ZAKI DAILY News HAUSA

ZAKI DAILY News HAUSA ZAKI DAILY News HAUSA jarida ce da zatana kawo muku labaran Kasa Najeriya

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojojin Faransa sun fara ficewa daga ƙasar Chadi bayan gwamnatin N'Djamena ta katse huldar soji da ƙasar.A...
27/12/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Sojojin Faransa sun fara ficewa daga ƙasar Chadi bayan gwamnatin N'Djamena ta katse huldar soji da ƙasar.

A watan da ya gabata dai ne hukumomin kasar Chadi s**a katse hulda tsakaninta da kasar Faransa, wanda hakan ya jawo tuni jiragen yakin Faransa s**a bar ƙasar.

Zuwa yanzu kuma ɗaruruwan sojojin ƙasar Faransa ne s**a tattare kayansu, tare da cifewa daga Chadi zuwa Faransa, kamar yadda RIF Hausa ta tabbatar. Me zaku ce ?

A ranar crisimeti aka haifi shugaban jam'iyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yau ya cika shekaru 75 a duniya.  ...
25/12/2024

A ranar crisimeti aka haifi shugaban jam'iyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yau ya cika shekaru 75 a duniya.

masu karatu wane fata kuke masa?

25/12/2024

Tsira Aminci Daraja Martaba cikar Matsayi Girmamawar Allah su kara tabbata ga wanda Allah ya yaba iyakar yabo
MUHAMMAD RASULULLAH

Da ɗumi ɗumi: kotu ta bada umarnin ci gaba da tsare yahaya bello har sai 10 ga watan decemberMe zaku ce?
28/11/2024

Da ɗumi ɗumi: kotu ta bada umarnin ci gaba da tsare yahaya bello har sai 10 ga watan december

Me zaku ce?

Shugaba Tinubu ya tafi kasar Fransa, a yayin da mataimakinsa Kashim Shettima kuma ya tafi kasar Côte devoreMe zaku ce?
28/11/2024

Shugaba Tinubu ya tafi kasar Fransa, a yayin da mataimakinsa Kashim Shettima kuma ya tafi kasar Côte devore

Me zaku ce?

‘Yan majalisar dokokin Nijariya na jam‘iyyun adawa sun kai wa madugun adawar kasar Atiku Abubakar na PDP ziyara ta girma...
28/11/2024

‘Yan majalisar dokokin Nijariya na jam‘iyyun adawa sun kai wa madugun adawar kasar Atiku Abubakar na PDP ziyara ta girmamawa domin taya shi murnar cika shekaru 78 a duniya

Malam Ba Kwana Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro Biyo Bayan Ruťùnțumawa Kwankwaso Àšhar Da Ya Yi A Wani Bidiyo Saboda Zargin...
28/11/2024

Malam Ba Kwana Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro Biyo Bayan Ruťùnțumawa Kwankwaso Àšhar Da Ya Yi A Wani Bidiyo Saboda Zargin Ya Dora Musu Shugabar Karamar Hukuma Mace A Yankin Tudun Wada Dake Kano

Tsagaita wuta a lebanon za ta buɗe ƙofar ta gaza- Amurka
28/11/2024

Tsagaita wuta a lebanon za ta buɗe ƙofar ta gaza- Amurka

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta liverpool tasha  real madrid 2-0 a gasar kofin zakarun turai
28/11/2024

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta liverpool tasha real madrid 2-0 a gasar kofin zakarun turai

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamnatin tarayya ta soke kwangilar gyaran hanyar  Sashi na I  Daga Hannun kamfanin Julius Berger Construc...
05/11/2024

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamnatin tarayya ta soke kwangilar gyaran hanyar Sashi na I Daga Hannun kamfanin Julius Berger Construction.

Me zaku ce akan hakan ?

05/11/2024

Allah ya Farantawa Duk Zuciyar dake Ƙaunar
𝘼𝙣𝙣𝙖𝙗𝙞 𝙈𝙪𝙝𝙖𝙢𝙢𝙖𝙙 𝙎.𝘼.𝙒 💙💖
Barka da wannan lokaci

Hutunan Sarkin Dauɗar unguwar Kurna Babban Layi, a  yayin da ya fita zagayen Takutaha a birnin Kano.
23/09/2024

Hutunan Sarkin Dauɗar unguwar Kurna Babban Layi, a yayin da ya fita zagayen Takutaha a birnin Kano.

