Jawaban Sheikh Zakzaky

Jawaban Sheikh Zakzaky Insha Allah zamu na kawo muku jawaban Jagora Sayyid Zakzaky (H) na Dakuma yazu

JAGORA (H) YA GABATAR DA JAWABIN ‘RANAR MAB’ATH’Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Da yammacin Litini 27 ga watan R...
28/01/2025

JAGORA (H) YA GABATAR DA JAWABIN ‘RANAR MAB’ATH’

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin Litini 27 ga watan Rajab 1446 (27/1/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin ranar ‘Mab’ath; wato ranar da aka fara wahayi ga Manzon Allah (S) da nufin isar da sako ga talikai, a gidansa da ke Abuja.

Jagora ya bayyana ranar ‘Mib’ath’ a matsayin muhimmiyar rana ce a wajenmu. Yace: “A wajen Amah suna cewa rannan ne Manzon Allah (S) ya yi Mi’iraji zuwa sama. (Da yake) su a wurinsu sau daya Manzon Allah ya yi mi’iraji zuwa sama. (Alhali) mu kuwa muna da ruwaya da ya nuna mana cewa, Manzon Allah (S) ya yi mi’iraji zuwa saman bakwai sau 120. Saboda haka ba sau daya ya je saman bakwai ba, tana iya yiwuwa daya daga cikinsu ya zama ranar 27 ga watan Rajab ne.”

Yace, ranar ‘Mib’ath’ na nufin randa aka ce yanzu an yarda Manzon Allah (S) ya isar da sako. “Wato k**ar ‘officially’ an ‘commission’ din shi, an ce daga yau an ayyanaka a matsayin Manzo zuwa ga mutane, isar da sako.” Ya kara da cewa: “Amma tambaya; dama can shi Manzon Allah ne? Eh! Eh! Ehh! Tun dama can shi Manzon Allah ne. Tun ma kafin a yi halitta yake Manzon Allah.”

Jagora ya cigaba da cewa: “Lokacin da Allah Ya halicce shi ya halicci Manzon Allah ne, lokacin da Ya sa haskenSa a Adam Ya sa hasken Manzon Allah (S) ne, Ya rika jujjuya shi daga tsarkakakken uba zuwa tsarkakakkiyar uwa, har Ya kai shi ga tsarkakakken uba; Abdullahi Alaihis Salam, da tsarkakakkiyar uwa; Aminatu Bintu Wahab (AS), har ya zuwa lokacin da ya fito (aka haife shi). An haifi Annabi ne, ya girma Annabi ne, amma ba a yi mashi izini ya kira mutane ba, sai da ya cika shekara 40, sannan aka ce to yanzu fada wa mutane sako.”

Ya jaddada cewa ba a ranar ‘Mib’ath’ ne ya zama Annabi ba, dama Annabi ne shi. Yace: “Shi ne fiyayye a cikin dukkan Annabawa, fiyayyen cikin Manzonni, shi ne Manzo da ya zo a karshe, amma shi ne shugabansu duka. Kuma sakonsa kawai ce mafita ga dukkan al’umma duniyarsu da lahirarsu.”

Yace: “Manzon Allah (S) shi ne na farko a jerin Annabawa, amma na karshe a aikowa. Shi aka aiko daga karshe, amma shi ne farkonsu a Annabta. Bihasali ma muna iya cewa, duk sauran Manzonni, sun zo sun isar da sakonsa ne kafin isowarsa. Wannan shiri ne na Allah Ta’ala.”

Jagora ya yi bitan yadda aka kirkiri wasu labarurruka akan yadda farkon saukan wahayi ya kasance, don a rage matsayin wannan Annabi (S), inda ya warware su da bayanai gamsassu a cikin jawabin da ya gabatar na tsawon kimanin awanni uku.

Ya jawabinsa da addu’ar samun jinkan Allah Ta’ala gare mu, da iyayenmu, da iyayen iyayenmu, da malamanmu, da Malaman malamanmu. Da kuma addua ga Shahidai da masu rauni, tare da fatan mafita ga wadanda suke tsare a hannun azzalumai a kurkukun Kuje, da Keffi da sauran guraren tsarewan soja da ‘yan sanda da jami’an tsaron ciki, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.





27/Rajab/1446
27/01/2025

27/01/2025

Shahadar Imam Musal Kazeem (AS), da kuma laifin Shahidai a wajen azzaluman da ke kashe su.

— Ɓangaren jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin tunawa da Shahadar Imam Kazeem (AS) ranar Asabar 25 ga Rajab 1446 a Abuja.

Update Leader Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) met with brothers and sisters of the islamic movement who are studying at vari...
20/01/2024

Update

Leader Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) met with brothers and sisters of the islamic movement who are studying at various universities in Iran.



19/01/2024

Hausa

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya gana da yan uwa na harka Islamiyya dake Karatu a Jami’o'i daban daban a Iran.



