Yantacciya

Yantacciya Shafin an samar dashine Domin Zakulo labaran Gaskiya daga sako da lungun Duniya

12/07/2024

WANI KARATU!

ba kowa bane ya lura da cewa wasan kokawan turai wanda ake yin sa daga kai sai dan kamfai, wrestling, ko kuma wasan dambe boxing da ake yi da gajerun wanduna idan ka zama na daya a duniya wai belt za'a baka! Duka wandunan da dan kamfan da gajeren wandon babu wanda yake amfani da belt! Ka taba lura da haka?

Wasan damben hausa wanda sai an nade maka hannu domin ka ji dadin kai naushi hannun a daure yake tamau amma bayan ka zama zakara a qasar hausa sai a baka takobi, takobin da ka ciwo da, daurarren hanu ta ina zaka iya sarrafa shi?

ABIN LURA!

shi wawantar da al'umma tare da hana musu yin nagartaccen tunani na ajiye komai a muhallin sa bai taqaita iya yan' Nigeria ba! Duniya ne baki daya,

Amma mafi munin ciki shine na malam bahaushe wanda shi an daure maka hannu tamau sannan an baka takobi,

WATO AN DAURE MAKA TUNANIN KA TAMAU SANNAN AN BAKA YAN'CI,

Yadda alqalan wasannin can dana yi misali dasu suke jan ragamar duk wani motsinka haka anan ma malamai suke jagorantar daure maka tunanin naka ka tamau! Su hana ka yancin tunani,

Idan ka kwance tunanin ka daga wancan mugun daurin tare da kwace shi daga hannun miyagun malamai zaka gane cewa banajin cikin nasarar da hulk hogan ko warriors da su hit man s**a samu a kokawar wrestling, ko kuma Muhammad Ali da mike tyson irin su deontey da Anthony joshua a fagen boxing a wannan zamanin s**a samu akwai wata gudunmawar malamin addini ko guda daya cikin ta!

Idan kana son zama me nasara kuma me yan'ci ka wai ka yaqi zalinci.

© Shehu Abumajid Abu Bakara.

DAN AREWA DA WAWAN TUNANI 2Zanga Zanga wani aikine da ya kunshi bayyana mastayar wani mutum ko gungun mutane akan wani a...
09/04/2024

DAN AREWA DA WAWAN TUNANI 2

Zanga Zanga wani aikine da ya kunshi bayyana mastayar wani mutum ko gungun mutane akan wani abu a bayyane ta hanayar Furtawa ko nunawa domin jama'a su shaida.

Irin wannan ta faru a ranar da aka bayyana Addinin Musulunci a sarai, inda Sahabbai s**ayi Jerin Gwano Daga gidan Arqam bin Abul Arqam (R.A)
inda musulmai suke Yin taron Addini a asirce, zuwa jika dakin Ka'aba mai Girma .
suna Shelanta wadannan Kalmomi

"Allah Ɗayane Kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Alihi Manzonsa ne"

Ana jifansu ana Dukansu , haka s**aci gaba da wannan Jerin Gwano Har Jikin Dakin Ka'aba mai Daraja.

Halasci Ko Haramcin Zanga Zanga a Musulunci ya dogara ne da sakon da Zanga Zangar take isarwa.
Sakon Halas ne ko Haram, shine zai Fassara Zanga Zangar a Shari'ance.

Domin A addinin Musulunci komai Asalinsa Halas ne , har sai an sami Haramcin aikatawa.

Shin Zang-Zanga tana da Amfani kuwa wajen kwatar kai daga Kangin Bauta ?

Eh tabbas Zanga Zanga tana da Amfani kwarai da gaske, domin itace kadai hanaya ta kwanciyar hankali wacce Al'umma suke iya bayyana matsayarsu akan wani abu ba tare da sun cutar da kowa ba.

Wannan Tsarin na Bayyana matsayar Al'umma itace ta Bambance Bawa da 'Yantacce, itace ta banabance wayayye da Kidahumi, itace ta Bambance Wanda yasan ciwon kansa da wanda bai sani ba.

Zanga Zanga ta samar da Mafita ga Al'ummomi masu yawa, akan wasu tsare-tsaren da aka dankara masu wanda yake tauye masu hakki.

Misali shine Zanga Zangar da kungiyoyin gwagwarmayar Africa ta Kudu s**ayi ta Allah wadai da nuna wariyar launin fata a Afrika ta kudu.
Wanda aka fara tun 1912 har 1992 Ya zama jigo ga gwagwarmayar neman 'Yancin Africa ta Kudu, kuma sila A samun 'Yancin kansu.

Zanga Zangar da Akayi a Nigeria ma Lokacin mulkin Jonathan akan kara kudin man fetur tayi tasiri, domin kuwa tasa dole ya janye kudirin karin kuɗin man a wancan lokacin.

Shin Zanga Zanga a Nigeria akan wani abu da yake faruwa a Duniya Tana da wani Tasiri a wancan muhallin ?

Eh tabbas duk daga inda kayi Zanga Zaga a Duniya domin nuna goyon baya ga wasu al'ummar da ake zalunta to yana taimakawa waɗan da aka zalunta ta ta hanyoyi masu yawa, daga ciki akwai karfafa Gwiwa cewa Ba'a manta dasu b akwai waɗan da s**a tare dasu a neman 'Yancin da suke , basu kaɗai bane.

