Opphicial_suleiman

Opphicial_suleiman LABORATORY TECHNOLOGIST
MICROBIOLOGIST
HEALTH WORKER

14/10/2025

Garin da aka niƙo ta hanyar banza, wajen hwaro-hwaron banza ya ke ƙarewa

14/10/2025

Digiri Ko Sana'a?

Idan kana da damar haɗa biyun to ka yi. Idan kana da kuɗin da za ka biya ko za a biya maka makaranta mai kyau da karatu mai inganci to kada ka bar damar ta wuce ka. Amma idan kai talaka ne, ba ka da kuɗin ɗaukar nauyin yin karatu mai inganci, babu mai ɗaukar nauyinka, na fi ganin ka nemi sana'a kawai, domin galibin irin waɗannan su ke shan wahala, sai ka ga mutum ya gama digiri da jiɓin goshi, kuɗin registration da TP da ƙyar yake biya, sa'an nan kuma bayan ya gama ya fara wata sabuwar wahalar ta neman aiki. Kuma koda ya samu aikin, albashin bai wuce kuɗin abinci da TP da ƙananan buƙatu ba.
Akwai waɗanda s**a haƙura da karatun saboda ba su da hali, s**a k**a sana'a da kasuwanci, daga ƙarshe sun samu kuɗin da s**a biya wa kansu karatu a manyan makarantu na duniya.
Ni a yadda na fahimci rayuwa, kada ka kushe abu don ba ka da ra'ayin sa, ka bar kowa da abin da ya zaɓa wa kansa matuƙar ba saɓon Allah ba ne. Kai ma akwai wanda ba ya ra'ayin abin da ka zaɓa wa kanka, idan ya kushe ba za ka ji daɗi ba.
OCTOBER/2025
Opphicial Jargaba

14/10/2025

Ɗalibin ilimi da hujja yake yaƙi ba da izgili ko zagi ba.

19/06/2025

Duk macen da ta yi shiga k**ar akuya, ba ta kyamaci namiji mai halin taure (bunsuru) ba.

19/06/2025

Ƙaunar ci gaba da aikin cigaba a rayuwa ke sa a ci gaba, ba son a iso su wane ko a wuce su wane ba. Babu alheri cikin kishi akan matsayi ko ɗaukakar da wani ya samu.

19/06/2025

"Wanda ya auri macen da take taimakonsa akan bautar Allah shi ne wanda ya rabauta" [Ibnu Rajab]

19/06/2025

Babban sinadarin tabbatacciyar nasara shi ne GASKIYA.

19/06/2025

Yi ƙoƙari ka nisanci duk abin da zai jawo maka zargi...!

Address

Bakin Kasuwa Jargaba
Bakori

Telephone

+2348120947406

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Opphicial_suleiman posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share