Dutsen-Reme Post

Dutsen-Reme Post Wannan shafi zai dinga kawo muku zafafa kuma sahihan labarukan abinda ke faruwa ba a iya Dutsen-Reme kawai ba, a ƙasa baki ɗaya da ma wajen ƙasar.

12/10/2023

Inalillahi wa'inna'illahirrajiun
ALLAH yayi ma shamsu kabiru na gidan su sule naira rasuwa, yanzu nan a general hospital Funtua bayan fama da yar gajeriyar jinya da yayi , Allah ya jikansa da gafara.

Zana'ida karfe 2:30
Layin chemist din Ibrahim karama ,wajan sola
~ Abdullahi Sanusi Mango

12/01/2023

Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

A yau Laraba ne dai ɗan Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano.

Ya bayyana cewa sun haɗu da marigayi Ummita ne a 2020, bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi.

Jaridar Justice Watch ta rawaito cewa ɗan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta riƙa karɓar kuɗaɗe a wajen sa, ya ƙara da cewa " haka na riƙa bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na ɓata mata rai. Ma kashe mata kimanin Naira miliyan 60,"

Ya ƙara da cewa har gida na miliyan 4 ya sai mata, amma sai ji yayi ta yi aure, bar hakan ya ɓata masa rai ya koma Abuja da zama.

"Amma duk da haka ta riƙa kira na tana hira da ni ta WhatsApp. Bayan nan ta ce min auren ya mutu, shine soyayyar ta mu ta dawo,"

A cewar sa, wata rana ta tambaye shi kuɗi shi kuma ya ce bashi da shi, shi ne Ummita ta yi fushi da shi har ta deba kula shi.

"Kawai sai ta ce min ta samu wani saurayin, har ma ta turo min hoton ta da shi sabon saurayin nata, lamarin da ya fusata ni," in ji shi

Alƙalin kotun, Sanusi Ado Ma'aji, ya bada umarnin a ci gaba da tsare Quanrong a gidan yari, sannan ya ɗage zaman zuwa gobe Alhamis domin ci gaba da sauraron kariya.

09/01/2023
05/01/2023

Ni zan kayar da Zulum a zaɓe mai zuwa, ƴar takarar gwamna a Borno ta ci alwashi

Yar takarar gwamna a jihar Borno a jam'iyyar ADC, Fatima Abubakar, ta ce tana da kwarin gwuiwar lashe zaben gwamnan na ranar 11 ga watan Maris, duba da ci gaban da aka samu a baya-bayan nan.

Abubakar, mace daya tilo da ta tsaya takara a zaben ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Maiduguri ra yau Laraba cewa ta fara kamfen gida-gida don jin ta bakin al’ummar jihar.

Ta ce tana samun karin goyon baya da farin jini daga masu zabe, tana mai cewa ta kusa samun nasarar lashe zaben.

“Ina kara samun farin jini tare da karin magoya baya, musamman matan da s**a yi imani da karfina na kawo sauyi mai inganci a rayuwar mata da matasa a Borno.

"Ina so in yi kira ga mata da matasa da muke tuntubar juna, suma su isar da sakon ga wasu kan bukatar a gwada 'yan mata 'yan takara a wannan takara don samun canji mai kyau," in ji Abubakar.

Wasu fusatattun 'yan Boko Haram ne s**a harzuka tare da afka wa bangaren ISWAP, bayan kisan kwamandansu Abubakar Munzir ...
06/12/2022

Wasu fusatattun 'yan Boko Haram ne s**a harzuka tare da afka wa bangaren ISWAP, bayan kisan kwamandansu Abubakar Munzir da karin wasu mayaka 15.

Bayanai na cewa tun a ranar 3 ga wannan wata na Disamba, jagoran Boko Haram na dutsen Mandara, Ali Ngulde tare da ayarinsa s**a kaddamar da farautar 'yan ISWAP da ke a dajin Sambisa.
~ DW Hausa

Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya fara aiki a safiyar Litinin bayan watanni 9 da kai hari kan jirgin.An dauki sabbin matakai ...
05/12/2022

Jirgin kasan Abuja-Kaduna ya fara aiki a safiyar Litinin bayan watanni 9 da kai hari kan jirgin.