Waɗan da suke zaluncin suna na muradunsu a kowacce kasa a duniya, dan haka duk ƙasar da al'ummar ta duk fito s**ayi Allah wadai da Zaluncin da akewa raunana a wani waje to Ita kasar da take aikata wancan Zaluncin tana da wakili a kasar da kake Kuma sakon ka yaje gareshi , kuma sun tabbatar baka tare dasu a Zaluncin da suke, kuma zaka taimakawa waɗan da ake zalunta Daduk abinda kake iyawa, Hakan Barazana ce Babba Ga Azzalumi.
Domin Munga yadda Zanga Zangar da akayi a Libiya Yankin Bengazi ta shafi Amurka kai tsaye, har ta ki ga rufe Ofishin Jakadanci na Amurka a Libya ɗin.
Kuma mmunga yadda zanga Zanga tasa Amurka da Isara'ila sake Mugayen manufofin su masu yawa a Iraq, Jordan da sauran ƙasashen da s**a yadda da yin wani yunkuri domin kawo sauyi.

Shin Idan Aka samu Nasarar Kwace wa Al'umma'Yancin yin Zanga Zanga mai zai iya biyu baya ?

Idan Al'umma Ta yadda aka kwace mata 'Yancin yin Zanga Zanga to an maida wannan Al'ummar Kamar bayi, domin za'ayi ta korasu k**ar dabbobi babu Mai kiwo, kuma basu da wata hanya ta nuna rashin amincewarsu akan wani tsarin da aka dankara masu.
Shiyasa Azzaluman masu mulki s**a dukufa wajen ganin sun Raba Al'umma da wannan 'Yancin da Addini ya basu kuma Tsarin Mulkin Demokradiyya ya basu.
domin ta Hakane kadai cikakkiyar bautarwa zai yiwu akan wannan Al'umma.

Rushin Gwagwarmaya da kwatar 'Yanci daga Azzaluman masu mulki shine kadai zai bawa duk wani mai son ya rayu cikin 'Yancin Addini da zamantakewa, Mafita da yake nema domin rayuwa cikin Aminci.

~Ibn Abubakar Alhausawy

DAN AREWA DA WAWAN TUNANI (1)Ya ishi mutum Jarrabawa Allah yayi shi a  Nigeria kuma Arewacin Nigeria, domin kuwa In Alla...
06/04/2024

DAN AREWA DA WAWAN TUNANI (1)

Ya ishi mutum Jarrabawa Allah yayi shi a Nigeria kuma Arewacin Nigeria, domin kuwa In Allah ya Azurta mutum da Fahimtar abubuwan da suke faruwa a kewaye dashi gwargwadon hali, to kullum zai dinga kwana yana tashi cikin damuwa da halin da al'umma take ciki.

To saide ita kuma Al'ummar mafi yawanta basa lura , kuma basa gane hakikar halin da suke ciki, kuma suna gaba da duk mai kokarin Nuna musu wannan halin da suke ciki domin a fara kokarin samo hanyoyin maganin matsalar.
To ya zakayi da wanda Baima yadda yana cikin matsala ba b***e ya fara tunanin hanyar Da zaibi domin Maganin ta ?

Idan ka duba a kewaye dakai sai kaga wani mutum wanda Malaman sa s**a hana masa 'Yancin yin tambaya, sannan s**a hana masa 'Yancin yin bincike, Saide abin da s**a fada masa kadai shin ma'auninsa, idan kace dashi, Ya k**ata ya dinga Tambaya sannan ya dinga bincike domin nemawa kansa amsosin wasu daga matsalolin da s**a dameshi , sai yace dakai , ai tunda akace dashi karya yayi tambaya kuma kar yayi bincike, to Ya Yarda, kuma matsayar da kenan , To irin wannan mutum Ya zakayi dashi ?

A wanan Al'ummar tamu ce zaka waiga kusa dakai sai kaga wanda wanda Aka baiwa wani hakkinsa ta hannun wani , shi wanda Aka baiwa hakkin nasa ya bashi ya cinye masa hakkin nasa, Saika bashi shawara kace, kaga tunda an baiwa wane Hakkin ka kuma ya cinye kana iya bin kadin hakkin ka dalilin da yasa ma akayi kotu da jami'an tsaro kenan , Sai Shi kuma yace dakai , ai Ba rabo bane domin Allah ne bai nufi kudin su iso gareni ba, idan kuma kace dashi Ai Allah ya riga ya bashi wanine ya cinye masa, Sai yace dakai Baka da Tauhidi, saboda kaki yadda da kaddara.
to ya zakayi da irin wanan mutum wanda bisan Dalilin da Yasa Allah zai yi Hisabi shine saboda wasu bayi suna cinye hakkin wasu bayin. ?

