Sabiu abubakar

Sabiu abubakar Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sabiu abubakar, Video Creator, Katsina state danja local government filin yan gwari, Danja.

07/05/2022
28/04/2022
Ina masu sayen daya ko sari muna bada su akan kudin kalilan babu tsawwalawa
07/03/2021

Ina masu sayen daya ko sari muna bada su akan kudin kalilan babu tsawwalawa

11/02/2021
Zaman tare
25/11/2020

Zaman tare

24/09/2020

Uhhhmm funny

Inatayaku murna dama zamanku a Chelsea babbar illache
17/07/2020

Inatayaku murna dama zamanku a Chelsea babbar illache

Lokaci kenan
17/07/2020

Lokaci kenan

17/07/2020

Wakili sabon shiri

14/07/2020

RANAR DA SAYYIDUNA UMAR YAYI SHAHADA :

Aranar 26 ga watan Dhul Hijjah, shekara ta 23 bayan hijirah (daidai da 03 ga watan November 644 miladiyyah) Sayyiduna Umar bn Khattab (rta) yayi shahada sakamakon s**ansa da wuqa har sau shida (a wata riwayar kuma an ce sau 3 ne) da wani la'anannen bamajuse yayi, mai suna Fairuz Abu Lu'u-lu'ah Almajusiy (tsinuwar Allah da Mala'iku ta tabbata akansa). Wai saboda ya kawo Qarar ubangidansa amma sayyiduna Umar bai goyi bayansa ba.

Bayan an dawo dashi gida, sai aka bashi nono (madara) ya kurba amma nonon bai zauna acikinsa ba, yayin da likitansa yaga nonon yana fita ta kwibinsa sai yace masa "Ya Sarkin muminai! Yi wasiyyah domin hakika alamomi sun nuna kamar ba zaka rayu ba". (dama Sayyiduna Rasulullahi ya ta'ba yi masa busharar cewa abincinka na karshe aduniya nono ne).

Sai Sayyiduna Umar ya kira babban 'dansa mai suna Abdullahi bn Umar (ra) yace masa "Jeka kira mun Huzaifah bn Yaman (rta)". Huzaifah shine sahabin nan wanda Manzon Allah ﷺ ya sanar dashi sunayen munafukai wadanda babu wanda yasansu sai Allah da Manzonsa ﷺ sai kuma shi Huzaifah din.

Sayyiduna Umar yana magana jini na fitowa ta kwibinsa, yace "Ya kai Huzaifah bn Al Yaman!! Ina yi maka magiya da Allah, shin ko kaji Manzon Allah ﷺ ya ambaci sunana acikin sunayen munafukai?".

Huzaifah yayi shuru hawaye na zuba daga idanuwansa, yace "Annabi ﷺ ya bani amanar wani sirri ne wanda bazan iya fa'darsa ba, Ya Umar!".

Sai yace "Ina yi maka magiya da girman hakkin Manzon Allah ﷺ Shin kaji Manzon Allah ﷺ ya ambaci sunana?".

Sai Huzaifah ya fashe da kuka, yace "Zan gaya maka, amma bazan sake gaya wa waninka ba. Wallahi Manzon Allah ﷺ bai ambaci sunanka awajena ba".

Sai Sayyiduna Umar ya nisa, yace "To yanzu kuma abu guda ya saura gareni aduniyar nan.. Sai 'dansa (Abdullahi bn Umar) yace "Menene shi, Ya babana?".

Sai yace "So nake a binneni kusa da dugadugan Manzon Allah ﷺ. Ya kai 'dana jeka wajen A'ishatu uwar muminai, kada kace mata 'Sarkin Muminai' Kace mata 'Umaru' ne yake neman izininki domin kece mai 'dakin nan. Idan kinyi izini yana so a binneshi a Qasar dugadugan abokan rayuwarsa din nan guda biyu (wato kusa da Manzon Allah ﷺ da kuma Sayyiduna Abubakrin).

Sai tace "Na kasance na tanadi wannan wajen ne musamman domin kaina. Amma yau na bar wa Umar".