An dauki sabbin matakai na tabbatar da tsaro a cikin jiragen, ciki har da tura ‘yan sanda dauke da mak**ai.

An kuma samar da wata na’ura inda fasinjoji za su iya haska tikitin jirgin da s**a siya maimakon bin layi a nuna wa masu duba tikiti.
~ BBC Hausa

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya isa birnin Washington DC na kasar Amurka ...
02/12/2022

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya isa birnin Washington DC na kasar Amurka domin ganawa da manyan jami'an gwamnatin Amurka.

Hotuna:NNPP

Wata uwa ta fille kan danta dan wata 11.Daga BBC HausaGetty ImagesCopyright: Getty ImagesAn k**a wata mai suna Blessing ...
01/12/2022

Wata uwa ta fille kan danta dan wata 11.

Daga BBC Hausa

Getty ImagesCopyright: Getty Images
An k**a wata mai suna Blessing bisa zargin ta da kashe danta dan wata 11 a kauyen Ugep, da ke karamar hukumar Yakurr na jihar Cross River.

Jaridar PUNCH ta ce jami'an 'yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru ne daidai lokacin da matasa ke kokarin lakada wa matar duka.

Lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce yanzu haka matar tana hannun hukuma.

Ugbo ya kara da cewa "ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ta yanka yaron, amma labarin

AN JANYE DOKAR HANA MASU TUKA ADAIDAITA SAHU BIN WASU TITUNA A KANO...Sanarwa ta nuna cewa Gwamnatin Kano ta dakatar da ...
30/11/2022

AN JANYE DOKAR HANA MASU TUKA ADAIDAITA SAHU BIN WASU TITUNA A KANO...

Sanarwa ta nuna cewa Gwamnatin Kano ta dakatar da dokar da ta sanya na hana matuka Adaidaita Sahu bin wasu Tituna a birnin Kano...

Sai dai duk da haka, Gwamnatin ta amince da baiwa wasu daga cikin masu tuka Adaidaita Sahu da yan kungiyar masu tuka Taxi sabbin motocin da zasu dinga amfani dasu wajen gudanar da sana'ar tuki a Kano, cewa da nayi An basu ba ina nufin Kyauta ba, an basu bisa Ka'idoji da s**a sanya hannu akai...

Sannan su kansu manyan motocin Saffa da Gwamnatin ta fito dasu kan tituna, zasu cigaba da nasu aikin tare da wadannan sabbin...

Sabbin motocin guda Hamsin ne zasu fara aiki a karon farko, zaa cigaba da fito da wasu sabbin don inganta hanyoyin sifuri a birni da kewaye, akwai ma wasu motocin na musamman da aka tanada saboda masu zuwa daurin aure ko taro a wasu jihohin, mutane zasu je su cika kaida su biya kudi a basu manyan motoci masu AC ko marasa AC ya danganta da wacce ake so....
~Rabi'u Biyora

Aisha Buhari: Kotu ta tura Aminu Muhammad gidan yariDaga BBC HausaBBC ta gano cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake z...
30/11/2022

Aisha Buhari: Kotu ta tura Aminu Muhammad gidan yari

Daga BBC Hausa

BBC ta gano cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja babban birnin kasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba s**a nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

''Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.''

''Akan haka muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,'' in ji CK Agu.

Tun da farko iyayen dalibi Aminu Muhammad sun fada wa BBC cewa za a gurfanar da dan nasu kotu yau Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman jiya Talata, kuma za a sake wani zaman yau ko gobe don duba bukatar ba da shi beli.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace '' yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.''

Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin k**a shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

ASALIN SUNAYEN WASU MAKARANTU A FUNTUAHamisu Adamu Gamarali Funtua 29/11/20201. Aya Primary School Funtua (1952)Sunan Ay...
30/11/2022

ASALIN SUNAYEN WASU MAKARANTU A FUNTUA
Hamisu Adamu Gamarali Funtua 29/11/2020

1. Aya Primary School Funtua (1952)
Sunan Aya ya samo asali ne da sunan matar Sarkin Maska muhammadu Sani Wanda shine na 15 a jerin sarakunan kasar Maska Kuma yayi sarauta daga shekara ta 1832 zuwa 1865.
Ita Aya diya ce ga Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje,
Ummarun Dallaje yayi sarauta Katsina daga shekara ta 1807 zuwa 1835 Kuma yayanshi guda 4 ne s**ayi sarauta bayanshi.

2. Gudindi Model Primary School Funtua (1937)
Sunan wannan makarata ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Gudindi Wanda yayi sarauta daga shekara ta 1810 zuwa 1817 Kuma shine Sarki na 12 a jerin sarakunan kasar Maska.

3. Idris Girls Model Primary School Funtua (1986)
Sunan wannan makarata ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Idris Sambo Wanda yayi sarauta daga shekara 1968 zuwa ta 1995 shine Sarki na 24 a jerin sarakunan kasar Maska, kuma shine mahaifin Sarkin Maska na yanzu Alh Sambo Idris Sambo da Kuma Hakimin Mairuwa Alh Sani Idris Sambo.

4.Sambo Primary School Funtua (1959)
Sunan wannan makarantar ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Sambo Wanda yake mahaifi ga Sarkin Maska Shehu da Kuma Sarkin Maska Idris Sambo.
Sarkin Maska Sambo yayi sarauta daga shekara ta 1927 zuwa ta 1963 Kuma shine Sarkin Maska na 22

5. Shehu Primary School Funtua (1956)
Sunan wannan makarantar ya samo asali ne daga sunan Sarkin Maska Shehu II Wanda yayi sarauta daga shekara ta 1963 zuwa ta 1968 Kuma shine Sarkin Maska na 23.
Sarkin Maska Shehu ya rike mukamin minista a zamanin Sardauna
Allah ya gafarta masu kuma ya albarkaci zuri'arsu baki daya ameen.

Kotu ta yanke wa Sifeto-Janar na Ƴan Sanda watanni 3 a gidan yariDaga Daily Nigerian HausaWata babbar kotun tarayya da k...
29/11/2022

Kotu ta yanke wa Sifeto-Janar na Ƴan Sanda watanni 3 a gidan yari

Daga Daily Nigerian Hausa

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Talata ta yanke wa Sufeto-Janar, IGP, na ƴan sanda, Usman Baba, zaman gidan yari na tsawon watanni uku, bisa zargin kin bin umarnin hukuncin da wata kotu ta yanke na kin mayar da wani jami’in dan sanda, Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritaya ta ƙarfi da yaji bakin aiki.

Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Okoli, Arinze Egbo, ya shigar, ya kuma gargadi Baba kan rashin bin hukuncin da kotun farko ta yanke a baya.

Mai shari’a Olajuwon ya yi gargadin cewa idan Sufeto-Janar din ya kasa wanke kansa daga laifin ƙin bin umarnin kotu, to za a sake daure shi na tsawon watanni uku a gidan yari.

Mista Okoli, a cikin wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/637/2009, ya kai karar IGP ne a matsayin mai shigar da kara a cikin lamarin.

Mai shigar da karar, wanda ya roki kotun da ta bayar da umurnin a dawo da shi bakin aiki, ya ce majalisar ‘yan sanda wacce a halin yanzu ake kira da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, PSC, ta yi masa ritaya ta dole ba bisa ka’ida ba a shekarar 1992, a lokacin da ya ke rike da mukamin cif sufritenda na yan sanda na jihar Bauchi da dai sauransu.

Ya ce ritayar da ya yi ta dole, a karkashin doka ta 17 na 1984, haramtacciya ce.

Mai shari’a Okorowo, a hukuncin da ya yanke a ranar 21 ga Oktoba, 2011, ya ba da umarnin tilasta wanda ake kara (IGP) da ya aikata wannan umarni k**ar yadda doka ta tanada.

