North East Daily Reporters

North East Daily Reporters News at its break

01/10/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Idris Muhammad, Aliyu Bappa, Muhammad Garba Yeerreemh

23/08/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Muhammad Ahmad Hassan, Abbati Bobo Abbati Bobo

A bamu dama mu fara biyan sadakin mazan nan inaga zaifi tunda sun kasa biyan namu 😃😃😃😃Duk wacce taga wanda takeso ta biy...
03/06/2024

A bamu dama mu fara biyan sadakin mazan nan inaga zaifi tunda sun kasa biyan namu 😃😃😃😃

Duk wacce taga wanda takeso ta biya sadakinsa kawai 🤣

Cewar Wata Matashiya- Jamila Ibrahim

Cikiya! Cikiya!! Cikiya!!!Ana cikiyan wannan Baiwar Allah mai suna Hasiya Usman Ciroma,  (Kanwace Garemu) Yar Shekara 20...
30/04/2024

Cikiya! Cikiya!! Cikiya!!!

Ana cikiyan wannan Baiwar Allah mai suna Hasiya Usman Ciroma, (Kanwace Garemu) Yar Shekara 20 Kuma Matar Aure Ce.

Ta fita daga gidan Iyayenta A Unguwar Hammadu Kafi Byass Tun Ranan Alhamis 25/04/2024 da misalin karfe 11:00 na safe da Nufin Zuwa Unguwar Sarankiyo Tsallaken Kwari Unguwar da Take da Zaman Aure Domin Amsar Kudin da Take Bi Bashi.

Tun Daga Fitarta Ba Ta Dawo Ba Har Yau Kuma Haryanxu Da Nake Wanan Magana 30/04/2024 Kwanaki Hudu (4) Kenan Haryanzu Babu Labarinta

Bayan Ga Haka Kuma Tana Fama Da Matsalar Makarai

Don Haka Muna Rokon Duk wanda Allah yasa ya ganta Ya Sanar Da Hon Mustapha Danyerwa Gombe

Ko A Tuntubemu Akan Wanan Lambobin Wayar

08066551011
09160168868
07040336969
08130026670

Don Allah A Taya mu Share Ko Allah Zai Saka A Dace🙏🏽

PRESS RELEASEDPDP conderm approval of 43 Billion for Governor's residence, High court and Assembly complex amidst hardsh...
29/03/2024

PRESS RELEASED
PDP conderm approval of 43 Billion for Governor's residence, High court and Assembly complex amidst hardship in Gombe State - Hon Sabo Sani Labaran

INNA'LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RA'JIUN😭Allah Ya Yiwa Maulanmu Khalifan Shehu Manzo Gombe Rasuwa A Yau Juma'a.Jana'iza Baya...
09/02/2024

INNA'LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RA'JIUN😭

Allah Ya Yiwa Maulanmu Khalifan Shehu Manzo Gombe Rasuwa A Yau Juma'a.

Jana'iza Bayan La'asar Ƙarfe 04:30pm

24/01/2024

Inna Lilllahi Wa Inna Ilaihi Raji'un
Allah ya jarrabemu da rashin uba kuma dattijo Alhaji Abdulkarim Kwami (A.A.K Motors)

Alhaji Abdulkarim Kwami ya kasance mutum na gari, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin an samar da shugabanci na gari a cikin al'umma. Mutum ne mai son gaskiya kuma mai zaman lafiya da dukkan mutane.

A madadin ni kaina da iyalaina da Kuma Al'ummar Karamar Hukumar Yamaltu Deba ina mika sakon ta'aziyyar mu ga iyalansa da yan uwansa da abokan arziki, ina fatan Allah ya bamu hakurin jure wannan babban rashi.

Allah ya jikansa da rahama, ya haskaka makwancinsa,

Rt Hon Inuwa Garba
Chairman House committee on Science Engineering

Nafiso Ayi Gwaje-Gwaje Kafin A Bizne Idan Kun Samu Labarin RaduwataCewar Wani Matashi - Hon Mustapha Danyerwa GombeInnal...
21/11/2023

Nafiso Ayi Gwaje-Gwaje Kafin A Bizne Idan Kun Samu Labarin Raduwata
Cewar Wani Matashi - Hon Mustapha Danyerwa Gombe

Innalillahi wa Inna Ilaihim Rajiu 😭

Tabbass Mutuwa Gaskiya Ne Kuma Dukkan Wani Mai Rai Wata Ranan Dole Zai Zamanto Mamaci.

