasu 'ýan ťsirarun mutane ba shine mafita ba.

Zanga zanga sassa daban daban katsina kano kaduna ibadan lagos sokoto zamfara taraba dadai sauransu.✍️ Muh'd Muh'd Salis
01/08/2024

Zanga zanga sassa daban daban katsina kano kaduna ibadan lagos sokoto zamfara taraba dadai sauransu.

✍️ Muh'd Muh'd Salis

Jahar Naija. sunfara Zanga-Zangan lumana kuma insha Allahu babu tsayawa sai burin mu ta cika Zanga-Zanga Babu Fashi
29/07/2024

Jahar Naija. sunfara Zanga-Zangan lumana kuma insha Allahu babu tsayawa sai burin mu ta cika

Zanga-Zanga Babu Fashi

Da dumi'dumi: 'Yan Majalisar dattijai da na Tarayya sun fasa Hutun da s**a dauka, Yanzu Majalisar Tayi kira ga membobint...
29/07/2024

Da dumi'dumi: 'Yan Majalisar dattijai da na Tarayya sun fasa Hutun da s**a dauka, Yanzu Majalisar Tayi kira ga membobinta da su dawo Bakin Aiki domin Akwai zaman gaggawa da ya taso.

Alhaji ka taimaka min ka saya min gari ko rabin gwangwani ne -- inji Wata karamar yarinya Wannan hoton ba wai burge ni y...
24/07/2024

Alhaji ka taimaka min ka saya min gari ko rabin gwangwani ne -- inji Wata karamar yarinya

Wannan hoton ba wai burge ni yayi na ɗaukesa ba, takaici ne kawai nayi da ganin wannan yarinyar mai matsakaicin shekaru wacce bata wuce shekaru 4 a Duniya ba.

Na sauka daga mota kenan a birnin Katsina sai ta same ni tana cewa, "Alaji a taimaka a saya mani gari yunwa nake ji. Wannan hali na kuncin rayuwa kullum abinda ake fama da shi kenan a sassan fadin Najeriya. Subhanallah!!! Allah ya kawo mana sauki alfarmar Annabi da Alkur’ani.

Daga : Dan jarida Alhaji Sani Zangina

Wannan inuwar wani shahararren malamin addinin musulunci ne da Allah ya yi wa rasuwa a Arewacin Najeriya.Shin waye zai i...
19/07/2024

Wannan inuwar wani shahararren malamin addinin musulunci ne da Allah ya yi wa rasuwa a Arewacin Najeriya.

Shin waye zai iya faɗa mana sunansa?

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin Sarakuna Uku a Kano masu daraja ta Biyu1. Ya nada Alhaji Muha...
17/07/2024

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin Sarakuna Uku a Kano masu daraja ta Biyu

1. Ya nada Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye (kafin nadinsa shine Hakimin Rogo)

2. Ya nada Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano (kafin nadinsa Hakimin Bunkure)

3. Sannan ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya (tsohon Sarkin Gaya).

Wane fata zaku yi musu?

YANZU-YANZU: Umar Bush ya samu muƙami a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu.Ya zama SA Entertainment a ofishin bab...
15/07/2024

YANZU-YANZU: Umar Bush ya samu muƙami a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu.

Ya zama SA Entertainment a ofishin babban mai bawa shugaban ƙasa shawara na musamman Hon Muhammad Abba Isa.

Wane fata za kuyi masa ?

Daga Salisu Editor

14/07/2024

HND holders can now apply for admission for Public Health and Health Information Management (HIM).

Alummar Jihar Zamfara Mu Farka, Ga Dama Ga Matasan Mu a ICONIC OPEN UNIVERSITYMuna kira da jan hankali ga shugabannin mu...
12/07/2024

Alummar Jihar Zamfara Mu Farka, Ga Dama Ga Matasan Mu a ICONIC OPEN UNIVERSITY

Muna kira da jan hankali ga shugabannin mu da matasa na jihar Zamfara ga wata damar raya matasan jihar mu da ilimin mai zurfi wanda matasa za su amfana domin cigaban jihar Zamfara.

Daga cikin dalillai na isar da wannan sakon shine ita wagga jami'a ta ICONIC UNIVERSITY tazo da sabon tsarin karatu da ake kira ‘distance learning’ na zamani da keda tsare tsare k**ar haka;

1. Tana da center a nan Gusau a cikin CIS Gusau ko ince makarantar kulliyar Gusau
2. Tsarin karatun ta ‘distance learning’ ne wanda baya bukatar ka baro duk local government da kake ka tare dindindin a makaranta.
3. Tana da lasisi da hukumar jami'o'i ta kasa NUC wato dukkanin kwasakwasanta amintattu ne kuma zaka samu shaidar NYSC bayan kammalawa.
4. Baka bukatar rubuta jarabawar JAMB sai dai idan an baka admission sai kaje kawai Ofishin JAMB kayi rijista a karkashin tsarin distance learning.
5. Suna bada DE admission ga masu Diploma, ND, NCE ko HND
6. Kudin karatu daga 65,000 ne zuwa 100,000 a kowane zangon karatu ga kwasa-kwasan da take gudanarwa; BSc. Public Health, BNSC Nursing, B.HIM Health Information Management, B.Sc. Computer & Information Technology, B.Sc. Software Engineering, B.Sc. Mass Communication, BSc. International Relations & Diplomacy, B.Sc. Criminology and Security Studies, B.Sc. Accounting, B.Sc. Business Administration, B.Sc. Public Administration, B.A. English Language da kuma B.A. Islamic Studies
7. Tsarin karatun ta, kaso 70 ne zaka kayi online kaso 30 kuma a nan center ta, k**ar su practical da jarabawar a karshen kowane zangon karatu.

Wannan ba karamar dama bace ga shuwagabannin mu da yan siyasa domin su taimakawa yayan tallakawa da matasan mu, ma'aikatan gwamnati, matan aure su samu ilimin a saukake ta wannan jami'a duba da yanayin matsin tattalin arziki da wasu dalibai ma basa iya tsayawa su gudanar da karatun su a jami’oin jeka ka dawo ko zama dindin din saboda ko kuddin abinci da zirga zirg

20/06/2024

Gwamnan Kano ya bada umurnin rushe gidan Sarki na Nasarawa inda Sarki Aminu Ado yake zaune.

~ Comr Abba Sani Pantami

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba kungiyar kwadago tabbacin cewa gwamnatin sa ta kuduri aniyar biyan mafi karancin albashi...
03/06/2024

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba kungiyar kwadago tabbacin cewa gwamnatin sa ta kuduri aniyar biyan mafi karancin albashi sama da Naira dubu sittin 60k Sai dai za a ci gaba da tattaunawa har tsawon mako guda har sai an cimma matsaya.

Kungiyar kwadago za ta kira taron dukkan mambobinta a gobe Talata.

Cikin Shekara Ɗaya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Ya Sharewa 'Yan Najeriya Hawaye Da Ayyukan Raya Ƙasa,Cewar Sen Abdula...
02/06/2024

Cikin Shekara Ɗaya Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Ya Sharewa 'Yan Najeriya Hawaye Da Ayyukan Raya Ƙasa,

Cewar Sen Abdulaziz Yari

Address

Gusau
632101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamfara Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share