Ya umurci IG da ya bi umarnin hukumar PSC, k**ar yadda ya ke kunshe a cikin wasikar su ta ranar 5 ga Mayu, 2009 (tare da Ref. PSC/CSP/01/11/295A), inda ya umarce shi da ya mayar da Okoli cikin ƴan sandan Najeriya.

Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan NijeriyaDaga Daily NigerianBabban hamshakin attajiri a Afrika, ...
29/11/2022

Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan Nijeriya

Daga Daily Nigerian

Babban hamshakin attajiri a Afrika, Aliko Dangote, na kyautata zaton cewa sabon saka hannun jari na biliyoyin nairori a ɓangaren s**ari zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da ba zai yi kasa da dubu 300 ba a Nijeriya.

Sanarwar da Sashen Sadarwa na Kamfanin Aliko Dangote Group ya fitar ta ruwaito Dangote ɗin na cewa kamfanin na samar da sabbin hanyoyin samun kudade don haka ya fadada ayyukansa a bangaren s**ari.

Dangote, wanda ke magana a wajen bikin bada lambar yabo ta shekarar 2022/2023 da aka yi a Numan, jihar Adamawa, ya ce damar da za ta samu za ta hada da ayyuka kai tsaye da kuma waɗanda ba na kai tsaye ba.

Dangote, wanda shi ne babban mai bayar da agaji a nahiyar Afirka, ya bayyana fatansa cewa dimbin jarin zai samar da ayyukan yi sama da 300,000 ga ƴan Nijeriya.

Ya ce, “Muna zuba jari mai yawa a jihar Adamawa ta hanyar fadada karfin tace s**ari na DSR Numan daga 3000tcd zuwa 6000tcd, 9800tcd, zuwa 15,000tcd.

"DSR zai iya ƙirƙirar ayyuka kusan dubu ɗari uku, kai tsaye da kuma wanda ba na kai tsaye ba, tare da ingantattun tasirin ninkawa kan tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya," in ji shi.

Duk duniya ba wanda ya fi ƴan Nijeriya kai ƙara kotu, Alƙalin Alƙalai ya kokaDaga Daily Nigerian Alkalin Alkalan na Ƙasa...
28/11/2022

Duk duniya ba wanda ya fi ƴan Nijeriya kai ƙara kotu, Alƙalin Alƙalai ya koka

Daga Daily Nigerian

Alkalin Alkalan na Ƙasa, CJN, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya yi ƙorafin cewa ƴan Nijeriya, musamman ƴan siyasa su ne s**a fi kowa kai ƙara kotu, inda hakan ke wahalar da ɓangaren shari'a.

Mai shari’a Ariwoola ya bayyana hakan ne a yau Litinin a Abuja, a wajen taro na musamman na kotun koli da aka gudanar don bikin shiga shekarar shari’a ta 2022/2023 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyi 62 na Nijeriya, SAN.

A cewar CJN, a duk ‘yar rashin jituwa, sai mu garzaya kotu, kuma a duk shari’ar da ba mu samu nasara ba, sai mu garzaya kotun daukaka kara har zuwa Kotun Koli, komai kankantar taƙaddama.

“Hakan ya haifar da cunkoson kararraki da dama da ke gaban Kotun Koli.

"Duk da cewa muna shan s**a daga jama'a game da yawan tuhume-tuhume, amma ba mu da iko a kan shari'o'i da ke zuwa kotu ko kuma ba mu da ikon da za mu iya kaiwa ga kowa da kowa.

"Mun sha maimaita cewa yawancin kararrakin ya k**ata a bar su a kawo karshen su a kotun daukaka kara, amma har yanzu ba a aiwatar da irin wannan tanadin kundin tsarin mulki don haka ba mu da wani laifi."

Ya ce yana da kyau a yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima a dakatar da kararrakin da ake yi a gaban kotun koli kuma ya k**ata a kawo karshen irin wannan kara a kotun daukaka kara.