Wasiyata Ga Yan Uwa Da Makusanta Na Da Sauran Yan Uwa Da Abokan Arziki A Duk Sanda Aka Samu Labarin Rasuwata Inma A Yanayi Na Jinyace Allah Ya Min Rasuwa Inma Rasuwar Fuji'ah Ce Ina Rokonku da Kada Ayi Gaggawan Bine Ni.

Kafin A Bineni Aje Asibiti Ayi Gwaje-Gwaje Wato (Autopsy) Idan Aka Tabbatar da Cewa Eh Rasuwar Nayi Sai Amin Sutura A Sallaceni K**ar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanadar.

Domin Gaggawan Bune Mutun Yakan Iya Sakawa A Bune Mutun Ba Tare da Ya Rasu ba.

Domin Da Yawwan Hausawan Mu Da Zarar Mutun Ya Rasu Babu Wani Jinkirtawa Da Akeyi Yadda Kasan Allah-Allah Ake Ka Rasu A Samu A Rabu Dakai

Kawaii Sai Kaga An Fara Shirye-Shiryen Bizneka Mai Makon A Jinkirta Ko Aje A Bincika A Tabbatar da Eh Ka Mutu Ko Baka Mutu Ba

Allah Yasa Mu Cika Da Imani😭

ALLAH YA KARA TONA ASIRIN MASU YIWA TSARON NIGERIA ZAGON KASA ASIRIJamian Yan sanda na sirrri sun K**a Rashida Umar da R...
27/09/2023

ALLAH YA KARA TONA ASIRIN MASU YIWA TSARON NIGERIA ZAGON KASA ASIRI

Jamian Yan sanda na sirrri sun K**a Rashida Umar da Rukayya Ladan A garin Akwanga, Dake Jahar Nassarawa dauke da Harsashi Sama da Dubu daya.

Wadannan Mata sun dauko Harsashin ne tun Daga wani Gari da ake kira Fadan_Karshe Dake Karamar Hukumar sangan Jahar Kaduna Zasu Kaiwa yan Bindiga Jeji A kontagora na Jahar Niger .

Ire iren Wadannan Matane suke hana zaman Lafiya a cikin Al'umma

Allah ya Kara tona wa maciya Amanar Tsaraon Kasa Asiri

27/09/2023

Zargin cire idon gawa a Federal Teaching Hospital Gombe ba gaskiya bane,

Daga shafin Hon Sabo Sani Labaran

Ga gaskiyar abun da ya faru daga bakin Dan Mamaciyar da CAN Chairman da kuma Family Doctor din su a cikin Video

K**ar yadda tun jiya wasu suke ta yada jita Jita akan an cire wa wata gawa ido a FTH ba Haka zancen yake ba,

Duk binciken daya kamata Hukumar FTH da Jami'an tsaron su gudanar nayi gwaji duk anyi An kuma tabbatar babu wani sashi daya da aka Cire a jikin Mamaciyar

Dan haka mutane su guji yada Jitajitan da ze kawo hatsaniya, tashin hankali ko rashin Zaman lafiya a cikin Al'umma.

Dayawan Mutane Basu Fahimce Tashar AREWA24 Ba.Dayawan Mutane Sun Jahilci Shirin Da Tashar Arewa24 Take Gudanarwa Mai Sun...
19/08/2023

Dayawan Mutane Basu Fahimce Tashar AREWA24 Ba.

Dayawan Mutane Sun Jahilci Shirin Da Tashar Arewa24 Take Gudanarwa Mai Suna MATA A YAU Haqiqanin Gaskiya Ni Banga Wani Aibu A Cikin Wanan Shirin da Sukeyi Ba.

Mussaman Yadda Naga Da Yawwan Mutanen Mu Sun Jahilci Shirin

To Allah Na Tuba Meye Aibu Don Gari Ya Waye (NA GAIDA MATA NA)

A Kowane Lokaci Nakan Nuna Mata Soyayya Idan Mun Samu Matsala A Zaman Takewar Mu Zan Iya Sunkuyar Dakai Na Bata Hakuri To Meye Laifi A Ciki Don Gari Ya Waye (GAISHE DA ITA) Inaga Wanan K**ar Ba Wani Abu Bane.

