18/02/2024
Gwamnatin ƙaramar hukumar Miga tana daf da kammala aikin hanyar kwalta na kimanin Naira Miliyan ɗari uku mai tsawon kilomita uku, wadda ya tashi daga Zango zuwa Zareku.
Shugaban ƙaramar hukumar Miga Hon, Adamu Sarki Miga aci-gaba da ayyukan raya ƙaramar hukumar Miga da yake gudanarwa, ƙarƙashin jagorancin sa, cikin hikimar Ubangiji, an kusa kammala aikin hanya mai tsawon kilomita uku wadda ya tashi daga Zango zuwa Zareku, wannan aiki ne da Gwamnatin ƙaramar hukumar ta bijiro dashi wadda zai lashe zunzurutun kuɗi na kimanin Naira (Miliyan ɗari uku)
Wannan aikin zai taimakwa rayuwar al'ummar wannan yanki wajen samun afuwar gudanar da zirga-zirga a wannan yanki, Gwamnatin ƙaramar ƙaramar hukumar Migan ta tabbatar ashirye take wajen tunkarar makamancin irin wannan ayyukan a wuraren da suke fuskantar matsalar hanya wajen gudanar da zirga-zirga.
Muna fatan wannan aiki zai samu kammaluwa cikin ƴan kwanaki kaɗan masu zuwa tare da fuskantar wasu manya ayyukan da zasu amfanar da al'ummar ƙaramar hukumar Migan baki ɗaya, muna yiwa jagororin mu addua'ar samun ƙwarin Gwiwar gudanar da ayyukan alheri a wannan yanki namu.🙏
Nura A Hussaini
Special Adviser on
New Media Office
Miga LGA ✍️