GAYA Youths Focus

GAYA Youths Focus Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from GAYA Youths Focus, News & Media Website, 12, Gaya.

22/02/2023

Al'ummar karamar hukumar Gaya mu tsaya mu zabi cancanta kada mu duba Bangaranci ko YanGaranci! Allah yasa ayi lfy

13/12/2022

We are still active and vibrant for your information ℹ️

12/06/2022
03/11/2021
GAYA YOUTH FOCUS
03/11/2021

GAYA YOUTH FOCUS

ZIYARARMU ZUWA Senator Kabiru Gaya KARO NA BIYU!!!Kamar yadda aka gani a shafinmu Na baya sa’ilin ziyararmu zuwa wajen S...
01/11/2021

ZIYARARMU ZUWA Senator Kabiru Gaya KARO NA BIYU!!!

Kamar yadda aka gani a shafinmu Na baya sa’ilin ziyararmu zuwa wajen Senatorn yayi alkawarin abubuwa kamar haka:

1. Daukar nauyin yiwa matasa register Na N-power da kuma samar musu da aiki.

2. Samarwa matasa aiyukan yi a matakai daban-daban Na gwamnati.

3. Samar da gidauniyar koyar da sana’oin hannu domin dogaro dakai.

4. Sayawa dalibai yan asalin karamar hukumar Gaya forms Na Jamb tare da yi musu register Wanda kiyasin su yakai dalibai 1000

5. Magana akan gyaran ofis din kungiyar Gaya youth focus.

6. Samar da gidauniyar talkafawa marayu da uniform, textbooks, exercise books, pencils, Biros da dai sauransu domin daqile matsalolin yawon banza da shaye shaye acikin alummah.

A cikin wadannan kudurorin babu Wanda Maigirma senator y’a cika mana Wanda a saboda wannan dalilin ne yasa muka koma domin gabatar masa da kudurori guda biyu daga cikinsu, sune kamar haka:
1. Kammala mana aiki Flyover wadda ta Kai kusan shekaru kuma mutane suna ta korafi akan aikin.

2. Samar da gidauniyar taimakon marayu maisuna GAYA ORPHAN EDUCATION TRUST FUND (GO ETF) Wanda muka buqaci y’a sanya BOARD OF TRUSTEES (BOT) wadanda zasu rinqa bin diddigin yadda aka kashe taro da sisi Na kudin gidauniyar.

3. Samar mana da kujeru, tebura da kujeru a sabon ofishinmu dake a Gaya opposite central primary school.

4. Tallafawa kungiyarmu da mota saboda zirga zirgar Neman tallafawa garinmu domin dorewar cigaba.

Jimillar kudin da aiyukan biyu zasu ci bai wuce naira dubu dari shida da tamanin da Tara ba (689,000.00).

Senatorn yayi muradin sake yi mana alkawari kamar yadda yayi à baya Wanda mu kuma muka ce idan bazai aiwatar ba mukuma bamason alkawarin tunda alkawarin da yayi à baya ma yakai tsawon watanni 21 wato shekara daya da watanni 9 bai cika ba kuma yana kokarin yi mana wani alkawarin wanda anan take muka dire masa kudin motar daya bamu muka Kamo Hanya muka dawo GAYA.

SHAWARA
Jamaa yakamata mu gane masu kaunarmu kuma masu kaunar cigabanmu sannan duk Wanda zaizo wajenmu Neman Kuria mu zauna dasu su fada mana abinda zasui mana kafin mu zabesu Wanda idan basu cika ba muna da damar kalubalantarsu tunda Siyasa ake kuma zasu dawo.

Secretary
GYF
Comr. Mubarack Auwal Sa'ad

Assalam alaykum wa rahmatullah!A Madadin Daukacin matasan karamar hukumar Gaya Mai albarka, muna miqa saqon taaxiyya ga ...
23/09/2021

Assalam alaykum wa rahmatullah!
A Madadin Daukacin matasan karamar hukumar Gaya Mai albarka, muna miqa saqon taaxiyya ga masarautar Gaya tare da Gwamnatin jihar kano a bisa rasuwar m’ai martaba sarkin Gaya Late (Dr.) Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya (Kirmau m’ai Gabas)....
muna adduar Allah y’a jikansa yasa mutuwa ta zamo hutu a gareshi tare Da daukacin musulmin duniya baki daya.