Misali: Akan Kaina A Halin Yanxu A Duk Lokacin da Garin Allah Ya Waye Zan Dauki Waya Na Kira Budurwata Na Gaishe Da Ita Naji Ya Take Ya Lafiyarta.

To don Tashigo Gidana Mun Cigaba Da Tafiya A Haka ai ba laifi Bane Inaga K**ar So da Qauna ne Ya Jawo Hakan.

Saboda Inda Bana Sonta Bazanyi Tunanin A Kullum Idan Garin Allah Ya Waye Na Kirata Na Gaishe Ta Ba

Ya K**ata Mutanen Mu Su Lura Da Wanan Idan Har Zamuyi Fada Ko Mu Samu Matsala A Zaman Takewar Mu Na Iya Bude Baki Na Rarrasheta Na Kuma Bude Baki Na Bata Hakuri Inaga Wanan Ai Ba Wani Abu Aciki Sai (Don Garin Allah Ya Waye Na Gaisheki Hakan Ya Zama Laifi)?

Nidai Inada Ra'ayin Girmama Matana da Iyalaina A Kowane Lokaci Idan Akwai Inda Yazo A Qur'ani ko A Hadisi Karna Girmama Mata To Sai Naji👂🏽

Ra'ayin Hon Mustapha Danyerwa Gombe
Dangane da Shirin MATA A YAU Na Tashar Arewa24.

Daga Shafin: Aliyu Nazir OfficerAlhamdulillah! Munyi magana da Baba Shuaibu Abdullahi ( Baba Kar'uzu ) yanzu, na fada ma...
08/08/2023

Daga Shafin: Aliyu Nazir Officer

Alhamdulillah! Munyi magana da Baba Shuaibu Abdullahi ( Baba Kar'uzu ) yanzu, na fada masa halin da muke ciki da wasu masu bukatar taimaka masa kuma ya yarda ya bani account number din shi

Wannan shine account number din Baba na First Bank wanda zaku iya taimaka masa da taimakon ku a ciki. Ubangiji Allah ya bada ikon taimakawa

3034702720
SHUAIBU ABDULLAHI
FIRST BANK

Innalillahi wa Inna Ilaihim Rajiu 😭😭😭Allah Yayiwa Yeriman Gombe Rasuwa
01/08/2023

Innalillahi wa Inna Ilaihim Rajiu 😭😭😭

Allah Yayiwa Yeriman Gombe Rasuwa

Ra'ayin Hon Sabo Sani Labaran daga Jihar Gombe
13/07/2023

Ra'ayin Hon Sabo Sani Labaran daga Jihar Gombe

Innalillahi wa inna ilaihiraji'un,An samu gawar wannan mutumin yanzu a anguwan herwagana layin kotu a kasan gada kusa da...
21/06/2023

Innalillahi wa inna ilaihiraji'un,

An samu gawar wannan mutumin yanzu a anguwan herwagana layin kotu a kasan gada kusa da gidan alh garba wali,

Wanda ya gane shi yazo specialist hospital gombe, ko gombe division, ya Allah ka yi masa rahama da sauran mamatan mu amin.

Uwar Gidan maigirma  Goman jihr GombeHajiya Asma'u Inuwa Yahaya  Uwa Tagari Mai Cikakkiyar K**ala Wacce Tadaura Rayuwar ...
30/03/2023

Uwar Gidan maigirma Goman jihr Gombe
Hajiya Asma'u Inuwa Yahaya

Uwa Tagari Mai Cikakkiyar K**ala Wacce Tadaura Rayuwar Ta Akan Mizanin Addinin Musulilci.
Tabbas Manzan Allah S W A yayi Gaskiya Da Yace Mu Aure Mace Tagari Ma,abociyar Addini Wacce Addini Yashiga Cikin Dukkanin Al,amuran Rayuwar Ta.
Muna Rokon Ubangiji Allah ya Azurtamu Da Mata Nagari Masu Kishin Addinin Musulilci.