A wannan yanayin na kunci da damuwa da wasu mutane s**a jefa al'umma a ciki da gangan idan kayiwa mutane da dama bayanin haka basa ganewa sai s**e ai Allah yaso ya gansu cikin wannan Kangin Bauta kunci da damuwa.
Idan kace dasu ai Tunda Allah ya ajiye Arziki na Zinariya, Azurfa, kasar noma , man Fetur, Iskar gas, Kogonni, Hasken rana da sauransu, Ai ya baku arziki, sai yace dakai ai A'a ai hakkin amfani da wannan Azikin masu mulki ne kadai suke dashi , idan ka tambaye shi to Meyasa masu Mulkin basa amfani da arzikin wajen inganta rayuwar al'ummar kasar?
sai yace dakai wai Allah ne bi nufiasu mulkin da suyi Adalci ba, Ya yadda ya jingina Mummuna ga Mahalicci akan ya jingina ga Mai Mulkin da yake zaluntar sa, shin ya zakayi da irin wadannan mutanen ?

A wannan Kasa tamune Azzaluman masu mulki s**a gano Amfani da malamai wajen Kamfen na siyasa shi yafi komai sauki, Ga Araha ga Biyan buƙata, Sannan Ga kariya ta musamman a duniya, su tafka sata da gangan mai gurgunta tattalin arziki, Daga sun ɗan sanya Malamai na Fada kadan , shikenan, sai a jinginawa Allah kuncin da Satar Azzalumin mai mulki ta Kawa talakawa, shinen Sai ace da talaka ai Tauhidene jure wannan kuncin rayuwa kuma akwai lada mai girma.
haka nan talaka zai yarda kuma yayi biyayya da nufin samun lada, bayan Malam ya dade da karbar nasa ladan daga cikin hakkin talakawa da aka sace.
shin ya zakayi ka Fahimtar da irin wadannan mutanen cewa Ba Allah ya dora masu Kunci da wahalar rayuwa ba, hakan ya faru ne saboda wasu sun sace Arzikin da ya k**ata ayi amfani dashi wajen saukaka wa rayuwarsu?

Jarrabawace ta Kasancewa a cikin wannan Al'umma wacce aka haɗu masu mulki da Malaman Fada aka daure mata Kwakwalwar ta , aka hana ta tunani mai kyau akan mokomarta , aka hanata duk wani yunkuri ko motsin da zai kai ga 'Yantar da kanta.
Ana cutar da ita ta hanayar amfani da imanin ta addininta da riko da Malaman ta shugabanninta.

Shin Zang-Zanga tana da Amfani kuwa wajen kwatar kai daga Kangin Bauta ?

Shin Zanga Zanga a Nigeria akan wani abu da yake faruwa a Duniya Tana da wani Tasiri a wancan muhallin ?

Shin Idan Aka samu Nasarar Kwace wa Al'umma'Yancin yin Zanga Zanga mai zai iya biyu baya ?

Mu hadu a Rubutu na Gaba.

~Ibn Abubakar Alhausawy

KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (2)A Rubutunmu na Farko Munyi bayanin yadda masu Bautar da Al'umma suke karanta...
27/02/2024

KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (2)

A Rubutunmu na Farko Munyi bayanin yadda masu Bautar da Al'umma suke karantar ta ciki da bai, kafin su bautar da ita, ta yadda Bazasu sami Turjiya ba daga waɗan da suke Bautarwar, inda wasu da ake bautarwar ma su kansu Basusan ana bautar dasu ba.

Matakin Da Masu mulkin mallaka suke bi domin tabbatuwar mulkinsu.

To bayan Masu mulkin mallaka sun karanci Al'ummar da suke yiwa mulkin mallaka to akwai hanyoyin da suke bi domin Tabbatar da wannan mulkin nasu, daga karantar Al'ummar da Sukayi, tunda sunsan Karfin Al'ummar da kuma Raunin ta.

Hanyoyin da 'Yan Mulkin Mallaka suke bi wajen Sarrafa Al'ummar Nigeria, Africa dama duk inda suke mulkin mallaka a duniya.

Tsarin Mulki: Soja Ko Farar Hulla ko Sarauta.
Wajen Tsarin Mulki suna samar da tsarin mulki ne da bazai taɓa cin karo da Muradunsu na mulkin mallaka ba, koda kuwa su waɗan da ake mulka suna tsammanin suna da 'yanci , to duk abinda zasuyi bazai wuce iyakar da 'Yan Mulkin Mallaka s**a shata musu ba, inde kuwa basu tsallaka wannan iyaka ba, to tsarin mulkin bazai amfani al'ummar ba.

