Jaridar Hasken Rana

  • Home
  • Jaridar Hasken Rana

Jaridar Hasken Rana Online Media News

An binne wannan saurayin Malam Ali Dogo a shekarar 1935, yau shekaru 90 da kwanciyarsa a Kabari.An haife shi 1908, ya ra...
07/11/2025

An binne wannan saurayin Malam Ali Dogo a shekarar 1935, yau shekaru 90 da kwanciyarsa a Kabari.

An haife shi 1908, ya rasu 1935 yayi shekaru 27 a duniya. Malam Ali Dogo yana kwance a Kabari yana jiran tashin Qiyama, ya shafe shekaru 90 yana kwance yana jira, kuma da sauran tafiya.

Malam kar ka bari rayuwar shekaru 30, 40 ko 50 tasa ka gagara shirya ma kwanciyar shekaru dubu a kasa. Mu shafawa kanmu ruwa, akwai aiki a gaban mu wallahi.

Allah Yajikansa, Allah Yasa mucika da kyau da Imani.

Muhammad Bello Sulaiman. ✍

Da Dumi-DumiDaga karshe, hukumar zaben k**aru ta ce Paul Biya ne ya lashe zaben shugaban kasa na K**aru
27/10/2025

Da Dumi-Dumi

Daga karshe, hukumar zaben k**aru ta ce Paul Biya ne ya lashe zaben shugaban kasa na K**aru

Sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, Ya Fara Aiki A Hukumance Yau A Babba...
23/10/2025

Sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, Ya Fara Aiki A Hukumance Yau A Babban Ofishin Hukumar Da ke Abuja

Da Dumi DumiMai Wushirya da 'Yar Guda sun je Asibiti yin gwajin jini, domin shirye-shiryen Aurensu.Wanne fata za ku yi m...
22/10/2025

Da Dumi Dumi

Mai Wushirya da 'Yar Guda sun je Asibiti yin gwajin jini, domin shirye-shiryen Aurensu.

Wanne fata za ku yi musu?

YANZU-YANZU: Jami’an tsaro sun fatattaki dan gwagwarmaya Omoyele Sowore tare da tawagarsa da tear gas yayin da suke guda...
20/10/2025

YANZU-YANZU: Jami’an tsaro sun fatattaki dan gwagwarmaya Omoyele Sowore tare da tawagarsa da tear gas yayin da suke gudanar da zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu, inda suke cewa “Free Nnamdi Kanu!

Rikici ya ɓarge tsakanin Sanata Nwoko da matarsa ƴar fim, Regina Daniels har ya zarge ta da shan miyagun ƙwayoyiSanata N...
19/10/2025

Rikici ya ɓarge tsakanin Sanata Nwoko da matarsa ƴar fim, Regina Daniels har ya zarge ta da shan miyagun ƙwayoyi

Sanata Ned Nwoko ya zargi matarsa, fitacciyar jarumar masana'antar fim ta Nollywood, Regina Daniels, da shaye-shaye ciki har da barasa, yana mai cewa hakan ne tushen rikicin da ke addabar aurensu.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi, sanatan mai wakiltar Delta-ta-Arewa ya bayyana cewa Regina na fama da matsalar shan miyagun kwayoyi wadda ya jawo ta zama mafaɗaciya kuma maras kunya a gare shi.

Nwoko ya ce ya nemi ta shiga cibiyar gyaran halin masu shaye-shaye a Abuja ko ƙasashen waje amma ta ƙi, inda ya zarge ta da guduwa wani wajen da bai sani ba don ta ci gaba da shaye-shaye.

Ya kuma zargi wasu mutane biyu da suna Sammy da Ann da kawo mata kwayoyi.

Sanatan ya ƙara da cewa har ta kai ga Regina ta doki ma’aikata uku na gidan sa kwanaki biyu da s**a gabata, sannan ta lalata motoci da tagogi, inda ya ce a baya wannan ba halaiyar ta ba ce sai da ta fara shaye-shaye.

Sai dai a makon da ya gabata, Regina ta wallafa bidiyo a intanet ta na kuka, ta na zargin cewa ta na fama da cin zarafi a hannun mijinta.

A cikin bidiyon, ta ce, “Ba zan jure tashin hankalin ba, ya yi yawa.”

Lamarin ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda ɗan uwanta, Sammy West, ya fito ya zargi sanatan da dukan 'yar uwarsa, yana mai barazanar daukar mataki.

Auren Ned Nwoko da Regina Daniels, wanda ya jawo cece-kuce saboda bambancin shekaru tsakaninsu, ya sake jawo hankalin jama’a bayan wannan sabuwar takaddama.