GYF
23/09/2021

United we stand again and divided we fall!We parted our ways due to so many reasons and we joined again due to a single ...
22/09/2021

United we stand again and divided we fall!

We parted our ways due to so many reasons and we joined again due to a single reason.

We move!

MUTANE MASU DARAJA DA KISHIN AL’UMMAH SU AKE BAIWA DARAJA BA INUWAR GIGINYA BA!!!  Nura Kani Gaya  Said MadakiHaqiqa duk...
05/01/2021

MUTANE MASU DARAJA DA KISHIN AL’UMMAH SU AKE BAIWA DARAJA BA INUWAR GIGINYA BA!!!

Nura Kani Gaya
Said Madaki

Haqiqa dukkan masu karatu zasu yarda dani Idan har na sanar damu cewa mutanen nan guda biyu sun ciri tuta waje tallafawa alummah musamman matasa ta fuskoki marassa misaltuwa kamar irinsu :

1. Samar da aiyukan yi ga matasa
2. Wayar da kan matasa
3. Farfado da martabar garin Gaya da ma masarautarmu m’ai albarka gami da tunatar damu Akan abubuwa wadanda zasu amfanemu kuma su amfani garinmu baki daya.
Cikin ikon Allah sai aka samu dace aka zakulo wadannan mutane guda biyu a kayi musu sarauta Wanda Alhaji Saidu madaki ba boyayye bane domin kowa yasan Shi a garin Gaya wajen tallafawa matasa sai kuma Mallam Nura Kani Gaya wanda y’a zamo Malami kuma jagora a garin Gaya dama fadin kano baki daya.

Matasa yakamata mu nunawa wadannan bayin Allah karamci sannan mu nunawa azzalumai makiya garin Gaya cewa matasa kanmu y’a waye munsan kanmu an daina amfani da siyasa ana kawo mana rarrabuwar kai gami da gaba da juna a tsakaninmu.

Jamaa musamman matasan masarautar Gaya m’ai albarka muyi cincirindo mu fito mu marawa wadannan Yan kishin Gaya wajen nadin sarautarsu.

Alhaji Saïd madaki as SARKIN YAKIN GAYA
Mallam Nura Kani Gaya as DAN MASANIN GAYA

Rana: asabar
Wuri: Fadar m’ai Martaba Sarkin Gaya Alhaji (Dr.) Ibrahim Abdulkadir (KIRMAU MAI GABAS)

Allah y’a kara taimakon masarautarmu m’ai albarka y’a kuma cigaba da yi mana jagoranci albarkar annabin rahama annabi SAW.

Gaya youths focus
Secretary
Comrade Mubarack Auwal Sa'ad
05/01/2021

30/08/2020

Community development service

GAYA YOUTHS FOCUS SUN SAMU GANAWA DA Sen. Kabiru Ibrahim GayaSen. Kabiru Ibrahim Gaya Kabiru Ibrahim GayaA yau 25/06/202...
25/06/2020

GAYA YOUTHS FOCUS SUN SAMU GANAWA DA Sen. Kabiru Ibrahim GayaSen. Kabiru Ibrahim Gaya Kabiru Ibrahim Gaya

A yau 25/06/2020 ne jagororin wannan ƙungiya mai albarka s**a samu kaiwa wannan shahararren dan siyasa ziyara a gidansa dake WUSE zone 6 domin kai masa wasu batutuwa masu matukar muhimmanci. Batutuwan da muka tattauna sune kamar haka:

1. Daukar nauyin registration da kuma samawa matasanmu guda dubu daya aikin N-power daga mazabun Gaya guda Goma (10)
Ma'ana mutum dari (100) kowacce mazaba.

2. Samarda gidauniya ta marayun dalibai gamida marassa karfi akan harkar karatu da rashin lafiya. Misali, marayu da guragu gami da marassa karfi.

3. Samar da doka mai karfi akan matasa masu tarewa a gidajen yan siyasa suna hanawa ayi mana ayyuka saboda maula da rashin sanin kishin kai.

Wadannan kudire-kudire sune wadanda muka kai masa kuma ranar juma'a mai zuwa 26/06/2020 da yardar Allah za'a fara kudiri na farko.