Jadawalin Gudummawar Da Jihohi Da Daidaikun Mutane Suuka Baiwa Al'ummar Maiduguri Sakamakon Ambaliyar Ruwa Zuwa Yanzu1. ...
23/09/2024

Jadawalin Gudummawar Da Jihohi Da Daidaikun Mutane Suuka Baiwa Al'ummar Maiduguri Sakamakon Ambaliyar Ruwa Zuwa Yanzu

1. Gwamnatin Bauchi = Naira milyan 250
2.Gwamnatin Kebbi = Naira milyan 200
3. Gwamnatin Adamawa =Naira milyan 50
4. Gwamnatin Yobe = Naira milyan 100
5. Gwamnatin Kano =Naira milyan 100
6. Gwamnatin Gombe =Naira milyan 100
7. Gwamnatin Taraba =Naira milyan 100
8. Gwamnatin Kaduna = Naira milyan 100
9. Gwamnatin Jigawa = Naira milyan 250

ƘUNGIYOYI DA DAIDAIKUN MUTANE

1. Alhaji Aliko Dangote =Naira bilyan 2
2. Alhaji Aminu Dantata =Naira bilyan 1.5
3. HE Atiku Abubakar =Naira 100m
4. HE Peter Obi =N50m
5. North East Dev Commission =N3b
6. Sanatocin Nijeriya = Nnaira milyan 54.5
7. 'Yan majalisun tarayya = Naira milyan 100
8. People’s Democratic Party (PDP) =N25m
9. 'Yan majalisun jihar Borno =N60m
10. Former Senate President Ahmed Lawan =N50m
11. Hon Zainab Gimba =N25m
12. Ibrahim Abba Umar =N50m
13. Sumaila Satumari = N10m
14. Hon Mallam Gana Kareto =N10m
15. Northern Senators Forum =N10m
16. Senator Barau Jibril =N10m
17. Hon Moh’d Abubakar Maifata =N50m
18. Southern Borno =N200m
19. Hon Zakariya Dikwa =N10m
20. Al-Amanah Aid =N1m
21. Hon Mohammed Imam =N50m
22. HE Maina Ma’aji Lawan = N10m
23. HE Ali Modu Sheriff = 100m
24. Hon Dr Ali Bukar Dalori = N50m
25. Sen MT Monguno = N50m
26. Sen Kaka Shehu Lawan = N50m
27. Hon Aliyu Betara = N100B
28. Hon Abdulkadir Rahis = N25B
29. Hon Ibrahim Abuna = N25B
30. Hon Usman Zannah = N10m
31. Hon Engr Bukar Talba = 10m
32. Hon Yerima Lawan Kareto = N2m
33. Abdussalam Kachallah = N100m
34. Awari Usman Alkali = N20m
35. Muhammadu Buhari =N20m

GUDUMMAWAR DA BA KUDI BA

1. Kungiyar Bunkasa Arewa Maso Gabas= buhu 200 ta shinkafa, makaronin katan dubu 20,000 da kuma galan dubu goma na man gyada

2. Sumal Food Group, Ibadan = biredi guda dubu 50,000 da kuma katan din biskit guda 5,000

3. Gwamnatin jihar Nasarawa = mota biyuta shinkafa, mota biyu ta taliya da makaroni da kuma ta siga guda biyu

4. General Bub

YANZU YANZU: Kasashe Hudu ne kawai a Africa Dake siyar da man fetur a farashi me rahusa fiye da Nijeriya.Libya na ci gab...
23/09/2024

YANZU YANZU: Kasashe Hudu ne kawai a Africa Dake siyar da man fetur a farashi me rahusa fiye da Nijeriya.

Libya na ci gaba da bayar da man fetur mafi arha a Afirka, inda farashin man fetur octane-95 ya tsaya a kan Dinar Libya 0.15 a kowace lita, kwatankwacin kusan $0.032 ko N52 a ranar 16 ga Satumba, 2024.

Wannan dai na zuwa ne a wani rahoto da kamfanin Global Petrol Prices ya fitar, wani dandali dake bin diddigin farashin man fetur a kasashe daban-daban.