30/03/2023 INEC Ta Baiwa Gwamna Inuwa Da Mataimakin Sa, Da Zaɓaɓɓun Ƴan Majalissa Takardun Shaidar Lashe Zaɓe ..Yayinda ...
30/03/2023

30/03/2023

INEC Ta Baiwa Gwamna Inuwa Da Mataimakin Sa, Da Zaɓaɓɓun Ƴan Majalissa Takardun Shaidar Lashe Zaɓe
..Yayinda Gwamnan Ya Yi Alkawarin Gudanar Da Gwamnatin Da Zata Tafi Da Kowa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), a Jihar Gombe, ta gabatar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Muhammadu InuwaYahaya, da mataimakin sa Dr Manassah Daniel Jatau da ƴan majalisan dokokin jihar da aka zaɓa.

Gabatar da takardun shaidar cin zaɓen ya biyo bayan nasarar da s**a samu ne a zaɓen gwamnoni dana ƴan majalisan jiha da aka kammala.

Yayin da Kwamishinan INEC mai kula da Jihohin Gombe, Adamawa da Taraba, Dr Baba Bila ya miƙawa Gwamna Inuwa Yahaya da Mataimakin sa takardar shaidar cin zaɓen, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Gombe, Umar Ibrahim ne ya miƙawa zaɓaɓɓun mambobin Majalisar Jahar Gombe nasu takardun shaidar.

A jawabin daya gabatar a wajen bikin, Gwamna Inuwa Yahaya yace nasar sa, nasara ce ga ɗokacin al’ummar Jihar Gombe, yana mai tabbatarwa jama’ar jihar cewa “wannar shaidar dana karɓa a yau lasisi ce a gare mu, mu sake zage damtse don ƙara hidimtawa jama'a bisa aminci da yarar da s**a ba mu”.

Ga waɗanda s**a yi takara kuma s**a sha kaye a zaɓen, Gwamnan yace, "K**ar yadda yake a kowace fafatawar zaɓe, babu shakka za a samu wadda yayi nasara da wadda ya faɗi. Amma a gare ni babu wanda ya yi nasara kuma babu wanda ya sha kaye. Idan manufar dukkan jam'iyyun da ƴan takara shine tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe, ya zama wajibi kowa ya bamu goyon baya wajen ciyar da jihar mu gaba”.

Ya kuma nuna godiya ga al’ummar jihar bisa goyon bayan da s**a bashi da kuma gudanar da zaɓen cikin lumana daga farko har ƙarshen sa.

Zaɓaɓɓen Gwamnan ya bayyana cewa zaɓukan 2023 na daga cikin sahihan zaɓukan da aka yi a Najeriya tun bayan dawowar demokraɗiyya a shekarar 1999, ya kuma yabawa INEC da hukumomin tsaro da kuma duk waɗanda s**a taka rawa wajen ganin zaɓen ya gudana cikin nasara, gaskiya da adalci a Jihar Gombe.

Ya kuma yabawa INEC kan sabbin tsare-tsaren da tayi na tabbatar da zaɓe mai inganci. Sai dai ya bada shawarar cewa a nan gaba, ya kamata hukumar ta ɓullo da sabbin tsare-tsare ta yadda zaɓukan zasu ƙara inganci.

Da yake jawabi tun farko, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Gombe Umar Ibrahim, yace gabatar da takardar shaidar cin zaɓen ga waɗanda s**a yi nasara a zaɓen Gwamna dana ƴan majalisan jiha da aka kammala na ɗaya daga cikin manyan harkokin zaɓen na 2023, don haka ya buƙaci zaɓaɓɓen Gwamnan da sauran su, su ɗauki zaɓen nasu a matsayin amana da kwarin gwiwar da masu zaɓe s**a nuna musu, tare da ƙiran su biya su wannan bashin ta hanyar samar musu da ribar dimokuradiyya.

Don haka kwamishinan hukumar zaɓen na Gombe ya taya zaɓaɓɓen Gwamnan da mataimakin sa da dukkan zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin Jihar Gomben murnar nasarar da s**a samu a zaɓen.

Ya bayyana zaɓen a matsayin wani aikin dake buƙatar gudunmawar masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban don samun nasarar aiwatar da shi.

Sai ya godewa duk masu ruwa da tsaki a jihar bisa goyon bayan hukumar a tsawon lokacin data shafe na shirye-shiryen babban zaɓen na 2023.

Bikin wanda aka gudanar a Otal ɗin ƙasa da ƙasa na jiha, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, da jiga-jigan jam’iyyar APC, da sarakunan gargajiya, da malaman addini da dai sauran su.

Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when North East Daily Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Media/News Companies in Gombe

Show All