Senator Kabiru Gaya mun gode da karramawa.

Muna roqon Allah ya karawa shugabannin hadin kai, son garinmu da kaunar al'umma.

Comrade Mubarack Auwal Sa'ad
Secretary
GAYA YOUTHS FOCUS
08154062675
for chairman

GAYA YOUTHS FOCUS BA KUNGIYAR JAGALIYAR SIYASA BACE!!!GAYA Youths Focus Bata Siyasa bace saboda haka duk wani dan jagali...
18/06/2020

GAYA YOUTHS FOCUS BA KUNGIYAR JAGALIYAR SIYASA BACE!!!

GAYA Youths Focus Bata Siyasa bace saboda haka duk wani dan jagaliyar siyasa Bama amanna dashi saboda kare mutunci da martabar kungiyar. Babu wani dalili da zai sanya wani mutum guda ya rinqa shiga gidan radiyo, kafar yada zumunta yana koda iyayen gidansa na siyasa da sunan kungiyar matasa. Wacce kungiyar? Badai Gaya Youths Focus ba domin dukkanin yayan wannan ƙungiya suna da sana'o'in su na rufin asiri babu mutuwar zuciya.

Fatanmu shine Allah ya daukaka garinmu ya kara mana cigaba ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya ameen ya Rabbal Alameen 🙏

Signed:
Secretary GYF
Comrade Mubarack Auwal Sa'ad

Akwai zargin danne haqqi a tare da Shugaban kansilolin karamar hukumar GAYA da jama'ar  garin KALAHADI😥 ku biyo mu akwai...
01/06/2020

Akwai zargin danne haqqi a tare da Shugaban kansilolin karamar hukumar GAYA da jama'ar garin KALAHADI😥 ku biyo mu akwai batu agaba....

Assalamu alaikum wa rahmatullah! Amadadin Kungiyar GAYA YOUTHS FOCUS da shugabannin ta muke miqa saqon taaziyyar mu zuwa...
28/05/2020

Assalamu alaikum wa rahmatullah!

Amadadin Kungiyar GAYA YOUTHS FOCUS da shugabannin ta muke miqa saqon taaziyyar mu zuwa ga Senator Kabiru Gaya abisa ga rashi da akai masa na matarsa Hajiya Haleemah Gaya.

Muna roqon Allah ya gafarta mata tare da sauran musulmai baki daya.

28/05/2020

Comr. Mubarack Auwal Sa'ad
Secretary
GYF
For chairman

BANKI A GARIN GAYA!!!A ranar Alhamis ne 28/05/2020 kungiyar matasa mai rajin kawo sauyi a karamar hukumar GAYA s**a samu...
28/05/2020

BANKI A GARIN GAYA!!!

A ranar Alhamis ne 28/05/2020 kungiyar matasa mai rajin kawo sauyi a karamar hukumar GAYA s**a samu damar kai ziyara gami da tuni a wajen sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji akan batun maganar BANKI da kuma matsayar da aka samu kasancewar har yanzu munji shiru kamar Mallam yaci Shirwa. Maigirma sakataren gwamnatin yayi jawabi kamar haka

"Da farko haqiqa naji dadi da kuka zama jajirtattun matasa kasancewar wannan shine zuwanku na biyu akan maganar BANKI a GAYA. Haqiqa naji dadin wannan tuni da kuka yi agareni , sannan ku sani cewa maganar BANKI a cikin garin Gaya abin ya samu cigaba ma domin banda maganar Bankin JA'IZ BANK ayanzu haka nayi magana da shugaban babban bankin Nigeria wato CBN kwanaki uku da s**a gabata domin shine yake da alhakin sanya commercial banks suje su gina mana banki a garinmu kuma ya tabbatar min da cewa Insha ALLAH zaiyi duk abinda ya dace kuma da izinin Allah mun kusa wuce wannan MATSALAR"
Maigirma sakataren gwamnatin ya dora da cewa " haqiqa Gaya Allah ya bamu kowacce irin dama domin ba kowanne LG ne a Nigeria Allah zai basu Senator, Dan majalissar Tarayya, Dan majalisar jiha gamida Chairman a lokaci guda ba, abinda kawai ya dace da al'ummar Gaya shine mu cigaba da addu'ar dacewa gami da roqon Allah ya tabbatar mana da wannan cigaba"

Akarshe Maigirma SSG yace mu tsammaci cewa akowane lokaci za'a zo akawo banki bawai lallai sai JA'IZ BANK ba.