27/11/2022

Hukumar zaben Nijeriya INEC ta haramta wa yan siyasa kamfe a wuraren ibada.

Yerima mai jiran gado a Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya yi alkawarin bai wa kowanne daga cikin ‘yan kwallon kasar da s*...
26/11/2022

Yerima mai jiran gado a Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya yi alkawarin bai wa kowanne daga cikin ‘yan kwallon kasar da s**a s**a yi nasara a kan 'yan wasan Argentina, kyautar motar alfarma kirar Rolls Royce Phantom.

Yeriman na Saudiyya, ya nuna farin ciki ne da nasarar da kasar ta samu musamman ganin cewa Lionel Messi da kansa na cikin wasan da s**a fafata a ranar Talata.

Kimanin dalar Amirka dubu 460 ne dai kudin kowace motar ta Rolls Royce Phantom yake.
Me kuka ce?
~DW Hausa

Talban Daura, Yusuf Buhari Kenan Tare Da Matarsa, Zahra Nasiru Ado Bayero
25/11/2022

Talban Daura, Yusuf Buhari Kenan Tare Da Matarsa, Zahra Nasiru Ado Bayero

Alfanun sauya fasalin takardun naira na da yawa sosai - CBNBabban Bankin Najeriya na CBN ya ce akwai alfanu sosai game d...
24/11/2022

Alfanun sauya fasalin takardun naira na da yawa sosai - CBN

Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce akwai alfanu sosai game da sauya wa wasu daga cikin takardun naira fasali, waɗanda ya ƙaddamar a yau Laraba.

Cikin jawabin da Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gabatar yayin bikin, ya ce daga cikin alfanun da za a samu har da daƙile yunƙurin buga jabun kuɗi.

"Alfanun da za a samu na sauya fasalin naira na da matuƙar muhimmanci ganin cewa yunƙurin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi ta hanyar mayar da kuɗi zuwa bankuna," in ji shi.

"Kazalika, zai tallafa wajen gyara fasalin kuɗin da kuma samun cikakkun bayanai game da zagayawar kuɗi a tsakanin jama'a.

"Mun yi imanin cewa hakan zai jawo ƙaruwar jama'a cikin harkokin kuɗi da kuma rage amfani da garin kuɗin.

"sauya fasalin zai taimaka wajen yaƙi da rashawa saboda za a ƙara saka wa manyan takardun naira ido waɗanda su kuma za a iya bin sawunsu daga bankuna cikin sauƙi."
~BBC Hausa

Masarautar Katsina ta dakatar da Mak**an Katsina Hakimin BakoriMajalisar masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Mak**...
24/11/2022

Masarautar Katsina ta dakatar da Mak**an Katsina Hakimin Bakori

Majalisar masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Mak**an Katsina Hakimin Bakori Alhaji Sule Idris daga mukaminsa na Hakimin Bakori.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Sarkin Tsaftar Katsina Alhaji Sule Mamman Dee wanda shi ne mataimakin Sakataren masarautar.

Sanarwar ta ce an dakatar da Hakimin daga Larabar nan 23/11/2022 har sai an kammala bincikensa.
~ DCL Hausa

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin takardun naira.Daga BBC HausaGwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sababbin takardu...
23/11/2022

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin takardun naira.

Daga BBC Hausa

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sababbin takardun kuɗin naira da ta sauya wa fasali.

An fitar da takardun kuɗin ne yayin bikin da ke gudana yanzu haka a Fadar Shugaban Najeriya ta A*o Rock Villa a Abuja.

Takardun kuɗin sun ƙunshi N1,000, da N500, da N200.

Gwamna Masari ya fashe da kuka yayin da yake gabatar da kasafin kudin sa na karshe ga majalisar dokokin jihar Katsina.Ka...
22/11/2022

Gwamna Masari ya fashe da kuka yayin da yake gabatar da kasafin kudin sa na karshe ga majalisar dokokin jihar Katsina.

