09/12/2024
DA DUMI-DUMI:Gwamna Bala Muhammad ya amince da Ƙirƙiro Masarautar Sayawa a Jihar Bauchi.
Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya sanarda Matakin Gwamnatin Jihar Bauchi game da batun ƙirƙiro Masarautar Al'ummar Sayawa a Jihar Bauchi.
Yayin wani taron Masu Ruwa da tsaki, Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Bauchi ta amince da kafa Masarautar, wanda za'a ajiye Fadar ta a Cikin Garin Tafawa Balewa.
Gwamnan yace Gwamnatin Jihar Bauchi Ba tada wani "Ra'ayin ƙashin kai" game da batun ƙirƙiro Masarautar kuma an bi dukkan hanyoyin doka gabanin yanke Hukuncin.
Bala Muhammad ya bayyana Matakai da aka tsara bi wajan zaɓo sabon Jagoran Masarautar wanda za'a ke kiran sa "Gungzaar".