16/04/2024
A SIYASA WANNAN SHINE UBANGIDA NA.
Na Jima Ina siyasa, amma Bansan Me Ake Nufi da Siyasarba saida Na Hadu da wannan Bawan Allah.
A baya Siyasar Kawai Nake, Batare da Sanin ina na Dosa ba, Kuma Babu Wanda ya fadamin Ina Zanje A Tafiyar siyasa.
Amma bayan na Hadu da El-Rasheed Abdullahi Member Representing Dukku/Nafada Federal Constituency, Sai na Fahimci a Baya ba Siyasa nakeyi ba, Face Amfani ake dani Domin Yin siyasar.
K**ar dai Tayar Mota Haka ake amfani dani a Tafi idan Nayi Dotti a Wankeni ni, amma Wanda Nake bin a Shirye yake idan na Mutu ya sayo wata sabuwar Tayar ya saka, ni kuma ya jefar dani.
Amma BALA KELLY ya Chanzamin Wannan Matakin, Yanunamin hanya.
A Taredashi akwai Jajirtaccun mutane Guda Biyu, Wadanda Zuciyarsu Fari Tas take cike da Burin Ganin Cigaban Al'ummar Dukku/Nafada.
1. Usman Gorki S.L.A
2. Bobo Maikudi P.A
Tareda Shawarar Wadannan Aka Samu Dukkan Wata Nasara.
Wadannan Mutanen Sune Ke Tuka Motar Tafiyar BaLA KELLY.
Nasani, Kuma inada Yakini Al'ummar Dukku/Nafada Sai Kunce Nafada Muku Zamuga Alkhairinda Bamu taba Zato ba.
Daman Kafin Yanzu Mun Gani.
Wanda Ke zuwa Nan Gaba, Saiya Shafe Duk Wani Tarihi a Siyasar Gombe ta Arewa.
Muna Yaya shi da Addu'a Allah ya Kauda Idon Makiya akansa.
Allah ya Bashi damar Taimakon Al'ummar Dukku/Nafada K**ar Yadda Yakeda Kudurin Hakan a Zuciyarsa.
Wata Rana Nasha Mamaki da Bala Kelly yace a Wakilcinsa babu maganar Jam'iyya.
Yace a Yanzu Shi wakilin Al'ummar Dukku/Nafada ne baki Daya ko PDP ko APC kake Zai Taimaka maka Muddin Rabonka ya Rantse.
Sabanin Siyasar da Nayi a Baya, Su Kawai Dan Jam'iyyar Su Shi kadaine ya Dace a Taimakawa.
ALLAH KA MANA JAGORA.
Ameen summa ameen.
✍✍✍
Engr Sabiyu Bigbononza
BALA KELLY MEDIA