Katsina Post ta samu cewa Gwamnan ya bayyana a gaban majalisar ne tare da rakiyar mataimakin sa da sauran mukarraban gwamnati ranar Talata domin gabatar da kundin kasafin kudin na shekarar 2023.

Kasafin kudin na shekarar 2023 dai ya kai sama da Naira Biliyan 288.

Wannan dai shine kasafin kudin na karshe da Gwamnan ya kai majalisa domin bisa dokar tsarin mulki, zai kammala wa'adin mulkin sa ne a watan Mayu na shekarar 2023 mai zuwa.

Cikin jawabin sa a zauren majalisar, Gwamna Masari ya yabawa majalisar da bangaren Shari'a da ma Sarakunan gargajiya bisa irin hadin kan da suke ba gwamnatin sa tare da rokon su ci gaba da baiwa gwamnatin da zata gaje shi irin sa.
~ Katsina Post

Buhari zai kaddamar da ayyukan hakar man fetur a iyakar Bauchi da GombeDaga BBC HausaA ranar Talata ne ake sa ran shugab...
22/11/2022

Buhari zai kaddamar da ayyukan hakar man fetur a iyakar Bauchi da Gombe

Daga BBC Hausa

A ranar Talata ne ake sa ran shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai kaddamar da ayyukan bunkasa hakar man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.

Kamfanin samar da man fetur na Najeriyar, NNPCL, ya ce shekara biyu da s**a wuce ne aka tabbatar da gano tarin arzikin man fetur mai yawan da za a iya sayarwa a yankin.

Wannan ne karon farko da ake haƙo man fetur a Arewacin Najeriya.

Wakilin BBC da yake can yankin na Kolmani, ya ce bayanai sun nuna cewa akwai karin wasu rijiyoyin da aka kammala aikinsu k**ar wannan a yankin na Bauchi da Gombe, waɗanda za a ci gaba da aikin samar musu da wuraren da za a sarrafa man fetur da dangoginsa, irin sa na farko a arewacin Najeriya, kana akwai wasu da dama da ake aikin haƙo man.

Bugu-da-kari kuma, bayan Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin bunkasa ayyukan hakar man fetur din, za a ci gaba da aikin hako sauran wuraren da aka gano don tantance yawan man fetur da iskar gas din da ke karkashin kasa wanda a za a iya fitar wa tare da sarrafa danyen man fetur din da iskar gas.

Ana sa ran za a gina matatar mai da sauran ayyukan albarkatun man.

Tuni dai al'ummar jihohin Bauchi da Gomben, musamman mazauna yankunan da ake aikin hako man fetur din s**a bayyana farin cikin su da wannan aiki.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa, sun ji dadi da aka kawo wannan aiki yankinsu tare da fatan samun alkhairi mai yawa dama samun ayyukanyi ga mazauna wajen.

Sun ce suna fatan kuma aikin bunkas ahakar man fetur din zai kawo wa yankinsu ci gaba da zaman lafiya mai dorewa.

A shekarar 2016 ne kamfanin mai na Najeriya NNPC, ya kaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin kasar, abin da ya kai ga gano dimbim albarkatun man fetur din a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Neja.

Najeriya dai ita ce kasar da tafi kowacce fitar da danyen mai a kasuwannin duniya a nahiyar Afrika, sai dai kuma takan kashe makudan kudaden wajen shigo da tataccen man da ake amfani da shi a cikin kasar saboda lalacewar matatun man kasar.

A lokuta da dama gwamnatoci daban-daban sun sha lasar takobin gyara matatun man kasar domin wadatar da ita da man take bukata, amma daga baya sai maganar ta bi shanun sarki.

Amma a yanzu rahotanni an ambato gwamnati na cewa gano dimbin man da aka gano a arewacin kasar zai kara yawan man da kasar ke hakowa a kullum tare da samar da wurin da za a rika tace shi.

