04/05/2024
DARASIN RAYUWA: CIN AMANA KO KAMUN ALLAH??
Rubutun yana da tsayi, amma a daure a karanta za'a amfana Insha Allah
Zan baku wannan labari na abinda ya faru da wani Babban mutum shahararre amma a boye mutumin banza ne fasiki, domin ya zama babban darasi ga kowa
Wani Babban Mutum ne wanda inda zan bayyana sunansa anan an sanshi saboda shahararsa, Mutumin ya sa wani yaron gidansa da ya dauka amintacce (amma ba dan cikinsa ba) akan yayi masa magana da wata shahararriyar 'yar fim zai yi fasikanci da ita, ita ma 'yar fim din da zan bayyana muku sunanta kowa ya santa
Yaron sai ya nemi hanyar samun magana da 'yar fim din, aka tura mata kudin jirgi tazo, aka k**a mata dakin hotel, sannan duk kwana daya da zatayi Mutumin yana biyanta Naira dubu dari biyar banda kudin abinci, sati guda tayi a hotel mutumin yana fasikanci da ita 'yar fim, kuma duk kudin da Mutumin ya kashe ta hannun yaron ne kudin ke zuwa gareta
To kafin zuwanta, yaron gidan mutumin da yake dan duniya ne, sai ya nemi camera na sirri wanda take nadar bidiyo da hotuna ya kafe a dakin hotel da ya k**awa 'yar fim, abin nufi, duk fasikancin da Maigidansa yayi da 'yar fim din wannan camera ta dauka
Bayan Mutumin ya gama fasikancinsa 'yar fim ta koma inda ta fito, sai yaron gidan mutumin ya kira wani abokinsa ya masa bayani cewa harka ta budu, zasu samu makudan kudi, don haka abokin shine zai jagoranci komai
Sai yaron Mutumin ya bawa abokinsa hotuna da bidiyo na Maigidansa da yayi fasikanci da 'yar fim, ya kuma bashi nambar wayoyinsu, inda abokin ya tura musu bidiyon yace idan ba su biya kudi adadi kaza ba zai watsa a duniya
In takaice muku labari haka yaron Maigidan tare da abokinsa s**a dinga tatsar makudan kudade na fitar hankali a gurin Maigidansa harda ita 'yar fim din basu kyaleta ba, Maigida da 'yar fim s**a rasa yadda zasuyi, sai daga bisani Maigidan ya kawo kara gurin wani babban jami'in 'yan sanda Officer
Shi kuma officer sai yayi endorsing case din ma wani kwararren jami'in dan sanda mai bincike, akayi ta gudanar da bincike cikin sirri daga karshe dai aka gano wanda s**a tsara abin aka k**asu, amma ba'a kai Kotu ba Maigidan ya nemi a kashe case din gaban 'yan sanda kar asirinsa da na 'yar fim ya tonu
Wannan labarin da nake baku ni shaida ne, kuma ganau ne ba jiyau ba, tsawon shekaru a wannan dandali ma Facebook nasha jan hankalin mutane akan suyi hankali da Artificial Karuwai, to kun ga yanzu ba karuwai ba har wanda ka dauka amininka ne zai iya hada baki a cuceka a harkan fasikanci, hatta su kansu Kawalai masu sana'ar nemawa Attajirai karuwai ana hada baki dasu a cuci Attajiri
Ina mai tabbatar muku akwai manyan mutane, k**a daga kan 'yan siyasa, manyan sarakuna harma da wasu manyan Malamai sun fada tarkon karuwai ana ta tatsarsu kudade masu dumbin yawa
Shekaru biyar da s**a wuce, a nan dandali na Facebook idan ban manta ba cikin Facebook account dina da ya lalace kafin wannan, nayi ta rubutu akan siffofin karuwai da rayuwarsu cikin sirri domin a gujesu
Batan basira ne ke sa mutum ya nemi karuwa, domin k**ar yadda nace duk abinda yake jikin karuwai akwaishi a jikin matarka na aure, kudin da zaka kashe wa karuwa ka bawa matarka ta gyara kanta mana, suma fa karuwai kudin da ake basune suke amfani dashi wajen gyara jikinsu, amma duk da haka ba za'a taba rasasu da cutuka ba
A karshen shekarar 2023 Gwamnatin Amurka ta ayyana wannan dabi'ah na masu nadar hoton tsiraici ko bidiyon mutane suna karban kudade daga garesu a matsayin Laifi, sun yiwa laifin lakani da "Sextortion", na karanta article din a website na 'yan sandan Amurka masu binciken manyan laifuka wato FBI
Na tabbata nan gaba itama Gwamnatin Kasarmu Nigeria zata amince da Sextortion a matsayin laifi babba, domin manyan mutane ke fadawa tarkon Sextortion, ko a yanzu duk wanda ya san ya fada tarkon karuwai ko cin amana mak**ancin wannan to ya min magana, zan sama masa mafita amma da sharadi masu tsauri
Wallahi duk wanda yake son ya zauna lafiya ya samu nutsuwar zuciya ta ya daure ya bi umarnin Allah tare da kiyaye aikata sabon Allah kowani iri
Ku ji da kyau, babu riba a harkan neman matan banza da kawalanci, karshenta kuma nadama ne marar amfani
Muna fatan Allah Ya tsaremu, Ya tsare mana imanin mu