Idan aka kwatanta, farashin man fetur a Masar, Aljeriya, da Angola ya tsaya kan dala $0.279, dala 0.342, da kuma dala 0.351 kan kowace lita.

DA ƊUMI-ƊUMI: Monday Okpebholo ya lashe zaɓen jihar Edo, inda ya samu ƙuri'u 291,667 inda ɗan takarar jam'iyyar PDP Asue...
23/09/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Monday Okpebholo ya lashe zaɓen jihar Edo, inda ya samu ƙuri'u 291,667 inda ɗan takarar jam'iyyar PDP Asue Ighodalo yake biye masa da kuri'u 247,274

17/09/2024

2:42am
💥Breaking News 💥

Only Muslim can complete Muhammad rasulullah🥰

DA DUMI-DUMI: Kwamitin Majalisar Wakilai kan Rundunar Sojin Ruwa ya sha alwashin binciki tsarewar da aka yi wa Seaman Ab...
17/09/2024

DA DUMI-DUMI: Kwamitin Majalisar Wakilai kan Rundunar Sojin Ruwa ya sha alwashin binciki tsarewar da aka yi wa Seaman Abbas Haruna ba bisa ka'ida ba har na kusan shekaru shida, bisa umarnin wani Birgediya Janar MS Adamu, tare da yin alkawarin tabbatar da cewa an sanya duk wadanda ke da hannu a cikin wannan sagar. fuskanci cikakken sakamakon ayyukansu.

Halin da Seaman Abbas ya fuskanta, kamar yadda mai dakinsa Hussaina Iliyasu ta bayyana a shirin ‘Berekete’ na gidan Talabijin na Human Rights, ya fara ne a shekarar 2018 a lokacin da aka ba shi aikin hadin gwiwa a Sarti Baruwa jihar Taraba, inda zai yi aiki karkashin rundunar. na Birgediya MS Adamu, amma an samu rashin fahimtar juna a tsakanin ‘yan biyun, lamarin da ya kai ga tsare shi a wani yanayi na rashin jin dadi na tsawon shekaru da dama ba tare da shari’ar da ta dace ba kamar yadda dokar soja ta 2004 ta Tarayyar Najeriya ta tanada.

Wannan cin mutuncin da aka yi wa sojojin ruwa a kan wata ‘yar rashin fahimta da babban hafsan sojan nasa ya yi, ya sanya jama’a da dama a dakin taro s**a zubar da hawaye yayin da matar ke ba da labarin irin wahalar da mijinta ya sha.

Tsananin Rashin Imani da Birgediya Janar MS Adamu ya nuna wa na karkashinsa kan wani dan karamin lamari, ya jawo kakkausar s**a daga miliyoyin ’yan Najeriya masu hankali da s**a ji labarin.

Labari mai ban tausayi na Seaman Abbas Haruna, wanda aka sanyawa kafar yada labarai ta ‘Berekete’ ya sa kwamitin majalisar wakilai kan harkokin ruwa ya shiga cikin lamarin da nufin bayyana gaskiya da kuma kare mutuncin sojojin mu da hakkin kowane mutum a karkashinsa. dokokin kasar. Bugu da kari, bukatuwar kuma a kamo duk jami'an da abin ya shafa tare da bibiyar matakan soja don tabbatar da duk wanda ke da hannu a cikin babban take hakkin Seaman Abbas an gurfanar da shi da gaske.

Sa hannu:
Rt Hon. Yusuf Adamu Gagdi, PhD OON.
Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa.

DA DUMI-DUMI: Motocin da za a yi jigilar man fetur na Ɗangote sun iso Najeriya inda ake sa ran nan da awanni 48 za a far...
04/09/2024

DA DUMI-DUMI: Motocin da za a yi jigilar man fetur na Ɗangote sun iso Najeriya inda ake sa ran nan da awanni 48 za a fara siyarwa a jahohin Najeriya.

Ana sa ran hakan zai rage farashin man fetur a Najeriya kuma fetur ɗin zai kasance mai kyau ba gurɓatacce ba kamar yadda Ɗangote ya shaidawa ƴan jaridu jiya a Ikko.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ZAKI DAILY News HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category