Zabar Shugaba:
Wajen Zabar Shugaba da zai jagoranci wannan tsarin da 'Yan Mulkin Mallaka s**a yiwa sitamfi wanda bazai amfani Al'ummar kasar ba, suna tabbatarwa Shugaban Zaiyi biyayya ne ga Tsarin da aka bashi (Na mulkin mallaka) Kuma bazai ketare iyakar da aka shimfida ba.
domin tabbatar da biyayyar Dan takarar wannan kujera ta mulki to dole yaje can kasashen 'Yan Mulkin Mallaka domin amsa tambayoyin da Zasuyi masa, wanda daga nan zasu gane Zaiyi biyayya ko A'a.
Shiyasa Lokacin Zabe ko nadin sarauta zakuga ana rige rigen zuwa kasashen waje tarukan tattaunawa, To
idan Mai Neman Mulkin Zaiyi biyayya to sai a bashi damar takara, idan yaci mulki su saka shi cikin rabon arzikin da zasu deba daga kasarsa, Sannan su bashi kariya shi da iyalansa daga tuhumar cin hanci da rashawa, Sai yayi Komai ba komai, Anan duniya, idan bazai yi biyayya ba kuma to wajen zaben fidda gwanima dakyar ya wuce inka ya wuce to bazai wuce Babban Zabe ba, Inko duka 'Yan takarar sun yarda da sharadinsu to sai su zabi wanda Zaifi yin biyayya su bashi mulki.
inko bayan yahau kan mulki ya nemi bijirewa, to sun shirya yadda zasu kau da wanna mai mulkin, ta hanayar amfani da turakun tsarin mulkinsu da yake jagoranta.
Irin wadannan turakun Mulkin sun hada da Soja, Majalisa, da sauransu.

Tsaron Kasa:
Kasashe'Yan Mulkin Mallaka basa taba bari tsaron kasashen da suke mulka yabar hannunsu.
sune suke Bada training ga Askarawa na kasa, suke sayar mata da mak**ai, suke kula da cibiyoyin tsaron kasar da sunan masu bada shawara, suke Bada umarni wajen ayyukan tsaro na wanan kasa, dan haka duk yadda za'ayi Kasar tsaronta yana tafin hannunsu.
Idan sunso sai su samar da rashin tsaro domin biyan wasu bukatunsu kuma babu wanda ya isa ya samar da tsaron.
Duk sirrin Kasa yana hannunsu. dan haka dolen masu rike da mulkin kasar suyi musu biyayya sau da kafa.
Abin takaicin ma Duk training din da zasu bawa sojan wannan kasa to marar amfani zasu bashi, haka duk makamin da zasu bashi to shima marar amfani zasu bashi domin karma yayi tunanin kalubalantar su wata rana.

Tattalin Arziki:
Kasashe 'Yan mukin mallaka, Sune suke Tasarrufi da tattalin arziki na ƙasashen da suke mulka, sune suke da Bankin Bada Lamuni na Duniya Wato (IMF) sune suke da Bankin Duniya da yake tsarawa dukkan sauran Bankunan ƙasashe yadda Zasuyi aikinsu wato (World Bank), sune suke da cibiyar hada-hadar kudade ta duniya wato (World Trade Center) sune suke da Hanyar musayar kudi a tsakanin Bankunan duniya wato (SWIFT) sune suke da Kudin da dole idan zakayi cinikayya ta kasuwanci sai dashi wato(Dollar) Koda kasuwanci Kasa zatayi to Saide ta siyar ko ta sayo kaya ta amfani da kuɗin kasashe'Yan Mulkin Mallaka.
dade sauransu.
Shiyasa sai talaka ya rasa Meye Dalilin da yasa kudin kasarsa kullum yake rage daraja.
duk wadannan cibiyoyin kayan aikine na tabbatar da Mulkin Mallaka ga kasashen da ake yiwa mulkin mallaka.
Dolen kasa tayi biyayya ga dokoki da Muradun 'Yan Mulkin Mallaka, inkuma taki su saka mata takunkumi (su hanata cinikayya a duniya)

Sanna Har yau dinnan Kasashen da Ba'ayi masu mulkin mallaka to basu da yawa ko Goma dakyar su kai.

Nan Munyi takaitaccen Bayani ne akan abubuwa da s**a shafi kasa kai tsaye , wanda su masu mulki sun san dasu, kuma sunayin biyayya ga Iyayen Gidansu 'yan Mulkin Mallaka, to amma Meyasa Koda talakawa sun gane anayin mukin kasar sune ba domin su talakawa su sami saukin Rayuwa ba, kuma basu da wata dama tacewa ayi ko a'a a al'amuran Tafiyar da kasarsu , Amma duk da hakan talakawa basa iyayin komai ?
Ko Meyasa kaso mafi yawa na al'ummu sunsan mulkin mallaka ake musu amma basa iya yunkurin kawo Gyara ?

Insha Allahu zamu amsa wadannan tambayoyi a cikin Rubutun mu na gaba , da Zaiyi magana akan yadda 'Yan Mulkin Mallaka suke sarrafa Al'ummar Gari Domin su hanasu kokarin kawo sauyi.

~Ibn Abubakar Alhausawy

Sojan Sama na Amurka Aaron Bushnell Kirista  Ɗan Shekaru 24 Ya cillawa kansa wuta a gaban ofishin Jakadanci na Isra'ila ...
26/02/2024

Sojan Sama na Amurka Aaron Bushnell Kirista Ɗan Shekaru 24 Ya cillawa kansa wuta a gaban ofishin Jakadanci na Isra'ila a birnin Washington DC na Amurka.

Sojan yayi Hakane a yunkurin sa na farkar da Duniya irin girman Zalunci da Amurka da Isra'ila suke aikatawa akan Al'ummar Falsɗinawa a Gaza da yamma da kogin Jodan.

