03/01/2025
Shin Kana Mamakin Yadda Nasara Ke Gudunka duk kuwa da tarin ƙoƙarinka? Saurari batu:👂👂
Wani lokaci dalilin da yasa ba ka yin nasara shine saboda ka bayyana wa duniya abin da kake son zama da abin da kake yi don kaiwa ga hakan.
Wannan kuskure ne. Dole ne ka fahimci cewa duk da cewa nasara abu ne na fili, hakan ba yana nufin cewa aiki tukuru da dabaru ma dole ne su kasance na fili ba.
Mummunan abu mafi girma da zaka iya yi shine ka sanar da jama'a cewa ka fara sabon tafiya don zama mafi kyawun kanka. Wannan kamar ba wa makiyanka bindiga da taswira ne don su san inda za su harbe ka.
Don samun nasara, dole ne ka koya ka yi shiru ka kuma ɓoye daga idanun jama'a. Kaɗan ne suke son ganin ka yi nasara; yawanci ba su son sunanka ya yi kamshin nasara.
Idan aka bar tsarin a asirce, mutane ba za su san inda za su kai maka hari ba. Za su ɗauka cewa har yanzu kai wawane, madalla! Ci gaba da yin kamar wawa har sai nasararka ta rufe bakin kowa.
Nasara abu ne na fili; tsarin kuma abu ne na sirri. Ka ci gaba da kasancewa mai wayo."
©Yusuf✍🏻