Jellah TV

Jellah TV An kirkiri wannan shafin ne domin nishadantarwa, ilimantarwa, tunatarwa gami da wa'azantarwa. Hausa sai Dan Hausa

17/11/2023
16/11/2023

Sheikh Ahmad Tijjani Yusif Guruntum

15/11/2023

Har abada zan sake yiwa mata kwalliya a yayin ɗaukar fim ba - Mansur Make-up

Mai sana'ar ƙwalliya a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Mansur Make-up, ya ce ba zai sake yiwa Mata ƙwalliya a yayin ɗaukar fim ba, domin ya gane cewa hakan kuskure a Addinin musulunci da kuma al'ada, wanda a baya Mutane da dama sun nusar dashi hakan, amma yana ganin k**ar ba masu ƙaunarsa bane, sai yanzu ya fahimci gaskiya.

Mansur ya bayyana haka ne ranar Laraba cikin wani fefen bidiyo, wanda yayi tsokaci akan kalaman jarumi Abdallah Amdaz bisa yadda yake fuskantar ƙalubale daga abokan sana'arsa, bayan wasu kalamai da ya furta a ranar Litinin din da ta gabata a hukumar Hisbah.

Jellah TV

Mugun mafarkin da ya ingiza matashi buga wa mahaifinsa tabarya a Kaduna'Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun k**a wani ma...
15/11/2023

Mugun mafarkin da ya ingiza matashi buga wa mahaifinsa tabarya a Kaduna

'Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun k**a wani matashi mai shekara 20, bisa zargin kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa tabarya bayan ya zuciyarsa ta kaddara masa cewa uban na yunkurin halaka shi.

"Ya shaida mana cewa yana yin mafarke-mafarke, inda yake ganin siffar mahaifin nasa, mai kimanin shekara 50, yana zuwar masa a cikin sigar jemage," in ji mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar.

ASP Mansur Hassan ya shaida wa manema labarai cewa suna ci gaba da gudanar da bincike kan matashin da suke zargi wanda ya fito daga yankin karamar hukumar Zangon Kataf.

Ya ce zuwa yanzu ba su samu wata shaida da ke nuna cewa matashin na da wata matsalar kwakwalwa, ko kuma yana shan kayan maye.

Jami'in 'yan sandan ya ambato matashin na cewa babu kyakkyawar alaka tsakaninsa da mahaifin, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

'Yan sandan sun ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da matashin mai suna David Phillips a gaban kotu

Jellah TV

A duk lokacin da akace min kaji tsoron Allah ka faɗi gaskiya, zuciyata bata samun nutsuwa har saina faɗa.Duk da cewa nas...
15/11/2023

A duk lokacin da akace min kaji tsoron Allah ka faɗi gaskiya, zuciyata bata samun nutsuwa har saina faɗa.

Duk da cewa nasan mafi yawan abinda zan faɗa zai haifar da gaba tsakanina da wasu mutanen, zaisa nayi bakin jini a gurin wasu.

To amma matukar hakan zai kusanta da Ubangiji, zaisa na samu yardarsa, wannan baya sakani nadama ko dana sani.

Nima ina da nawa laifukan, ina da abubuwan da nake marasa kyau, wanda ko yaushe nake rokon Allah ya gafarta min, yasa kuma na daina aikata su.

Don haka duk mutumin da maganata zataiwa zafi bai kai nawa zafin ba, don nima ina da iyaye da iyali, saidai duk wanda ya Sanni yasan halina, bana gudun magana matuƙar ban zalunci wani.

Abdallah Amdaz

An k**a shine a sakateriyar kungiyar NLC dake jihar Imo. Wannan na zuwa ne yayin da aka gaza samun daidaito tsakanin kun...
01/11/2023

An k**a shine a sakateriyar kungiyar NLC dake jihar Imo.

Wannan na zuwa ne yayin da aka gaza samun daidaito tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya.

01/11/2023

Gaddafi speech in front of Arab leaders 😥😔😭

Address

Dawakin Kudu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jellah TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category


Other TV Channels in Dawakin Kudu

Show All