24/03/2024
SIRRIN SAMUN SAUYI A KOWACE AL'UMMA..
Kowace al'umma tana samu ko yunƙurin kawo sauyi ne kawai, idan ta cika wasu sharuɗɗa guda uku su nek**ar haka:
1-Sharaɗi na farko: shi ne ya zama wannan al'umma din tana da (Mabda'i ingantacce) ma'ana ya zama tana da wani abu da take komawa zuwa gare shi ingantacce, kuma take ganinshi a matsayin wani abu me tsarki kuma abin girmamawa.
2- Sharaɗi na biyu: ya zama wannan al'umma din ta fahimci wannan mabda'in nata, hakikanin fahimta kuma cikakkiyar fahimta.
3- Sharaɗi na uku: ya zama wannan al'umma din bayan ta fahimci mabda'in, ya zama ta yi imani da mabda'in.
Idan al'umma ta cika wadannan sharuɗɗa to duk lokacin da ta yi yunƙuri domin kawo gyara to babu shakka za ta yi nasara, fiye da haka ma, idan al'umma ta cika wadannan sharuɗɗa ba zai yuwu barna da lalacewa su shiga cikinta har su yi mata tasiri ba.
Don haka Idan muka kalli al'ummarmu ta Nigeria a dunkule za mu ga cewa dukkan waɗannan sharuɗɗa guda uku na samun sauyi mun rasa su, ko kuma mu ce duk wadannan sharuɗɗan an hana mu samunsu, wasu kuma muna da su a can baya amma an yi kokarin raba mu da su. Saboda idan muka kalli sharaɗi na farko "mabda'i" kuma muka kalli Nigeria a dunkule, za mu ga cewa ba a kafa ta a kan wani mabda'i ko wani asasi ba, saboda idan muka koma can baya a tarihi za mu ga cewa al'ummu ne kala biyu ( ýan yankin kudu marasa addini da ýan yankin arewa masu addini) aka dauko su aka gwama aka samar da Nigeria. Don haka babu wani mabda'i da aka ɗora Nigeria a kai, ko aka kafata domin shi, kenan mun rasasharadi na farko tun asali don haka sauran sharuddan ma mun rasa su wato fahimtar mabda'i ko imani da shi, saboda su suna biye masa ne sai ya tabbata za su tabbata.
Wannan nigeria kenan a dunkule, sannan idan muka dawo yankinmu na Arewa, za mu ga cewa mabda'i dai muna da shi, shi kuma mabda’in nan ko dai ya zama addini ko kuma ya zama al’adu da tarihi, kuma dama kakaninmu suna da addinin muslunci, kuma sun yi imani da shi, kuma sun fahimce shi daidai bakin gwargwado. Wannan ma shi ne dalilin da yasa, har s**a iya samar da abin da ake cewa Daular Usman Ɗan fodiyo, Kuma s**a yi nasara. Saboda me? Saboda waɗancan sharuɗɗan sun cika. suna da mabda'i kuma sun fahimce shi dai gwargwado kuma sun yi imani da shi, bari mu kalli fuslkacin addini kafin al’adu da tarihi.
A yau babbar matsalar da take damunmu a yankin arewa da ta sa kullum baya muke ci, kuma muke samun cigaban me shiga rijiya shi ne: tun bayan da aka rusa wancan abin da kakaninmu s**a yi na samar da addini da tsarin musulunci, sai aka shigo mana da tunaninnuka sababbi marasa ma'ana wadanda s**a nisanta mu da al'adunmu da ɗabi'unmu na muslunci.
Na farko, wancan addinin da muke ruko da shi an gurɓata shi, ta hanyar bin duk inda addini yake da tasiri a gurɓata shi, babban abin da aka fara gurbtawa su ne malamai, saboda su ne addini yake a hannunsu, kuma su ne ke faɗa a ji. Sannan kuma aka sanya mana tsarin zaɓo wawaye a matsayin shuwagabanni, kowane wawa wanda be san kansa be san ina aka fito ba b***e inda aka nufa kawai sai ya fito takara ya zama shugabanmu, kuma da wannan wawancin nasa ake amfani wajen shigo da tunaninnuka munana da suke nisantar da mu daga al'adunmu, saboda dama hukuma ita ce take da alhakin lura da wadannan abubuwan.