Kafin Ya kunna wutar a Jikinsa Saida yayi bayani inda yake cewa

"Ni Bazan kasance mai taimakawa Kisan Kiyashin da Akewa Falsɗinawa ba, dan haka zanyi Wani abu mai tsananin hatsari domin Farkar da duniya dan haka dole Falastinwa su sami 'yanci. "

Bayan ya cillawa kansa wuta a Gaban Ofishin Jakadanci na Isra'ila, yaci Gaba Da maimaita kalmar Free Palestine har Saida wutar taci karfinsa 😭 yazama muryarsa bata fita anajin me yake faɗa, amma yana tsaye yana daga hannu yana kara tabbatar da matsayarsa har Saida ya fadi kasa.

Duk Wannan abun yayi shine yayin da wayarsada ya ajiye ta akan ma'ajiyin waya take daukar video na abinda yake faruwa.

Hoton da yake Kasa Hoton Aaron Bushnell ne.

Menene ra'ayin ku akan irin wannan yunkuri na Aaron domin Farkar da Duniya Halin da Al'ummar Falasɗinawa suke ciki ?

WASU MALAMAN DA KARYA KADAI SUKE GA ZASU RIKE MABIYANSU.To idan ba da karya kadai sukega zasu iya rike mabiyansu ba Ya a...
26/02/2024

WASU MALAMAN DA KARYA KADAI SUKE GA ZASU RIKE MABIYANSU.

To idan ba da karya kadai sukega zasu iya rike mabiyansu ba Ya abinda ya faru kowa ya shaida , harma kukayi walima da farin ciki da faruwar sa, kukayi nade-naden sunaye ga waɗan da s**a aikata shi, kukayi ta isgili da yaɗa hotunan faruwarsa sannan ku dawo kuce wai bai faru ba ?

Kune fa kuka ce Buhari da Elrufa'i da Buratai da Sukayi wannan kisan kiyashin Aikin Allah suke , harma kuka raɗawa Burtai suna (Ayatullahi Burtai) sannan kuke Tsokala da sunan sa kuna cewa waɗan da kuka tabbatar ya aikatawa ta'addanci Ga Buratai nan , domin ku muzanta musu Har kun manta ?

Kune fa kukace Lefin Zagin Sahabbai yasa akayi kisan kiyashin Zariya, kuma wadan da s**a aikata ta'addancin sunyi dai-dai, kuma har kukayi walima da bukukuwa, harda waɗan da s**ayi sallar Godewa Allah da kisan da Gwamnatin Buhari tayi, sannan kukace ko Buhari baiyi maku komai ba , tunda ya (K*ashe 'Yan Shi'a) To ya gama yi maku komai , Har kun manta Kenan?

Kune fa Kuke yawo da hotunan Malam Zakzaky An dauko shi a Wilbaro jikinsa duk jini, idonsa yana zubar jini, kuna yaɗa hoton kuna Cewa (Wali mai Baro) har kun manta ne ?

Kune fa kuka dauko hoton sa da likitoci s**a dauka bayan Sunje duba Lafiyarsa , wanda a cikin hoton kowa yana iya kallon Idon Malam Zakzaky guda daya a mace baya aiki, kuka dinga yaɗa hoton kuna cewa Yazama mai Ido daya kuna kiransa da (Dujal mai ido ɗaya) saboda isgili da shakiyanci irin naku , Yanzu duk wannan abinda kukayi kun manta kenan ?

Kune fa Kuke cewa Kunyi ajalin Shia'a ba ita ba kayanta, domin duk Gomnonin Shia'a na Kaduna , Kano , Da Yobe Buhari ya K*ashe su , kuna murna kuna fada , dan haka Shia'a tazo karshe Yanzu kuma kuzo kuce ba'ayi kisan ba ? Anya har kuna da saurin mantuwa haka?

Kune fa kukace kar abar Zakzaky ya fita neman lafiya, idan aka barshi ya fita Guduwa Zaiyi bazai dawo ba, saboda tsoro, shin har kun manta?

To abin mamakin duk da tabbatarwa da kukayi , harda murna da kukayi , da isgilanci da kukayi da goyon baya da kuka nuna ta duk hanayar da kuke iyawa , Saboda kunga Allah ya kunyata ku Allah ya bashi Lafiya ba domin kunso ba, Yanzu saiku dawo kuna ƙaryata kanku da sabbin karyayyaki saboda ku katange miskinan almajiranku daga fahimtar Ikon Allah da yake kunshe a cikin tseratar da bawansa Malam Zakzaky dakuma Warkar dashi.

A cikin wannan rubutun Na makala hotuna , domin bawa Ɗan Rijiyar lemo amsa, dakuma miskinan almajiransa. Cewa Duniyafa Bazata manta ba Ta'addancin Buhari a Zaria, da rawar da kuka taka, yanzu ba Zamanin Shekaru 1400 da s**a wuce bane, da zaku aikata ta'addanci ko sauya tarihi domin boye Ta'addancin.

~Ibn Abubakar Alhausawy

KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (1)Shinfida da Gabatarwa:Kamar yadda na rubuta a taken rubutu kafin mu sami 'ya...
17/02/2024

KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (1)

Shinfida da Gabatarwa:

Kamar yadda na rubuta a taken rubutu kafin mu sami 'yanci sai mun nemi 'yanci , to haka wanan Magana take daga nan har birnin Sin.