Abdullahi 'dan Umar (ra) da yaji haka sai ya dawo da farin ciki yace wa mahaifin nasa "Ya Babana! Ai ta yarda ta bada izini". Amma dubawan da zai yi sai yaga mahaifin nasa ya dora kumatunsa akan Qasa, sai ya zauna kusa dashi ya dauko kansa ya 'dora bisa cinyoyinsa.

Sayyiduna Umar ya 'daga kai ya kalli 'dan nasa, yace masa "Don me baka bar kumatun nawa akan Qasa ba?".

Sai yace "Ya babana....!" kafin ya fa'di abinda zai fa'da sai Uban yace masa "'Dora kumatun mahaifinka akan Qasar nann domin yai birgima akanta! Kaiton Umaru idan Allah bai gafarta masa ba, a gobe Alqiyamah!!".

Babu da'dewa sai yaja numfashinsa na karshe, ruhinsa mai tsarki ya koma zuwa ga Ubangijinsa, ruhi yardajje kuma abin yarjewa ga Allah..

Amma kafin ya rasu ya Qara yin wasiyyah ga 'dan nasa cewa "(bayan na rasu) idan ka daukeni ka kaini masallacin Manzon Allah ﷺ ka sallaceni, to kayi duba zuwa ga Huzaifah watakil ko kunyata yaji, bisa amsar da ya bani.. To idan kaga Huzaifah cikkn wadanda s**a sallaceni to ka daukeni zuwa kofar gidan Manzon Allah ﷺ ka tsaya akan Qofa, sannan kace wa Nana A'isha (rta) :

"Yake uwata! 'danki ne Umaru 'dan Khattabi muke neman izinin shigowa dashi, kar kace Sarkin Muminai. Idan tayi izini sai ku shigar dani. Idan kuma batayi ba, ku dawo ku binneni a makabartar sauran musulmai".

Bayan rasuwar tasa, an dauki jikinsa an kai cikin masallacin Sayyiduna Rasulullahi ﷺ, sai Abdullahi bn Umar ya duba cikin jama'ar da s**a sallaceshi sai yaga har da Huzaifah (rta) ganin haka sai Ibnu Umar yayi farin ciki ya daukeshi zuwa kofar gidan Nana A'isha (ra) yace "Ya Uwarmu! 'danki ne Umaru a kofar gida muke neman izinin shigowa dashi".

Sai tace "Ku shigo dashi".

Allahu Akbar!! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!! A wannan ranar duniya tayi babban rashi, lahira kuma tayi babban baqo. Ya Allah yi salati mafi cikar haske, da aminci mafi cikar Qamshi bisa Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki dayansu. Ka Qara yardarka bisa Khalifofinsa shiryayyu yardaddu.

FASSARA DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 08157968686 (12/07/2020 21/11/1441).

09/07/2020

Idan kana da Digirin Digirgir a daukar Hoto.

DIMOKURADIYYA.

09/07/2020

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!

Mun samu labarin rasuwar Abubakar Abbas Matazu, ya rasa ranshi ne sakamakon harbin da 'yan bindiga s**a yi mishi akan hanyar Karaɗuwa zuwa Matazu dake jihar Katsina a ɗazun nan.

Allah muke roko ya jiƙanshi ya gafarta mishi Allahumma Amin

Allah yasa da alkhairi
08/07/2020

Allah yasa da alkhairi

08/07/2020

All things Blancos: latest news and instant scores, video highlights and stats, transfer rumors and expert opinions at Tribuna.com

08/07/2020

Wani sako da kungiyar Boko Haram ta ce ta fitar daga jihar Neja mai makwabtaka da Abuja na iya ta'azzara matsalar tsaro a babban birnin kasar.

07/07/2020

Uhhmm yakamata mu kalli wanann

07/07/2020
07/07/2020

A ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, muƙaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya amsa gayyatar kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin gudanar da bincike a kanshi. Ana kishin-kishin din cewa wannan kwamiti zai bada shawarar a sauke shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zago...

06/07/2020

Address

Katsina State Danja Local Government Filin Yan Gwari
Danja

Telephone

+2349069465234

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sabiu abubakar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sabiu abubakar:

Videos

Share

Category



You may also like