Don haka sai al'ummarmu ta zama k**ar wata abar farauta ta bangare uku, ɓangaren turawan yamma, da bangaren wawaye shuwaganni, da bangaren makwadaitan malamai, saboda su dai turawa burinsu shi ne kada mu cika waɗancan sharuɗɗa saboda kada mu fita daga ƙangin bautarsu, su kuwa shugabanni abin da ya dame su kawai shi ne me za su samu me za su tara wa iyalansu a kasashen waje?! Don haka kullum sata suke da lalata kasa, a cikin haka kuma sai suke amfani da malami, saboda su turawa sun karanci mutumin Afrika ko Nigeria ta arewa sun gano cewa mutum ne mai son addini da mutunta shi, kuma yana mutunta wanda ya sanya rigar addini a cikin jama'a, sai ya zama shugabani suna amfani da hakan wajen sanya malamai su dinga ba ƴan kasa hakuri, suna tara laifin duk wata barna da rashin cigaba ga Allah (t) da cewa ai Allah ne ya kawo ba shuwaganni bane, wannan shi ne abin da ake ce wa: ( التماهي والتخادم بين علماء الدين والسلطة الحاكمة) "Wato cuɗanni-in-cuɗe ka tsakanin malamai da masu mulki" wannan ne ya sa duk lokacin da wani ya fito domin nuna cewa hukuma ta yi ba daidai ba, ya k**ata a yi mata bore, sai kaji malamai sun dira a kansa sun ce ai haramun ne yi wa hukuma bore, misalan irin haka bayyanannu ne ga duk wani dan Nijeriya a yanzu.
Don haka abin da ke faruwa shi ne malamai sun zama yan siyasa dumu-dumu! Sai ya zama duk wata izza da malami yake da ita an kwace ta hanyar mayar da shi makwadaici ko dan siyasa. Wannan ya sa su da kansu malaman s**a yi watsi da hakikanin manufofin addini s**a cusa kansu cikin siyasoshi, kuma dama addini ne yake da alhakin samar da wadancan sharuddan ta hanyar malamai, saboda su ne ke da alhakin wayar da kan mutane da bas u mafita. Saboda haka sai ya zama an rusa mana mabda'inmu wato addininmu ta hanyar lalata malamai a fakaice, kenan ba mu da mabda'i.
Wannan bisa kaddara cewa addini shi ne zai zama mabda’i kenan!
TARIHINMU DA ADDININMU
Abu na biyu da ya k**ata ya zama mabda'inmu wanda shi ma aka raba mu da shi, shi ne al'adunmu na Hausawa da tarihinmu, kuma duka kiyaye su yana a hannun hukuma ne, amma tunda tunda tsarin da aka sa mana na zabo shugaba wawaye yake tsayar mana a matsayin yan takara kuma shuwaganni, wannan ya sa sam ba su damu ba. saboda yanzu ko jami'o'i ka je kana karanta harshen hausa ko asalin Hausawa za ka ga sam babu wani bayani tak**aimai dangane da hausawa, saboda zantuka ne za ka gani na mutanen yamma suna bayanai masu cin karo da juna dangane da asalin bahaushe ko mutanen arewa, wanda hakan ke son ya bayyana wa ɗalibi ko mai bincike cewa bahaushe fa ba shi da wani asali. Kuma ai ba wai ba mu da tarihin bane, a'a muna da shi, kuma ba wai ba mu da asali bane, a'a muna da shi, sun yi aiki tukuru ne domin lalata shi ta hanyar sanya tarihimu wanda ake karantarwa a makarantu da jami'o'i ya zama duka ra'ayoyi ne da rubuce-rubucen turawa, to ya kake tunani idan ya zama makiyinka shi ne zai rubuta tarihinka?!