Ba'a taba yin wata al'umma ba da ta sami 'yanci batare da aiki Tukuru domin samun 'yanci ba a Tarihin Duniya, kuma ba za'a fara daga Nigeria ba.

Duk wata Daula ko wata ƙasa da muke kallo ta zama abin kwatance a yau, ta fannin ci gaban tattalin arziki, tsaro da rayuwa mai inganci, to wasune s**ayi aiki domin samar da wanna yanayin, da yanzu wasu suke mora kuma suke Girmamawa tare da sanya Albarka ga gwarazan da s**a samar da wanna yanayin.

Shi 'Yanci Nemansa ake a wajen wanda ya tauye ma al'umma shi, sannan a kwace shi ta yadda daga wanan lokacin to wannan mai tauye 'yanci din ya rabu da ikon da yake dashi na Bautarwa ga al'umma sannan dole ya tabbatar bashi da ta cewa a cikin al'amurran da s**a shafi wannan al'umma, kuma wannan al'umma bata bukatar izninsa wajen yin abinda ya dace ga Al'ummar ta, a takaice de Gudanar da wannnan al'umma ya dawo hannunta Dari Bisa Dari.

Tarkon Masu Bautarwa Ga waɗan da Ake Bautarwa:

Koda mutum kiwo yake to dole ne yasan irin dabbar da yake kiwo, dakuma halayyar ta a maban-bantan yanayi, Ya takeyi ida tana jin yunwa, Yaya takeyi idan tana jin ƙishirwa, wanne irin abinci tafi so, ya takeyi idan bata da Lafiya, ya takeyi idan ta fusata, wanne irin kololuwar mataki take dauka idan tayi Fushi?
Shin Halbi take ? ko Tunkuyi take ? shin Cizo take ? ko kuma kuka takeyi kawai ?

Kuma Dole wannan Mai kiwo yayi tanadin Yadda zai shawo kanta kowanne irin yanayi take ciki, ta hanyar amfani da dabaru, tsoratarwa, Yaudara, Da duk wata hanya mai yiwuwa, Shiyasa Masu kiwon suke samun damar sarrafa abin kiwonsu cikin sauki, koda kuwa sun nufi yanka abin da suke kiwon ne to turjiyar da zasu samu kadance kuma baze hana yanka abin kiwon ba, kuma sauran Dabbobin Bazasu iyayin komai ba. Domin Shi mai kiwon yasan Halayyar abin da yake kiwo ciki da bai a kowanne yanayi.

Dan Adam Kamar Abin kiwo ne Ga Masu Bautar dashi:

Kamar yadda mukayi bayani a sama yadda Masu kiwo Sukeyi na dabba da Allah bai bata Daraja , Ta Hankali k**ar dan Adam ba, da yadda Masu kiwon suke ɓata lokaci wajen karantar Halayyar abin kiwonsu, to inaga Masu Sarrafa Dan adam domin su bautar dashi ?

To masu bautar da dan adam da suke kwace masa dukkan 'Yanci na rayuwa da zamantakewa, suma suna karantar Al'ummar da zasu bautar ne tun kafin su mamaye ta, Dole su karanci Dabi'a ta wannnan Al'umma, Shin wannnan Al'umma Tana da tsarin gudanarwa ne , Yayi tsarin shugabancin su yake, Idan akazo musu da bakon abu yaya Sukeyi, Idan sunajin Yunwa yaya Sukeyi, idan an kwace musu Wani abu nasu mai girma a wajensu yaya Sukeyi, Maganar wa sukeji, Idan Sunje Kololuwar yin fushi da tunzura iya me suke iya yi, Shin suna da juriya da Hakurin gwagwarmayar kwato abinda aka kwace musu ko de kawai bari sukeyi ya kwatu?
dade sauransu.
Sannan Masu Mulkin Mallaka suna tanadin ya Zasuyi su samar da maganin waɗan nan yanayi na al'ummar sannan kuma su Bautar da ita, ba tare ma ita Al'ummar tasan bautar da ita ake ba, b***e tayi Yunkurin Neman Hakkinta.

To waɗan da suke bautar da al'ummar Nigeria dama Nahiyar Afirka baki ɗaya, suna Bautar da Al'ummar ne ta hanyar amfani da duk wata hanya ta sarrafawa da suke da ita kuma har gobe A Kangin Bauta Nahiyar Afirka take, Saide bautarwar da ake yiwa wani wajen tafi ta wani wajen rashin Imani.

Zamu ci Gaba Da wannan rubutu Insha Allahu, a fita ta 2.

©️Ibn Abubakar Alhausawy

KISAN KIYASHIN BUHARI A ZARIYA: BAMU MANTA BA, BAMU YAFE BA.Yau shekaru Takwas kenan cur, a irin wannan ranar ta 12 ga 1...
12/12/2023

KISAN KIYASHIN BUHARI A ZARIYA: BAMU MANTA BA, BAMU YAFE BA.