Muna roqon Allah ya tabbatar da wannan al'amari. Jama'a don Allah mu kasance masu fatan alkhairi.

Comr. Mubarack Auwal Sa'ad
Secretary
GYF
For chairman

GANAWA TA MUSAMMAN TARE DA MAIGIRMA TSOHON DAN MAJALISAR JIHAR KANO MAI WAKILTAR KARAMAR HUKUMAR GAYA!!!28/05/2020A koka...
28/05/2020

GANAWA TA MUSAMMAN TARE DA MAIGIRMA TSOHON DAN MAJALISAR JIHAR KANO MAI WAKILTAR KARAMAR HUKUMAR GAYA!!!

28/05/2020

A kokarin wannan ƙungiya mai albarka na shawo kan wasu daga cikin matsalolin dake addabar wannan gari namu mai albarka, GAYA YOUTHS FOCUS ta samu ganawa da Hon. Suwidi Mahmoud Kademi, tsohon dan majalisar jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar GAYA inda muka tattauna batutuwa masu matukar muhimmanci gami da faida akan yadda zamu tallafi matsalar tsarin shugabanci, matsalar matasa gami da bunkasa harkar kasuwanci da ilimi ta fannoni da dama akaramar hukumar GAYA.

Muna roqon Allah ya cigaba da dafa mana ba domin iyawarmu ba. Allah ya kawo mana cigaba mai ɗorewa gami da shugabanni masu kishinmu ameen summa ameen.

COMR. Mubarack Auwal Sa'ad
Secretary:
Gaya Youths Focus
For chairman

12/05/2020

Ga zahiri

DAYA DAGA CIKIN RIJIYOYIN KANKAREN DA MUKE AIKIN HAQAWA TA KAMMALA!Alhamdulillah!A kokarin wannan ƙungiya mai albarka na...
12/05/2020

DAYA DAGA CIKIN RIJIYOYIN KANKAREN DA MUKE AIKIN HAQAWA TA KAMMALA!

Alhamdulillah!
A kokarin wannan ƙungiya mai albarka na warware kadan daga cikin matsalolin da s**a addabi Gaya akan rashin wadataccen ruwan sha, ya sanya muka assasa wannan aiki mai albarka wanda cikin ikon Allah yau 12/05/2020 muka samu nasara mai girma.

Kofa a bude take ga duk wani mai son tallafawa wannan gari namu da wannan sadaqatul jariya zai iya tuntubar mu ta wannan lambar waya 08154062675.
Allah ya bada ikon tallafawa ameen thumma ameen.
Kada amanta
+2348154062675
Secretary,
Gaya Youths Focus
Mubarack Auwal Sa'ad

GIDAN RUWAN WUDIL!WUDIL REGIONAL WATER SUPPLY (WRWS)Ayayin ziyarar da muka kaiwa wannan gidan ruwa domin magance matsalo...
09/05/2020

GIDAN RUWAN WUDIL!

WUDIL REGIONAL WATER SUPPLY (WRWS)

Ayayin ziyarar da muka kaiwa wannan gidan ruwa domin magance matsalolin dake addabar garin Gaya na Ruwa. Abisa haka muka samu ganawa da manyan ma'aikatan wannan gidan ruwa kuma sunyi mana bayanin matsalar daki-daki inda akarshe mukai musu alkawarin cewa da izinin Allah zamui iya bakin kokarin mu domin ganin an kawo karshen matsalolin ruwan a garin Gaya.

Muna roqon Allah ya dafa mana yasa mufi ƙarfin duk wani abu daya shige mana gaba.
Kada ku manta, addu'ar ku itace karfinmu.

Signed:
Secretary GYF
Comr. Mubarack Auwal Sa'ad

Yayin ganawa Da daya daga cikin matasa yan kishin Gaya Alhaji Muhammad Gaya, Accountant a Sa'adatu Rimi College of educa...
08/05/2020

Yayin ganawa Da daya daga cikin matasa yan kishin Gaya Alhaji Muhammad Gaya, Accountant a Sa'adatu Rimi College of education, Kano.
Allah ya Kara girma ranka shi dade.

