02/09/2019
Kotun kolin Najeriya ta kori karar da Kalu Kalu Agu ya shigar tare da wasu mutane biyu kan takardar kammala karatun Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.
Kotun ta kori karar ne bayan lauyan da ke kare Kalu ya janye bisa dalilai na rashin shigar da karar a cikin lokacin da doka ta tanada.
APC ta fadi zaben jihar Zamfara - Kotun koli
An kai karar ministan tsaro kotun koli
A baya dai kotun daukaka kara a Abuja ta yi watsi da karar, wacce aka shigar bisa zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da takardun kammala makaranta na bogi ga Hukumar Zabe ta Kasa, INEC a matsayinsa na dan takara a zaben 2019.
Haka kuma kotun ta ce bai dace shugaban kasa ya yi amfani da lauyan gwamnatin don kare shi a karar da ta shafe shi ta kashin kansa ba.
Hakan a cewar kotun ya sabawa dokar da'ar ma'aikata.
Sauran mutanen da aka yi karar sun hada da jam'iyyar APC da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC.
Dalilin korar karar shi ne, an shigar da ita bayan kwana 14 da kudin tsarin mulki ya tanada.
Sai dai kuma jam'iyyar hamayya ta PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar su ma suna kalubalantar Shugaba Buharin a kotun sauraron kararrakin zabe kan batun takardar shaidar kammmala karatun nasa.