Yau shekaru Takwas kenan cur, a irin wannan ranar ta 12 ga 12, 2015. Sojojin inada-kisa, Sojojinda ke kashe Mata da Yara a Ƙasar Hausa da sunan Ta'addanci, s**a fito da maitarsu ƙarara, s**a aukar da Kisan Kiyashi mafi muni a tarihin Kasar nan, da rana tsaka a Zariya.

Wasu sun ɗauka wai bisa Haɗari abun ya faru, sam ba haka bane, tsararren Shiri ne, wanda aka yi shekaru ana tsarawa, kuma ake neman yadda za a yi ya faru, ba tare da wata matsala ba. Shi ne s**a laɓe da Ƙaryar tare hanya domin su aiwatar, karyarda har yanzu za ka ji wasu marasa kan gado daga cikin 'Yan Jaridu da sauran mutanen gari na yaɗawa, duk da an je kotun hukuma ta yi hukunci, ta ce ƙarya ne, ba a ma tare hanya ba, b***e hayaniya, b***e dukan Ƙirjin Soja, ta ce ƙarya ce kawai aka tsara, aka zartar, don haka a biya Diyyah.

Amma har yanzu za ka ji wasu gauga'u da wasu makirai na cika baki suna cewa wai an tare hanya, ko hanyar Uwasu aka tare oho. An zo an yi wasa da Hankalin Al'umma domin a hanasu gane inda aka dosa, a hanasu tausayawa, su kuma ba su ankara ba. Kotun ƙasa ta ankarar da su,cewa ba a yi ba, amma har yau miyagun 'yan Jarida da Miyagun Malamai na masu wahayin Sheɗan.

To yanzu shi kisan Kiyashin Tudun Mauludi (Tudun Biri) da ya faru a satin da ya wuce, hanyar Uwarwa aka tare..? Iye..? Su suna kisan ne da manufa, amma kafin su yi za su samu wata ƙarya su fake da ita, domin a yita riritawa, kafin a gano gaskiya sai an dade, sai an sha wahala.

Yanzu a Tudun Mauludi ai da farko musawa s**a yi, da s**a ga 'Yan Uwa da Mutanen Kogo,da sauran masu Hankali sun dage ne sunata surutai a social media ne, sannan s**a ce wai kuskure ne. Su so s**a yi a yi shiru, sai abun ya wuce haka na. Kuma wallahi talnahi da mun yi shiru da yanzu sai dai guna guni, hatta malamanda ke cika baki yanzu daga dukkan ɓangarori, suna yi ne domin sun ga Arhar abun, domin sun ga hukuma ta yadda itace ta yi.

Wallahi ,summa talnahi, da hukuma ta ja daga k**ar yadda ta ja daga a kisrn Zariya, wallahi da mafi yawan waɗannan Lusaran Malaman muƙis za su yi. Ba muna rena abukda s**a yi daga baya bane, amma k**ata yayi tun ranar farko, tun awar farko, su zabura su mike, amma wasu ko tari basu yi ba sai bayan kwana biyu, wasu Uku. Wato sai da s**a ga hanyar babu ƙaya sannnan s**a ratsa.

Idan da za a yi Tambaya, a ce shin wai yaushe ne aka aukar da Kisan Kiyashi a Tudun Mauludi, wace rana ce aka tsara wannan abun, ? Amsa itace tun ranar 12 ga 12 2015. Aiwatarwa ne kawai ta faru a satin da ya wuce, amma tun a zariya aka zartar, aka buga sitamfi. Duk wani kisan Kiyashi da Kidnnaping da Banditry da ake yi a Arewa ta Yamma, ba a samu Lasisin farashi da tsananta shi ba, sai bayan da aka aukar kisan kiyashin Zariya.

Da s**a kashe raunana a tsakiyar rana, kuma a tsakiyar Birni, s**a ga an masu shiru, s**a ga wasu na murna, s**a ga wasu na zugawa, s**a ga wasu na walima, sai s**a ce, ashe Hausa Hankali bai isheta ba, ashe za mu iya aiwatar da Plan dinmu ba tare da tsrngwama ba.

To tun sannan farashin kashe Talaka a wannan yankin yayi arha. Tun sannan aka kashe 'yan mauludi a Tudun Biri. Dama itama ranar ranar 1 ce ga watan Maulidi, kuma an taru a zariya domin ɗaga tutar Maulidi.

Ba za a bar kisan babu Dalili a Arewa ba, har sai ranar da muka san ciwon kanmu, har sai ranar da muka san cewa da Hankali ake hukunci, da shi ake kallon Lamurra idan sun faru ba da Son rai ko son kai ba. Har sai mun san cewa Zalunci a kan Ɗaya, zalunci ne a kan kowa.

Kuma kowa ya sani har yanzu waɗanda aka kashe a zariya suna bin wannan Al'umma bashi. Bashin shi ne, su fito su yi tofin Allah tsine da wannan Aika-aika k**ar yadda da yawansu s**a giyi baya, k**ar yadda da yawansu s**a yi shiru a lokacin, kuma su nemi gafarar 'Yan Harka Islamiyyah da Jagiron Harka Islamiyyah. Wannan hakki ne a kan wuyan duk wani Dan kasar nan.

