04/08/2023
ABIN DA YAKAMATA KU SANI GAME DA ALAƘAR NIGERIA DA NIGER.
Nigeria da Niger, Abokai ne, kuma makusanta, akwai alaƙa ta kusa a tsakanin waɗannan ƙasashe biyu, sau da yawa ma, idan ku ka kalla cikin ɗabi'un su sunyi kusan ɗaƴa, wasu 'ƴan yankin da ke tsakanin bodojin Nigeria da Niger su kan fi zaɓar alaƙa da Niger sama da Nigeria, cikin Niger suke shiga domin gudanar da ayyukan su na yau da kullum, ko kuwa domin kasuwanci, su kan shiga su gama ayyukan su, ko kasuwancin su, da yammaci ko dare su koma gidajen su wajen iyalan su.
Haka zalika suma mutanen yankin bodojin Niger da Nigeria s**an aiwatar da irin hakan, ba don komai ba, sai don sabawa da akayi da juna.
Akwai auratayya da ta shiga tsakanin mutanen waɗan nan ƙasashe guda biyu.
Mafi akasarin mutanen yankin addini iri ɗaya suke yi, hakan yasa suke alaƙa da junan su.
Mutanen yankin kudancin Nigeria ba mu da wata alaƙa dasu ta kusa, sai dai ta nesa, tunda mun kasance ƙasar mu guda da su, ɗabi'un mu ba ɗaya bane da su, sannan akasarin su ma ba addini iri ɗaya muke dasu ba, River Niger ya raba mu (su turawa sun san wannan).
'Ƴan Niger kuwa sune 'ƴan uwanmu, babu wani ruwa ko sahara ko wani abu da ya raba mu, an same mu kusan iri ɗaya, kuma ɗabi'un mu da addinin mu, da cigabanmu, shiyasa turawa s**a raba mu domin haɗewarmu zai basu matsala. Kuma sunyi nasara tunda a yanzu ɗan Nigeria yafi ganin ɗan Kudu a matsayin ɗan uwansa akan ɗan Niger.
Yanzu magana ma ake ta yaƙi tsakanin Nigeria da Niger, tunda dai Nigeria ita take da shugaba a ƙungiyar (ECOWAS), Wai don lalacewa irin ta wasu mutanen mu, har sun ma fara zagin junansu a tiktok takan batun. Wanda wannan abin takaici ne a gare mu.
To ku sa ni, yaƙin da turawan mulkin mallaka suke so su haddasa a tsakan-kanin ƙasashen yammacin Africa, babu abinda zai haifar sai dai maida ƙasashen baya, da taɓarɓarewar abubuwa, musamman a waɗan nan yan ku nan da abin zaifi ƙamari.
Misali: Abin Allah shi kiyaye, idan yaƙi ya ɓarke tsakanin Nigeria da Niger,
Tabbas za'a illat.