22/01/2024
Gidauniyar Mallam Adamu wacce take ƙarƙashin iko da kulawar Alhaji Musa Adamu (Mamallakin Khadija University Majia) ta shirya tsaf domin bada gurbin karatu kyauta a jami'ar ta Khadija University da ke garin Majia a fannoni daban-daban.
Waɗanda da za su ci gajiyar wannan shirin sune ɗaliban da suke da Credit biyar zuwa sama a SSCE ɗinsu, suke kuma da maki 130 ko sama da haka a JAMB ɗin shekarar 2022 da 2023.
Ɗalibai za su iya zuwa ɗaya daga cikin wannan makarantun domin karɓar Form su kuma cike nan take a farashin Naira dubu biyar kacal (5000).
Za'a fara siyar da Forms ɗin daga 22 ga watan January zuwa 2 ga watan Febuary.