Daya daga cikin rijiyoyin mai na farko da aka gano a arewacin Najeriya kenan a kauyen Barambu da ke karamar hukumar Alka...
21/11/2022

Daya daga cikin rijiyoyin mai na farko da aka gano a arewacin Najeriya kenan a kauyen Barambu da ke karamar hukumar Alkaleri. Rijiyar mai lamba KR2 ita ce ta biyu cikin uku da aka kammala aikinsu.
~ BBC Hausa

21/11/2022
21/11/2022
Halima Atete za ta shiga daga ciki 👰‍Tauraruar Kannywood Halima Yusuf Atete tare da angonta Mohammed Mohammed Kala wadan...
20/11/2022

Halima Atete za ta shiga daga ciki 👰‍

Tauraruar Kannywood Halima Yusuf Atete tare da angonta Mohammed Mohammed Kala wadanda za a daura aurensu ranar Asabar 26 ga watan Nuwamban 2022 a Maiduguri.

Allah Ya sanya alheri 🤲

Innalillahi waa inna ilaihi raji'uun!Ibrahim Karama Dutsen-Reme, Allah Ya gafarta maka Ya sa ka huta. AminKafin rasuwar ...
20/11/2022

Innalillahi waa inna ilaihi raji'uun!
Ibrahim Karama Dutsen-Reme, Allah Ya gafarta maka Ya sa ka huta. Amin

Kafin rasuwar sa shine PHC Director Danja LG, Katsina State.

Janaza anjima da yamma a ƙofar gidansa 4:30pm.
~ Comr Umar Iliyasu Danbaba

Abubuwan Da Qatar Ta Tanadarwa Musulunchi A Wannan WorldCup Ɗin ...1. A duk biranen da za'a buga wasan, Qatar ta rubuta ...
20/11/2022

Abubuwan Da Qatar Ta Tanadarwa Musulunchi A Wannan WorldCup Ɗin ...

1. A duk biranen da za'a buga wasan, Qatar ta rubuta Hadisan Annabi (saw) a alluna ta yadda idan kazo wuchewa sai ka karanta.

2. Qatar ta hana shan ko siyar da giya a duk stadiums ɗin da za'a yi wasan.

3. A bango na ɗakunan hotels ma duk an rurrubuta hadisai da koyarwar musulunchi

4. An ɗauki ladanai masu zaƙin murya, sannan an kawo speakers har stadium saboda idan lokachin Sallah yayi za'aji ƙiran sallah mai daɗi har a stadium.

5. Qatar ta tanadi wasu mutane/malamai kimanin 2000 waɗanda zasuyi da'awa na musuluntar da mutane, an tanada musu mobile cars da tanti tanti guda 20 na kai mutane masallachi da koya musu sallah da sauransu.

6. Qatar ta tanadi wajajen sallah da alwala a daf da dukkannin stadiums ɗin da za'ayi wasan domin masu kallo su samu saukin gabatar da sallah akan lokachi.

Daga Basheer Muhammad LwNgr

INNALILLAHI WAINNA ILAIHIR RAJIUN Matar nan da mijinta ya kulleta a daki me suna sadiya ta rasu.Sedai an tabbatar mijin ...
20/11/2022

INNALILLAHI WAINNA ILAIHIR RAJIUN

Matar nan da mijinta ya kulleta a daki me suna sadiya ta rasu.

Sedai an tabbatar mijin nata ya shiga hannun jami'an tsaro

Allah yajikan ta Allah yasa hakan yazama sanadin shigar ta aljanna madaukakiya

~ ATP Hausa News

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun tabbatarwa da Freedom Radio cafke mawaƙin nan Mista 442 da Daraktansa Ola of Kano bisa z...
19/11/2022

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun tabbatarwa da Freedom Radio cafke mawaƙin nan Mista 442 da Daraktansa Ola of Kano bisa zargin samunsu da takardun shaidar zama ƴan ƙasar na bogi.
Ƙarin bayani na tafe.
~Freedom Radio Kano

Address

Dutsen-Reme Katsina Road
Bakori

Telephone

+2347032910220

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dutsen-Reme Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dutsen-Reme Post:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Bakori

Show All