Signed:
Secretary,
Comr. Mubarack Auwal Sa'ad
07/05/2020

PRIMARY HEALTH CARE HOSPITAL BALAN.Ayaune wannnan asibitin ya samu karuwa bisa ziyarar da shugabannin wannan ƙungiya ta ...
08/05/2020

PRIMARY HEALTH CARE HOSPITAL BALAN.

Ayaune wannnan asibitin ya samu karuwa bisa ziyarar da shugabannin wannan ƙungiya ta Gaya Youths Focus s**a kai masa sakamakon matsalar rashin ruwa data addabi wannan asibiti da kuma al'ummar wannan Gari na Balan.

Bazamu gaza ba har sai munga mun fito da garinmu a idanun duniya.
Allah shine madogararmu kuma gareshi muka dogara saboda haka Bama tsoron duk wani mahaluki walau Dan siyasa, jami'in gwamnati ko wanene mai shirin kalubalantar lamuranmu tunda munsan dalilin gwagwarmayar mu.

Jama'a kune karfin guiwarmu kuma da karfinku ne kaɗai zamu iya samun nasarar da zamui mamakinta anan gaba kadan.
Allah ya dafa mana.

Signed:
Secretary,
Comr. Mubarack Auwal Sa'ad
08/05/2020

MATSALAR RUWAN SHA A GARIN GAYA!05/05/2020A kokarin wannan ƙungiya mai albarka na samar da cigaban matasan garin Gaya ay...
05/05/2020

MATSALAR RUWAN SHA A GARIN GAYA!

05/05/2020

A kokarin wannan ƙungiya mai albarka na samar da cigaban matasan garin Gaya ayau talata 05/05/2020 mukai kokari wajen samarda ginin sabbin rijiyoyin Kankare a garin na Gaya domin rage radadin rashin ruwan da yake damun garinmu na Gaya.
Za'a fara gabatar da aikin wannan rijiya ta farko ne a bayan Gaya Gandu wanda Maigirma Dawakin Gaya Alhaji Abubakar Abdulkadir ya bayarda fili kyauta domin samarda wannan rijiya sadaqatul jariya.

Muna fatan wannan rijiyoyi su zamo alkhairi ga al'ummar mu na Gaya da kewaye.
Ya Allah muna roqonka da tsarkakan sunayen ka 99 ka kawo mana dauki sannan ka bamu cigaba mai ɗorewa ameen ya rabbal Alameen.

Jama'a mu cigaba da addu'a a wannan wata mai albarka domin ya kawo mana dauki a wannan hali da muke ciki.

Secretary,
Gaya Youths Focus
05/05/2020

GASKIYAR MAGANA AKAN MAGANAR BANKI A GAYA!Assalam alaykum al'ummar garinmu na Gaya mai albarka, amadadin wannan ƙungiya ...
22/03/2020

GASKIYAR MAGANA AKAN MAGANAR BANKI A GAYA!

Assalam alaykum al'ummar garinmu na Gaya mai albarka, amadadin wannan ƙungiya mai albarka, muna miqa saqon godiyar mu gami da ban gajiya ga Maigirma sakataren gwamnatin jihar Kano ALHAJI Usman Alhaji abisa karramawar da yayi ga wannan kungiya ta hanyar tarbar da yayi mana Cikin mutuntawa.
Ayau Lahadi 22/03/2020 ne Shugabannin wannan kungiya ta GAYA YOUTHS FOCUS ta samu damar kaiwa sakataren Gwamnatin jihar Kanon ziyara akan maganar Bankin da Gwamnatin jihar Kano ta yiwa garin Gaya alkawari inda muka tattauna batutuwa masu matukar muhimmanci.
Maigirma sakataren gwamnatin ya tabbatar da cewa haqiqa an samu wasu matsaloli kananu amma ya gode bisa tunasar dashi da mukai sakamakon aiyuka da s**ai masa yawa amma ya tabbatar mana da cewa nan bada dadewa ba za'a ga an fara wannan aikin da izinin Allah mai kowa mai komai.
Idan mai karatu bai manta ba, Alhaji Usman Alhaji dama shine mutumin daya nemo mana wannan banki awajen director na Central bank of Nigeria ganin irin halin da muke ciki amma wasu tsirarun mutane s**a hana filin da za'a gina wannan banki.
Muna roqon Allah (SWT) ya kara kawo mana cigaba garinmu na Gaya ta kowanne fanni kuma ta hannun kowaye walau dan siyasa, mai kudi, dan kasuwa ko dan Boko.