Hukumar Sufuri Ta Jihar Gombe Ta K**a Wani Yaro Da Ya Ƙuduri Tafiya Abuja Shi Kaɗai, A Tashar Gombe Line Dake Jiha Hukum...
17/10/2025

Hukumar Sufuri Ta Jihar Gombe Ta K**a Wani Yaro Da Ya Ƙuduri Tafiya Abuja Shi Kaɗai, A Tashar Gombe Line Dake Jiha

Hukumar sufuri ta Gombe State Transport Services (Gombe Line) ta k**a wani yaro da ya bayyana sunansa da Muhsin, wanda ya zo a matsayin ɗan kai, yana ƙoƙarin yin tafiya zuwa Abuja shi kaɗai. Yaron ya bayyana cewa sunan mahaifinsa Ukasha, wanda shi makaniki ne a Abuja, yayin da sunan mahaifiyarsa Fatima ne, daga unguwar Nayinawa.

A cewar hukumar, yaron ya ce yana karatu a makarantar Nasara Primary School, kuma bai bayyana dalilin da yasa ya ke son tafiya ba tare da rakiyar kowa ba. Hukumar Gombe Line ta ce tana rike da yaron a halin yanzu, tana kuma neman wanda ya san shi ko iyayensa da su hanzarta zuwa ofishinsu.

Daraktan hukumar, Dr. Sani Sabo, ya bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da hakan ke faruwa ba. Ya ce a cikin watanni tara da s**a gabata, sun samu irin wannan matsala har sau 95, inda s**a mayar da yara gida tare da haɗin gwiwar rundunar ƴan sanda, Hukumar Kare Haƙƙin Yara (NAPTIP), da Ma’aikatar Kula da Mata.

Ya kuma ja hankalin iyaye da su ƙara kulawa da 'ya'yansu, musamman wajen lura da inda suke da kuma irin shirin da suke yi, domin kare su daga fadawa cikin haɗurra ko matsaloli.

- Gombawa

Matawalle Ya Tabbatar Da Ingancin Tsaro Bayan Wata Fashewa Da Ta Faru A Kamfanin DICON Na KadunaMinistan kasa a ma'aikat...
22/09/2025

Matawalle Ya Tabbatar Da Ingancin Tsaro Bayan Wata Fashewa Da Ta Faru A Kamfanin DICON Na Kaduna

Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Muhammad Matawalle, a ranar Lahadi ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa kamfanin kera mak**ai na kasa DICON yana nan cikin tsaro da aminci kuma yana aiki yadda ya k**ata duk da fashewar da ta faru a masana’antar a Kaduna.

Matawalle, wanda ya kai ziyara wurin a ranar Asabar, ya ce lamarin yana “cikin cikakken iko da tsari tun bayan fashewar,” tare da rokon jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke yawo da ba su da tushe bare mak**a kan abin da ya faru.

Wata sanarwa daga mai taimaka masa a harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ta bayyana cewa Ministan ya samu bayani daga Darakta Janar na kamfanin DICON, Manjo Janar B.I. Alaya, da kuma Daraktan da ke kula da kere-kere, Air Commodore E. Benson.

A yayin duba wurin, Matawalle ya tabbatar cewa fashewar ta takaita ne a cikin wani dan tsuki da ke dauke mak**an da s**a rigaya s**a lalace ko kuma wa'adin aiki da su ya kare da tuni tawagar kwararru ta shawo kan lamarin cikin gaggawa.

“Babu wata ko da tagar window da ta samu matsala a yayin da lamarin ya faru,” in ji Ministan, ya ƙara da cewa gine-ginen masana’antar, ɗakunan ajiya, rijiyar adana dizal da al’ummomin da ke kewaye ba su sami wani lahani ba.

Ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da kare lafiya da tsaron ma’aikata, tare da shan alwashin cewa abin da ya faru zai haifar da ƙara tsaurara matakan tsaro bisa tsarin ƙa’idodin duniya.

A halin yanzu, an kafa kwamitin bincike don gano musabbabin fashewar.

Matan Shugabannin Kananan Hukumomin Adamawa Sun Isa Turkiyya Don Horo Kan JagoranciWata tawaga ta musamman daga Jihar Ad...
22/09/2025

Matan Shugabannin Kananan Hukumomin Adamawa Sun Isa Turkiyya Don Horo Kan Jagoranci

Wata tawaga ta musamman daga Jihar Adamawa, wacce ta ƙunshi matan shugabannin kananan hukumomi na 21, ta sauka a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar wani shirin horo na mako guda.

