![](https://img4.medioq.com/077/456/117901430774566.jpg)
27/01/2022
Ko Ka Taba Hawa Mota Daya Da Jerin Irin Wadannan Mutane Yayin Doguwar Tafiya?
1. MASU BARCI: Wadannan ana fara tafiya za su bige da barci, wasu ma harda zabga munshari.
2. MASU BAKIN AKU: Wadannan mota na fara tafiya za su fara hira iri-iri, har a je inda za a je ba za su gaji da surutu ba har sai kowa ya kosa da su.
3. MAJIYA KIDA: Wadannan mota na tasho za su saka kida a kunnensu, su toshe kunne suna jin sauti har a je inda aka nufa.
4. ACICI: Wadannan sun fiye ciye ciye. Ana tsayawa a tasha ko junction za su fara sayan gyada, kantu, lemo, tsire, cincin da sauransu. Haka za suyi ta tauna har su isa inda s**a nufa.
5. MASU TSAWATARWA: Su kuma wadannan hankalinsu na kan direba, da zarar sun ga gudunsa ya yi yawa za ka ji suna cewa " direba ka yi a hankali fa! Ba mu da wani ran a gida"
6. MASU CINYE GURIN ( MUSAMMAN MATA): Gurin mutum biyu za su cinye, idan kuwa kai rashin sa'a s**a saka a tsakiya sai an tausaya maka.
7. DA U FATAKEN MOTA (BARAYI): Su kuwa wadannan ba ta ka suke ba, ta kayanka suke. Yawanci tun kafin a shiga mota sun gama dana tarkon wanda za su lalube, ana shiga kuma sai kiyayewar Allah.
8. MASU WA'AZI: Su kuwa wadannan ana fara tafiya za su fara wa'azi suna jawo hankalin abokan tafiya a koma ga Allah.
9. SHIRU SHIRU (KAMILALLU): Ai wadannan sun fi dadin sha'ani a harkar tafiya malam. Za su yi wa makocinsu sallama, daga nan in s**a zauna jar a je inda a aka nufa ko uffan ba za su ce ba.
RIGIMAMMU: Su kuwa wadannan ba sa so a zauna lafiya, za su ja magana ko su yi wa wani ba'a, kana tanka musu kuma sai a K**a hayaniya, ga su da musu da taurin kai.
IYAYEN TSARI: Su dama wadannan baje kolin samartakarsu kawai suke, musaman samari, kafin a je inda za a sai sun kashewa budurwa kusan rabin kudin guzirinsu.
Daga Imam Auwal Warure