Idan ba haka ba, to Allah dai ba Azzalumi bane. Idan ka yiwa wani Izgili, to zai kawo ranar da wasu za su.maka kaima. Kuma wallahi matukar Al'umma bata barranta da bannar da aka yi a zariya ba, to wallahi ba za ta taɓa ganin daidai ba. Jinin nan zai yita bibiyarta har sai ya leƙa gidan kowa. Wannan ba mummunar fata bace.haka sunnar Allah take.

Shamsudeen Hassan Zuru
12/12/2023

03/12/2023

— 🇮🇱/🇾🇪 SABON LABARI: Haramtacciyar Kasar Isra'ila, ta aike da jiragen ruwan Yaki Kusa da Kasar Yaman, Bayan da Sojojin Yemen Masu taimakawa Falasɗinawa s**a kai hari kan Jiragen ruwa na Isra'ila da suke kai mata kayayyakin yakin da take Falsɗinawa, - Asalin Labarin daga Jaridar Al -Arabiya

03/12/2023

⚡️🇾🇪 A GAGGAUCE: Kamfanin Jigilar Jiragen ruwa na Haramtacciyar Kasar Isra'ila "Tsim"
Ya fitar da sanarwar: '' Sun Karkata Jigilar Jiragen ruwan Haramtacciyar Kasar Isra'ila daga shiga tekun Maliya, biyo bayan kona jiragen ruwan Isra'ilan da Sojojin Yemen s**ayi a 3/12/2023''

Yau 3/12/2023 Dakarun Yemen Sun Hari Jiragen ruwa Na Haramtacciyar Kasar Isra'ila da mak**ai masu linzami da jiragen sam...
03/12/2023

Yau 3/12/2023 Dakarun Yemen Sun Hari Jiragen ruwa Na Haramtacciyar Kasar Isra'ila da mak**ai masu linzami da jiragen sama marasa matuka, a Kogin Maliya.

ABUN DA ƊAURE KAI, KUMA DA TAKAICI SOSAI... 😭A daidai lokacin da Koriya ta Arewa ke ayyana za ta taimakawa Gazawa da mak...
02/11/2023

ABUN DA ƊAURE KAI, KUMA DA TAKAICI SOSAI... 😭

A daidai lokacin da Koriya ta Arewa ke ayyana za ta taimakawa Gazawa da mak**ai, kuma har shugabansu ya bada Umurinin haka, a lokacin ne aka k**a Ƙasar Dubai tana aikawa Isra'ila da tallafi... 😭

A daidai lokacin da Russia take bayyanawa Duniya a Majalisar Dunkin Duniya cewa batun cewar da ake Isra'ila na haqqin Kare kanta ƙarya ne, domin ita 'Yar mamaya ce, a lokacin ne, Kasar Jordan ke buɗe Sararin Samaniyarta ga Jiragen.' Yan mamaya domin a Shigar musu da Mak**ai.

A daidai lokacin da Khazastan da Ajerbijan ke bawa Isra'ila duk abunda take buƙata na Man Fetur da Gas, ta hannun Kasar Turkiyya, a daidai lokacin ne Kasar Egypt take yiwa Falasdinawa rowar RUWAN SHA, kuma ta ƙasa shigar musu da magani, wai sai da Iznin Isra'ila da Amerika.. Bayan Egypt Itace Runduna mafi karfi a duk Fadin Afrika, kuma tana cikin mafi karfi a duk Fadin Duniya... 😭

A daidai lokacin da Kasar Yemen ke antayawa 'Yan Mamaya ruwan mizayil da Drone, a lokacin ne Saudiyya take basu warning cewa kada su kara yin amfani da Sararin Samaniyarta wajen kai hare harensu marasa kan gado inji ta, a lokacin ne ta yadda Amurika ta kara girke air defence systems a Cikin kasarta, wai domin a hana Mak**an Yemen kaiwa cikin Kasar Isra'ila.

Yanzu bayyana cewa, Amerika ce Uwar Isra'ila ila, Ƙasashen Musulmi kuma su ne masu reno.

Egypt, da Jordan da Saudiyya sun zamar mata Katanga, su kuma Turkiyya, Azarbejan, Khazastan da Dubai suna bata duk abunda take bukata na Mak**ashi da Abinci da Kuɗi.

Ƙasashen Latin Amerika na katse huldarsu da Isra'ila, su kuma kasashen Larabawa na neman Kulawa.

Kasashen Kirista da Maguzawa;Russia, China da North Korea nan Ƙoƙarin tallafa masu da mak**ai, su kuma kasashen Larabawa da wasu na musulmi na kokarin tallafawa Isra'ila.

Abun da rudar da kai, ga Musulmi amma babu Musulunci. Babu 'Yan Adamtaka. Kai babu hatta hatta Ƙabilancin ya gushe... Sun cika cikkuna da Haram sun kasa aikata Halal.

© Shamsudeen Hassan Zuru

29/01/2023

YANZU YANZU CBN YA KARA WA'ADIN KWANA GOMA (10) KAFIN A DENA KARBAR TSOFFIN TAKARDUN KUDI.

28/01/2023

Address

Amfanuwa Duniya/lahira
Abuja

Telephone

+2348062100586

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yantacciya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Yantacciya:

Videos

Share