26/03/2024
Mai girma Abba Kabir Yusuf wannan case din fa tabbas ko mahaukaci yasan akwai abinda bai dace ba a ciki, in kuma babu abinda bai dace ba, to akwai rashin imani tare da danne hakkin Dan Adam, idan shima babu, maiya kawo batun hana beli tunda babu cikakkiyar shaida?, in duk rashin fahimtar shari'a ne yasa haka, menene abinda yasa aketa jan case din tsawon shekaru?.
Mai Girma Gwamna AKY, Alhamdulillah, nasani ba daya ba biyu ba, inayin rubutu akan abubuwa mabanbanta, kuma ana kawo maka kana gani, wasu kuma makusantanka suna gani, har su aika min sakonka, wani lokaci muyi magana ta waya akan abinda muka wallafa, to cikin ikon Allah wannan ma sakon gareka ne, tare da yakinin zaije maka, don Allah kasa a dau mataki, a matsayinka na mai tausayi da sanin yakamata, wanda ina da yakinin sanin da nayi maka ta wani fannin yasa nake wannan magana.
Mai Girma AKY yakamata a matsayinka na Uban Kanawa, wanda Allah ya dora alhakin kula dasu a kanka, ayiwa wannan magana duba na tsanaki, a duba lamarin marayun nan, tunda dai Allah yasa kaima ubansu ne, bai kamata ace suna kukan rashin gata ba.
Domin indai abinda wannan yar baiwar Allah ta fada haka yake gaskiya ne, yakamata a dauki mummunan mataki mai Girma Gwamna, don wannan bata sunan jihar Kano ne, jawowa Kano abin kunya ne da koma bayan yancin Dan Adam.
Daukar mataki wajibi ne akan wanda s**a zalunci wannan baiwar Allah da yayanta, kuma magana ma ta gaskiya maiya kawo maganar saita Amsa?, kunga kenan izza da jin cewa na isa, ina da karfin da zan wulakantaku, inko ba haka bane meya hana karbar uzuri bada hakuri?, shin yaron da ubansa ma'asumai ne basa laifi?, in sunayin laifi to muna rokon Ubangiji suma kada ya karbi kowanne irin tuba nasu har saiya hukuntasu akan abinda s**ai masa na laifi, Indai haka zuciyarsu take ta kafirawan farko.
Sannan a karshe don Allah Ina rokon freedom tasa a baiyana mana sunan wancan mai baki da kunun, da aketa sakaya sunansa,
Source ABDULLAHI AMDAZ
Abba Kabir Yusuf