Kuma a nan za mu fahimci, zancen nan na hikima da ake cewa: "duk wanda ba shi da jiya, ba shi da yau kuma ba shi da gobe" abin nufi duk wanda ba shi da tarihi mai kyau to fa zamaninsa ma ba zai yi kyau ba, haka gobensa ma. Wannan kuma shi ke kara jefa nigeria cikin mummunan halin da take ciki, musamman yankin arewa, mutumin arewa ba shi da wani abu a yanzu da zai kalla na tarihi da zai yi alfahari da shi. Sawa'un a bangaren addini ko a ɓangaren al'adu, duka an nuna masa cewa ba su da wata kima shi kuma ya amsa ya yarda.
Haka abin yake idan muka kalli al’adunmu su ma an raba da su sai yan wadanda ba a rasa ba, sabod al’adunhausawa yanzu sun zama kauyanci da rashin wayewa acikin al’ummunmu, kuma hakan ya kasance saboda kawo mana sababbin al’adun turawa na zamani.
A bisa wannan, mutanen arewa ba su da mabda'i, ko kuma mu ce suna da mabda'i, amma an lalata shi, an rusa shi kuma an raba su da shi.
To idan ya zama ba mu da mabda'i Kaga ba maganar fahimtarsa, saboda duk abin da babu shi ba za a yi maganar fahimtarsa ko rashin fahimtarsa ba. Kuma duk wata al'umma da bata da mabda'i, to lallai ba fa zata taɓa yin nasara ba, kullum zata ci gaba da lalacewa ne.
A daidai wannan gabar ne Allah ya albarkaci wannan yanki da wani malami mai tunani da zurfin hangen nesa, masanin zamaninsa da addini, Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky (H), wanda ya zama shi kullum kiransa shi ne al'ummar wannan yankin ta koma zuwa ga tarihinta, kuma ta koma zuwa ga abin da ta gada, saboda tasirin da hakan yake da shi wajen zaburantarwa da yunkurawar duk wata al'umma zuwa ga cigaba da cin nasara da wayewa.
Don haka sai ya zama shi kullum kiransa shi ne al'ummar wannan yanki ta haɗu wato ta haɗa kanta, ta yi watsi da inda ta samu sãɓãni, amma inda aka haɗu a haɗu a yi aiki tare domin dawo da kimar wannan al'umma, ta hanyar mayar da ita zuwa ga tarihinta, kuma dama tarihin nata shi ne addini, saboda idan aka koma zuwa ga tarihi hakan yana nufin an koma zuwa ga addini ne, idan aka koma zuwa ga addini to hakan yana nufin al'ummar arewa ko Hausawa sun riki mabda'i, idan aka riki mabda'i (addini) kuma aka yi imani da shi, daga nan kuma sai a yi kokarin fahimtarsa. Idan aka fahimci mabda'i, to daga nan ne al'umma zata fara motsi zuwa cigaba.
Kuma lallai wadanda s**a kwace mana waɗancan abubuwa guda uku sun fahimta dakyau haɗarin wannan aikin da wannan shehin malamin (H) ya dauko, saboda in dai ya kai gaci to babu makawa al'umma zata ýantu kuma zata kai zuwa ga inda take burin kaiwa a cigaba da wayewa, kuma saboda haka ne wannan shehin malami ya hadu da abin da yake haduwa da shi har gobe na dauri kala-kala da kashe iyali da rusa gidaje da muhallan addini.
Saboda haka ne s**a yi kokarin bakanta sunansa a idon mazauna wannan yanki ta hanyar bakanta akidar da yake a kai da nuna cewa shi maƙiyi ne ga kasa yana so ya rusa ta!
To Nigeria ce fa, dama ai ba mu muka ƙirƙire ta ba, kuma ba saboda mu aka ƙirƙire ta ba, to sai me in ta rushe? Wannan bisa kaddara cewa abin da suke faɗa gaskiya ne cewa rusa kasa yake son yi. Sai dai a haƙiƙa shi yana so ya kauda abin da turawa s**a kafa ne ya dawo da abin da muka gada na al'adu da addinai, wato abin da yake kokarin kawarwa shi ne lalataccen tsarin da aka kawo domin amfanuwar yahudawa da turawan yamma, sai ya maye gurbinsa da tsarin da zai taimaki mazauna yanki da kasa.
Muhammad Ishaq Ɗanmaigauta