24/06/2024
Wata Rana MANZON ALLAH (S.A.W) YA CE: IDAN AL'UMMATA SU KA AIKATA ABUBUWA GUDA GOMA SHA BIYAR (15), TO A SAURARI ZUWAN BALA'I
1. Idan dukiyar Baitil-Mali ta kasance Ganima ga wasu mutane.
A saurari zuwan Bala'i
2. Idan Amana ta kasance abin-cinyewa, wato aka wofintar da ita, ba'a bayar da ita kamar yadda shari'a ta umurta.
A saurari zuwan Bala'i.
3. Idan ma su dukiya su ka dauki Zakka kamar wani Haraji ne aka dora akansu.
A saurari zuwan Bala'i.
4. Idan aka wayi gari Mutum ya na girmama abokinsa, ya na wulakanta Mahaifinsa.
A saurari zuwan Bala'i.
5. Idan Mutum ya na girmama Matarsa, ya na wulakanta Mahaifiyarsa.
A saurari zuwan Bala'i.
6. Idan aka koma ana koyon Karatun
Al - Qurani ba don Allah ba, sai don saboda Duniya.
A saurari zuwan Bala'i.
7. Idan ya kasance ana girmama Mutum saboda sharrinsa.
A saurari zuwan Bala'i.
8. Idan ya kasance ana shan Giya iri Daban-Daban.
A saurari zuwan Bala'i.
9. Idan ya kasance ana ado da Alharini bayan Shari'a ta hana.
A saurari zuwan Bala'i.
10. Idan ya kasance ana Cudanya tsakanin Maza da Mata ana Rawa.
A saurari zuwan Bala'i.
11. Idan ya kasance an bullo da sabbin kayan Kade-Kade da Goge-Goge.
A saurari zuwan Bala'i.
12. Idan ka ji ana daga sauti ana hayaniya a Masallatai.
A saurari zuwan Bala'i.
13. Idan aka samu Al'ummar karshen zamani su na zagin wadanda s**a gabacesu.
A saurari zuwan Bala'i.
14. Idan Zinace Zinace su ka yawaita.
A saurari zuwan Bala'i.
15. Idan mutane s**a halatta cin Riba.
A saurari zuwan Bala'i.
Wannan duk halayenmu ne yanzu
Kafin Mu Zagi Shugabanni Mu Fara Gyara Kawunanmu Dan Allah
Allah ka Karemu Ka Tsare Mana Imanin Mu