18/08/2023
(((❗MUTUWA DOLE❗))).
🌹= Yayin da ranka yazo makogoro, a wannan lokacin zaka manta da makusantanka, iyalanka ko 'Ya'Yanka b***e makubta. A wannan lokacinne Dan Adam yakanji Qishirwa mai tsanani wacce sai ya gwammaci inama yabayar da dukkan abunda ya mallaka domin abashi ruwan koda kurbi guda ne!!.😭
ZAFINDA BAWA YAKEJI YAYIN FITAN RAI...
🌹= Hakika Fitan Rai yanada wani irin Radadi wanda babu mai saninsa saidai mamacin..😭
🌹= mamaci yayinda Ransa yakusa fita, mauryansa takan karyewa, karfin jikinsa yakan tafiya, babu damar eihu ko kururuwar zafinda yakeji, domin zafin mutuwa yariga ya ratsa dukkan sassan jikinsa..😭
🌹= Bazai samu daman neman taimako ba, ballantana a dauke masa zafin radadin da yakeji, sai yayi fatan wannan nishinda yakeyi ko zaizama dalilun samun rangwame amma inaa.!!😭
🌹= idan har akwai ragowar wani Qarfi a gareshi shine za'a rinka jin wani gurnani yana fitowa daga chan chikin Qirjinsa da makogoransa yayinda rai yazo fita..Alhali launin fiskansa ya chanza saboda tsananin halinda yake cikiii!!.😭
🌹= A wannan lokacin Duniya da dukkan abin cikinta zasu zamanto ba komaiba agunsa, Ballatana Dukiya ko Mulki ko wani Gata a wannan lokacin 'Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai bane... kuma tundaga sannan zai fara nadamar lokutan rayuwarsa da s**a tafi awajen sa'bon Allah!!.😭
🌹= zan mutu
zaka mutu
zaki mutu
wlh watarana za'a wayi gari babu mu,
wannan Duniyar da muke nema,
wannan Duniyar da mukewa ado,
wannan Duniyar da muke takama da ita,
wlh ba matabbata bace,,😭
🌹= wata rana zamu tattaru a gaban mahaliccin mu domin auna ayyukan mu, Allah ka gafarta mana badon Halinmu Ba..👏
DUK WANDA WANNAN SAKO YAXO MASA YAYI KOKARI YA TURA WASU DOMIN NEMAN GAFARAN ALLAH.
YA ALLAH KAGAFAR TAMANA ZUNUBANMU.