18/04/2024
KARATU KYAUTA A KASAR JAPAN A KARKASHIN MEXT JAPAN SCHOLARSHIP
Hukumar Ilimi bai daya ta kasar Japan wato Japan Ministry of Education ta sanar da shirin bayar da ilimi kyauta ga daukacin dalibai na ko’ina a fadin duniya. Wannan Scholarship ne wanda zai daukewa dalibi komai da komai na karatu. Wannan tsarin karatu kyauta za’a rufe a ranar 15th May, 2024.Akwai Undergraduate, MSc da PhD.
Ga abubuwan da wannan scholarship ya qunsa:-
1. Karatu kyautane
2. Wajen kwana (Accomodation kyauta)
3. Abinci kyauta
4. Visa da Ticket din jirgi zuwa Japan kyauta
5. Tallafin kudin kashewa N900,000 duk wata.
6. Kula da lafiya kyauta.
GA DOCUMENTS DIN DA AKE BUKATA DOMIN SAMUN WANNAN SCHOLARSHIP:
1. Transcript
2. Certificate
3. Recommendation Letter
4. Medical Certificate
5. Application Form
6. Birth Certificate
7. Eligibility Letter ( A ministry of education zaka je ka karbo).
YADDA ZA’A CIKE WANNAN SCHOLARSHIP:
Masu ra’ayin samun wannan scholarship zasu kai photocopy din takardun su zuwa Japan Embassy dake Abuja. Dalibai su sani cewar kafin s**ai takardun su zuwa Japan Embassy dole sai sunje Ministry of Education sunyi verification din takardun su daga nan su nemi abasu eligibility letter, idan sun gama zasu je Ministry of Foreign Affairs domin a sanya masa hannu. Idan ya gama da saiya kai takardun nasa zuwa Japan Embassy.
DOKOKIN WANNAN SCHOLARSHIP:
1. Dole ne Dalibin da zai nemi MSc ko PhD kar ya wuce shekaru 34 (Ma’ana daga 1990 zuwa sama)
2. Dole ne Dalibin da zai nemi Undergraduate kar ya wuce shekaru 20 ( Ma’ana daga 2000 zuwa sama).
3. Dole sai kaje ministry of education da ministry of foreign affairs domin erification din documents dinka
4. Dole sai Ministry of education sun baka “Eligibility Letter”
• GA JERIN COURSES DIN DA SUKE AVAILABLE
• SOCIAL SCIENCES AND HUMANITIES – A
• Law, Politics, Pedagogy, Sociology, Literature, History, Japanese Language, Economics, Business Administration., Accounting, Financial economics, etc.
• NATURAL SCIENCES – A
• Science (Mathematics, Physics, Chemistry)
• Electric and Electronic Studies (Electronics, Electrical Engineering, Information Engineering)
• Mechanical Studies (Mechanical Engineering, Naval Architecture)
• Civil Engineering and Architecture (Civil Engineering, Architecture, Environmental Engineering)
• Chemical Studies, Applied Chemistry, Chemical Engineering, Industrial Chemistry, Textile Engineering)
• NATURAL SCIENCES – B
• Agricultural Studies (Agriculture, Agricultural Chemistry, Agricultural Engineering,, Animal Science, Veterinary Medicine, Forestry, Food Science, Fisheries)
• Hygienic Studies (Pharmacy, Hygienics, Nursing), Science (Biology)
• Natural Sciences – C
• Medicine, Dentistry
• Japan Embassy dake Abuja, Nigeria: https://www.ng.emb-japan.go.jp/itprtop_en/index.html
• Domin dauko Application form, Medical Certificate Form, Recommendation Letter format na masu Undergraduate ku shiga nan: https://www.studyinjapan.go.jp/en/smap-stopj-applications-undergraduate.html
• Domin dauko Application form, Medical Certificate Form, Recommendation Letter format na masu MSc da PhD ku shiga nan: https://www.studyinjapan.go.jp/en/smap-stopj-applications-research.html
• Domin karanta cikakken bayanin wannan scholarship a harshen turanci ka shiga nan: https://opportunitiescorners.com/mext-undergraduate-scholarship-2025/
Daliban da suke so ayi musu processing din wannan scholarship, musamman wadanda s**ayi nisa da Abuja zasu iya tuntubar mu domin samun wannan scholarship din, a tuntube mu akan Whatsapp Number din mu k**ar haka: 0806 965 4613
The Applications are open to apply for the MEXT Undergraduate Scholarship 2025 (Embassy Recommendation). Fully Funded Scholarship in Japan.