Putting Gaya first.

GAYA YOUTHS FOCUS ( GYF).A Daren yau ne 23/2/2020 wannan Kungiya Mai Suna Ta Samu Zama Da  Shugaban Karamar hukumar Gaya...
23/02/2020

GAYA YOUTHS FOCUS
( GYF).

A Daren yau ne 23/2/2020 wannan Kungiya Mai Suna Ta Samu Zama Da Shugaban Karamar hukumar Gaya Wato Hon. Ahmad Abdullahi Tahi Gaya .

Domin Gabatar da Wannan kungiya Da Kuma Bayyana Kyawawan Manufofin ta Domin neman Sahalewar Sa a Matsayin sa na Shugaban Kuma Jagora ga Garin Gaya Mai Albarka.

Kuma Alhamdullah An Samu Babbar Nasara Da Goyon Bayan sa .

Muna Godiya kwarai da Gaske da Kuma Addu'ar Samun kariya Da Kuma dorewa Mai Albarka Da Kishin Al'ummar Gaya.

Written ✍✍✍By Gaya youths focus Sec.

GAYA YOUTHS FOCUS (GYF).____________________________A Yaune Asabar 23/2/2020 , 3: 00 pm Wannan kungiya Mai Suna a Sama T...
23/02/2020

GAYA YOUTHS FOCUS (GYF).
____________________________

A Yaune Asabar 23/2/2020 , 3: 00 pm Wannan kungiya Mai Suna a Sama Ta Samu Zama Da hukumar Hisba Ta Gaya wato Hisbah Commandant Gaya Division Domin Gabatar da Wannan kungiya Da Kuma Bayyana Mata kyawawan Manufofin ta.

Kuma Alhamdullah Ta Samu Gagarumar Nasara Da Kuma Goyan Baya Da Shawarwarin Da S**a Dace na yadda Zamuyi mu Taimaki Gina Wannan kungiya Domin Taimakon Al'ummar Garin Gaya Gaba Daya.

Don Haka Jama'a muna Neman Addu'ar Ku Da kuma Da Goyon Bayan ku Allah ya yi Mana Jagora Amin.

Written by Sec. Gaya youths focus (Gyf).

GAYA YOUTHS FOCUS (GYF).____________________________A Yaune Asabar 23/2/2020 , 2:00 pm Wannan kungiya Mai Suna a Sama Ta...
23/02/2020

GAYA YOUTHS FOCUS (GYF).
____________________________

A Yaune Asabar 23/2/2020 , 2:00 pm Wannan kungiya Mai Suna a Sama Ta Samu Zama Da hukumar tsaro Ta Gaya wato Nigerian Police Force Gaya Division Domin Gabatar da Wannan kungiya Da Kuma Bayyana Mata kyawawan Manufofin ta.

Kuma Alhamdullah Ta Samu Gagarumar Nasara Da Kuma Goyan Baya Da Shawarwarin Da S**a Dace na yadda Zamuyi mu Taimaki Gina Wannan kungiya Domin Taimakon Al'ummar Garin Gaya Gaba Daya.

Don Haka Jama'a muna Neman Addu'ar Ku Da kuma Da Goyon Bayan ku Allah ya yi Mana Jagora Amin.

Written by
Sec. Gaya youths focus (GYF).

A madadin daukacin mahukunta na wannan ƙungiya mai albarka muna miqa saqon Barka da juma'a ga daukacin al'ummar masaraut...
21/02/2020

A madadin daukacin mahukunta na wannan ƙungiya mai albarka muna miqa saqon Barka da juma'a ga daukacin al'ummar masarautar GAYA mai albarka.
Alkhairan dake cikin wannan rana Allah ya tabbatar mana sannan ya kare mu daga dukkanin sharri gami da yi mana jagora a al'amuran mu na rayuwa.

GAYA YOUTHS FOCUS

Address

12
Gaya

Telephone

+2349041816845

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GAYA Youths Focus posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to GAYA Youths Focus:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Gaya

Show All

You may also like