Zulkifli Yusha'u Burgel

Zulkifli Yusha'u Burgel Riko DA ALLAH maganin waiyo Allah

24/11/2022

Ita mace ko kuka 😭 takeyi takan duba madubi taga ko kukan yayi mata kyau...
🙄🙄🚶🚶

MUNA SAURARON MUHADARA NA KWAMITIN WA'AZIN MATASA JBWS JOSS AGARIN ZULL T/BALEWA L.G.AMAUDU'I(FADLUL ILIMI WA AHAMMIYATI...
24/11/2022

MUNA SAURARON MUHADARA NA KWAMITIN WA'AZIN MATASA JBWS JOSS
AGARIN ZULL T/BALEWA L.G.A
MAUDU'I(FADLUL ILIMI WA AHAMMIYATIHI)
TARE DA: MALAM MUHAMMAD TUKUR ABDULHAMID TUDUN WADAN SHALL

02/11/2022

Allah ya saka da Alkhairi

Wannan ita ce rijiyar Ghars wacce Manzon Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a yi masa wanka da ruwa...
01/11/2022

Wannan ita ce rijiyar Ghars wacce Manzon Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a yi masa wanka da ruwanta bayan ya yi wafati.

📸 madeenahalmunawwara.

29/10/2022

Ameen ya Allah

29/10/2022

MATA MUTANENMU

Nasir Almustapha Sheshe ya rubuta:

Yau naci karo da abunda yafarantamin rai Allah ya ƙara ma annabi daraja amin 😍😍

Jiya bayan na fita kasuwa sai kawai naga mai ɗakina ta min magana a WhatsApp. Abban Sultan yau kaji da kifi muke buƙata a gidan. Nace toh kuci mana. Sai tace zaka aiko dasu yanzu ko mu saya anan? Nace ku saya anan ɗin. Tace guda nawa kajin Tarwaɗar, kuma kilo nawa? Cikin gatse nace mata kaji 10 tarwada kilo 5

Tace wow ta tura wasu stickers.

Toh ni dai nasan ban ajiye ko sisi a gidan ba iyaka dai in ta saya da kudinta sai ta dora akan bashin da ake kakaba min na babu gaira babu dalili

Kuma nama san ba zata iya sayen adadin da nayi mata gatse ba. Karkari tayi kuru ta sayi kowanne guda dai dai..

Kuma na kudurce a raina in ta saya bazan biya ba.

Kawai na sauka daga WhatsApp na kashe data ma dan kar muyi dogon zance.

Ga mamakina ina dawowa naga an gama gyara komai k**ar yanda na ambata an soya na soyawa anyi farfesun wasu wasu anyi miyi saura kuma ansa a FIRIZA

A Raina nace zanci banza kenan Dan wlh ba biya zanyi ba. Na ɗauki wayata na kira abokina nace kar kaci komai fa yau kazo gidana yar Aljanna ta shirya mana liyafa.

Na kalleta cikin murmushin ƙeta nace ina zoɓo. Tace ai aiki ne yayi yawa amma na siyo five alive. Nace wohoho! Allah Ya baki Aljanna, tace Ameen.

Bayan naje sallar Magariba sai nace bari in biya gidan su amaryar can in karɓo kuɗin ankon dana fidda musu. Maƙociyarmu ce bikinta za'ai kuma ni na fidda ankon nata. Akwai kuɗin turmi 10 da zata bani dama.

Ina biyawa nayi sa'a kuwa ta dawo daga rabon goro nace mata amarsu miko inyi gaba. Tace me fa? nace 45k, tace auho! Baka koma gida bane? Nace daga gidan nake, naje sallar Magariba ne sai na biyo tanan. Tace okay ai tun safe na shiga tace yanzun nan ka fita kasuwa, sai na bata kudin.

TUN JIYA BAYAN MAGARIBA NAKE FAMA DA WANI ABU ME KAMAR ZAZZABI.

BAKINA SAI DACI YAKE.

20/09/2022

Wato Sunaye. Mata yawanci Baya Huce Harafi 7 zuwa 6 Wazai kawo sunan mace Mai Harafi 10 🏃🏃🏃🏃

02/09/2022

Shugaban Masu Gaskiya
Jagoran Sada Zumunchi, Sarkin Adalchi.
Muhammad Rasulullah ﷺ 💕💘

02/09/2022

Wahalale shine wanda ya wahalar da kansa wane binciko aibin mutane
Allah kasare mana imaninmu

24/08/2022

Alhmdulillah Alhmdulillah Alhmdulillah

12/07/2022

Kuskure ne iyaye su dinga barin saurayi da budurwa a keɓantaccen waje da sunan hirar soyayya, musamman da daddare. So samu ne a yi hirar ido na ganin ido - komai Ustazancinsu kuwa. Saɓon Allah baya buƙatar niyya. Kauce wa hanyoyin faruwarsa ake. Idan ta k**a, za'a iya amincewa da matashi mai jini a jika akan kuɗi komai yawansu, amma ba akan mace ba.

Muhammad Khalid Idris

Address

Burgel
Bauchi
08146102146

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zulkifli Yusha'u Burgel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zulkifli Yusha'u Burgel:

Videos

Share

Category