Shirin, wanda aka tsara musamman don ƙarfafa jagoranci, gogewa da ci gaban al’umma, na daga cikin shirye-shiryen ƙara wa shugabanni mata basira wajen gudanar da muhimman ayyuka a matakin ƙananan hukumomi.

Rahotanni sun bayyana cewa horon zai ba su damar koyon sabbin dabarun gudanarwa, haɗin kai da yadda za su inganta ayyukan raya ƙasa a mazabunsu.

A cewar wani jami’i daga tawagar, wannan damar za ta taimaka wajen ƙarfafa mata a siyasa da shugabanci, tare da bada gudummawa wajen ɗaukaka jihar Adamawa da Najeriya baki ɗaya.

Hoto: Bitrus Ishaya SSA Media To the First Lady Adamawa State.

An k**a Boka da ya ke sayen kwaroron roba da aka yi amfani da su daga ƴan mata masu zaman kansuAn k**a wani boka a jihar...
07/09/2025

An k**a Boka da ya ke sayen kwaroron roba da aka yi amfani da su daga ƴan mata masu zaman kansu

An k**a wani boka a jihar Anambra bayan da ya amsa cewa yana karɓar kwaroron roba da aka yi amfani da su daga wajen ‘yan mata masu zaman kansu domin shirya tsafi.

Wanda ake zargin, mai suna Anagbo Emeka daga garin Umugbo a karamar hukumar Ayamelum, matasan ne s**a k**a shi a unguwar Echara, Awka North.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Dr. Uche Nworah ya nuna lokacin da Emeka ya amsa laifinsa a fili.

Ya ce: “Na yi yarjejeniya da ita ta sayar min da kwaroron roba da aka yi amfani da su. Ta kawo min, amma daga baya ta kai rahotona. Wannan shi ne kuskuren da na yi,” in ji shi a cikin bidiyon.

A cewarsa, ya kulla yarjejeniya da wata karuwa da ta rika kawo masa kwaroron roba daga gidajen karuwai. Amma daga baya ta fasa alkawarin, ta tona asirin sirrin da s**a ɓoye.

Emeka ya kuma bayyana cewa waɗannan kwaroron roba na da matuƙar amfani wajen harkokin tsafi da yake yi.

Ya ce: “Ina amfani da kwaroron roba wajen yin tsafi don sihiri, husuma, rikicin filaye, har ma da shari’ar ‘yansanda.”

Ƴansanda a Kano sun k**a mutane 9  bayan rikicin da ya faru kan zargin kisan kai a GarkoRundunar ’Yansanda ta Jihar Kano...
06/09/2025

Ƴansanda a Kano sun k**a mutane 9 bayan rikicin da ya faru kan zargin kisan kai a Garko

Rundunar ’Yansanda ta Jihar Kano ta ce ta k**a mutane tara da ake zargi da hannu a tashin hankali da ya faru a karamar hukumar Garko bayan wani lamari na kisan kai.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Satumba, 2025, lokacin da jami’an 'yansandan, shiyyar Wudil su ka k**a wasu mutane uku da ake zargi da kisan kai, sannan aka kai su caji-ofis na Garko domin bincike.

Sai dai a ranar 5 ga Satumba, jama’a dauke da sanduna da duwatsu s**a farmaki ofishin, suna zanga-zangar mutuwar wanda aka kashe, tare da kokarin kashe wadanda ake tsare da su.

Harin ya jawo konewar motar sintirin ’yansanda, lalata motoci uku na Hisbah da na karamar hukumar Garko, da kuma lalata tagogin ginin ofishin ’yansanda.

Jami’an ’yan sanda guda uku sun jikkata, inda aka garzaya da su asibitin Wudil kuma suna samun sauki.

A lokacin hargitsin, wata tayar da aka kunna ta fashe ta bugi wani daga cikin masu tada zaune tsaye, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa, yayin da wasu uku s**a jikkata.

Kwamishinan ’Yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gaggauta tura jami’ai tare da shiga tattaunawa da shugabannin al’umma, abin da ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya da natsuwa a yankin.

Rundunar ta gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, saboda hakan na iya haifar da tada hankalin jama’a da karya doka.

CP Bakori ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da adalci. Ya kuma bukaci jama’a su kasance cikin natsuwa, su ci gaba da hadin kai da jami’an tsaro, tare da gujewa duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke sauran da ake zargi da hannu a wannan hari.

~Daily Nigerian Hausa

Hotunan bikin Maulud 1447 AH a garin Gombe.
06/09/2025

Hotunan bikin Maulud 1447 AH a garin Gombe.

Address

Wuse 2 Abuja

Telephone

+2348189217438

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Hasken Rana posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share