
18/02/2025
Azzaluman Yan Kasuwa Sun Boye Kaya Da niyyar Suyi Tsada,
Yanzu kuma sai Karye Suke,
Allah Ubangiji Yakara Saukar Da Sauki Ga Talakan Najeriya.
WASU 'YAN KASUWA DOLE NE SU SHIGA WUTAR JAHANNAMA!!!π
Talakkawa su yi noma lokacin girbi su sayar maka da buhun gero akan kudi 30k, kai kuma ka ajiye shi sai irin wannan lokaci ya yi ka fitar da shi ka sayar misu akan kudi 96k. Babban abin takaici da ban haushi shine; yadda ka sayi wannan buhu a hannun talakka akan Mudu 40, idan ka tashi sayar masa baza ka sayar masa da shi yadda ka saye shi da Mudu 40 ba har sai ka sayo wani sabon buhu mai daukar Mudu 37, ma'ana ka cire Mudu 3 daga cikin kowane buhu. A haka har ka samu karin wasu buhuna na daban daga cikin wadanda ka rage.
Wannan wace irin hadama ce?... Ka samu ribar 56k amman duk bata ishe ka ba har sai ka cire Mudu 3 daga kowane buhu ka sake samun karin wasu buhuna duk ka hada ka sayar domin ka yi arziki.
Na rantse da Allah wannan shine abin da 'yan kasuwa ke yi a halin yanzu.
Allah ya sa mu yi kyakykyawan karshe ππ
Ibrahim Rabi'u π