Aliyu Said Gamawa

Aliyu Said Gamawa Aliyu said Gamawa

10/09/2025

Ɗan'uwa kasani mutuwa bazata jira har sai kazama mutumin kirki ba.

Ka zama mutumin kirki, kayi ta addu'a sai ka jira mutuwa.

23/05/2025

Madina

08/05/2025

🍃

"...... ku sabar ma ƴaƴanku aikata alkhairi domin shi aikin alkhairi yana dawowa".

-Ibn Abbas

07/05/2025

MATASHIYA:
Kada ka yi tarayya da mutane 4:

1. Wadanda idan suna tsararka, sai su rika yin gasa da kai, da kushe ka

2. Idan ka fi su, sai su rika yi maka hassada da cin kafa da aibata ka

3. Idan sun fi ka, sai su rika raina ka, suna yi maka wulakaci da nuna maka matsayin ka

4. Wadanda basa taimako sai in suna bukatarka, in sun gama da kai suyi gori

Irin wadannan mutane kada ka saki jiki da su, babu alheri a mu'amala da su

28/04/2025

MUTUM UKU BA SA NADAMA A RAYUWA !!!

1. Wanda Yake jin Tsoron Allah
2. Wanda Yake Kiyaye Lokaci
3. Wanda Yake Yarda da Kaddara

21/04/2025

Kukan Kurciya......(2)

Daga cikin abin da Imam Alkadi Iyad - Allah ya yi masa rahama - ya lissafa cikin zagi da batanci ga Annabi S.A.W akwai; Mutum ya ambaci zagi ko batanci ga Annabi (S.A.W) ya ce, wai wani ne ya fadi hakan, kuma a duba ba a ga wannan magana ba, to shi ne ya yi wannan zagin, don haka, hukuncinsa, hukuncin wanda ya zagi Annabi ne. Ga abin da yake cewa a cikin "Ash-shifa (2/246). Ya ce:

وإن اتهم هذا الحاكي فيما حكاه أنه اختلقه ونسبه إلى غيره، أو كانت تلك عادة له، أو ظهر استحسانه لذلك، أو كان مولعا بمثله والاستخفاف له، أو التحفظ لمثله وطلبه، ورواية أشعار هجوه صلى الله عليه وسلم وسبه، فحكم هذا حكم الساب نفسه، يؤاخذ بقوله ولا تنفعه نسبته إلى غيره، فليبادر بقتله، ويعجل إلى الهاوية أمه.

Ma'ana: "Idan aka tuhumci wannan mai kawo labarin (zagi ga Annabi) cikin labarin da ya kawo cewa, shi ne ya kirkiri wannan labari ya dangana shi ga waninsa, ko kuma dama hakan al'adarsa ce, ko kuma ya nuna kyan abin, ko kuma dama yana yawan kawo irin hakan, da daukarsa ba komai ba, ko kiyayewa daga irin wannan abin, da neman wakokin da a yi wa Annabi Zambo da zagi, to hukuncin mai yin haka, shi ne hukuncin mai zagin Annabi, za a k**a shi da wannan zance, kuma cewa wani ne ya fada ba zai amfane shi ba. Kawai a gaggauta kashe shi, a gaggauta kai shi uwarsa wutar Hawiya".

Wannan shi ne abin da Alkali Iyad ya fada, don haka duk wanda zai ce auren Manzon Allah (S.A.W) da Nana Safiyya F......, ya dangana hakan ga Imamu Muslim, har ya ba da lambar hadisi, kuma a ce ya bude ya karanto wurin, ko ya nuna wurin, amma ya kasa, saboda babu hakan a ciki, karya kawai yake, to ko shakka babu shi ne ya yi wannan batanci ko zagin.

Hakanan wanda zai ce sahabbai mata suna zuwa wajen Annabi (S.A.W) su nuna suna bukatarsa, irin bukatar....!. Ya ce hakan yana Sahihul Bukhari, a ce, nuna wurin ya kasa, don babu a ciki. Shi ma ba shakka shi ya yi wannan batancin ko zagin!.

Don haka, babu sharri ko kage a maganar nan, sai dai a wurin wanda yake da son zuciya, ko ya jahilci lamarin.

Allah ka kara mana so da imani da biyayya ga Annabi (S.A.W), ka tabbatar da dugaduganmu a kan sunnarsa. Ameen

Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo

20/04/2025

HALAYE DA ALLAH DA MANZON SA SUKE SO

Anas Ɗan Malik yace,
Manzon Allah (SAW) yace:
"Bin abu sannu sannu daga Allah ne, (wato wani abu ne da Allah yake so) Amma garaje da gaggawa wannan daga shaiɗan ne

Mu sani ba wanda ya fi karɓan Uzuri k**ar Allah, haka kada mu manta ba wani abinda Allah ya fi so k**ar yabo da godiya da kirari gareshi.

Imam Muslim ya fitar da hadisi daga Abdullahi Ɗan Abbas Annabi (SAW) yana gaya ma AbdulQais, cewa; "Kana da wasu halaye guda biyu da Allah da Manzon sa suke son su; HAKURI/JURIYA, DA BIN ABU SANNU SANNU."

Amma game da aikin alheri don lahira a guje ake yin su, ana so bawa ya riƙa himmar riga kowa aikin lada, wato kada ka zauna ana barin ka a baya..!

Cikar hankali da nagarta shine bin al'amuran duniya a sannu sannu a hankali. gaggawa da garaje aikin shaiɗan ne

Allah ya bamu dacewa duniya da lahira, amin

06/04/2025

Zaman takewar aure......

Address

Garko Street
Gamawa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aliyu Said Gamawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share