19/01/2024

BANGAREN JAWABIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) DANGANE DA ‘PASSPORT’ DINSU DA AKA BASUDa yake ganawa da ba’adin ‘ya...
03/10/2023

BANGAREN JAWABIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) DANGANE DA ‘PASSPORT’ DINSU DA AKA BASU

Da yake ganawa da ba’adin ‘yan uwa Musulmi a ranar Mauludin Manzon Allah (S) -17 ga Rabi’ul Auwal 1445 (2/10/2023)- a gidansa da ke Abuja, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ambata cewa:

“Kuma na so in muku wani albishir da cewa, ainihin ‘Passport’ din nan da aka yi ta fafutukar a samu, to dai yanzu yana hannu. A karshe, su da kansu s**a zo nan har gida s**a dauki hotuna da duk abubuwan da ake bukata wanda akan yi a ofis din, sun zo har gida s**a yi mana, kuma s**a aiko da Fasfo din, insha Allah.

“Saboda haka yanzu muna ‘yan shirye-shirye ne na k**a hanya, mun shirya da asibitocin da za mu je, da kuma likitocin da za su yi aikace-aikace, saboda haka ba da jimawa ba, insha Allahu za a dan ji mun dan fita. Insha Allah.

“To, muna godiya Allah Ta’ala, da kuma sadaukarwar ‘yan uwa da yawan gaske. Na ji wadansu har suna surutai, wani yana cewa, wai ‘yan Shi’a a kan Passport takardar banza wai su sun yi shahada. Nace, ba kan passport s**a yi Shahada ba, ‘Fisabilillahi’ s**a yi. Su wadanda s**a ga taron, haushin da suke ji shi ne, duk wani abu da yake bayyana izzar addinin nan tsoro yake basu. Koma wane iri ne. Shi yasa kaga suke adawa da duk wani abu. Suna son kowa ya yi shiru ne.

“Mauludin nan suna son kowa ya yi zamansa a gida ne, yace yana son Annabi (S) a zuciyarsa. Da zaran an fito, to ya nuna izzar addini, kuma haushi suke ji. To duk wani lokaci da s**a ga kuma abin da ya shafi Harkar nan, in dai s**a ganshi a bayyane, haushi suke ji. Shi yasa su kuma ‘yan uwa ko da wane lokaci akan samu wani dalili da zai sa ko da wane lokaci a rika nuna izza din, don fitowar namu izzar ce.

“Idi ainihin an yi shi ne don nuna izza shi ma, don haka aka koyar da mu cewa, a taru ne a tsakiyar gari, a fita ta hanya guda ana Azkar, in an gama Idin a dawo ta wata hanya tadaban, ba wadda aka fita zuwa Idin ba, sannan a sake haduwa a tsakiyar garin inda aka fara, sannan kowa ya k**a hanyar gida. To, da za a yi haka nan a gari guda, ace a hadu duk guri daya, kuma a dawo ta wata hanya daban. Haba! Ai ka ga zai nuna izzar wannan al’ummar.

“To, haka nan duk abin da s**a ga muke yi, wanda yake nuna martaban iyalan gidan Annabi (S) haushi yake basu ai. Mauludi yana nuna son Annabi (S) ne, sauran ‘Marasim’ na A’imma (AS) yana nuna ana raya abin da ya shafi iyalan gidan Annabi (S) din ne, don haka kowanne yana basu haushi. Suna jin haushin Ashura, suna jin haushi Mawalid da muke yi na A’imma (AS), duk wani taro namu, kai ko mene ne namu ma.

“Saboda haka, babu wani wanda ya yi shahada kan wani abu ‘in particular’. Alal misali, wanda aka kashe ranar Quds, ba za ka ce musu sun yi Shahadar Quds ba, Fisabilillahi s**a yi. Wanda aka kashe ranar Ashura, ba sunansa Shahadar Ashura ba, sunansa Shahada Fisabilillahi. Wanda aka kashe ko ma a kan mene ne, in dai an kashe shi a kan ‘manifestation’ na addini ne, to saboda addini ne. Shi ma cewa, lallai a sakar mana fasfuna dinmu, ya nuna cewa an samu wadansu mutane da su ba su yarda a zalunce su ba. Suna neman hakkinsu ta kowane hali. Kuma abin da basu so kenan, suna son a yi musu shiru ne kar a ce komai. Yauwa.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “wannan alama ce da ke nuna mutane (da s**a rika Muzaharori) sun yi ne saboda nuna izzar addini, kuma haqa ta cimma ruwa insha Allahul Azeem.”

Sannan ya kuma mika godiyarsa ga Allah (T) da cewa: “Kuma mun godewa Allah Ta’ala, duk da mun zauna da rashin lafiyar da ga yadda aka saba bisa dabi’a Dan Adam ba zai yiwu ya rayu da irin wannan rashin lafiyar ba, amma kuma da yake Allah ne mai rayawa, sai ya raya mu haka nan din.”

Yace: “Amma duk da haka dai da lalurori, musamman kuna iya ganin Malama yadda take takarkarowa babu kafa, tun 2016, yau shekara bakwai cur tana sallah a kujera ne, to amma kuma haka nan, yana dada tabarbarewa ne al’amarin guiwan nata, ba don kiyayewar Allah ba.”

Yace: “Mun yi sa’a, lokacin da aka kai mu ‘prison’ na yi ta jin tsoron kar abin ya taso mata, don takan yi k**ar ba za ta yi rai ba (idan ya tashin), to sai kuma dai bai taso ba sam har izuwa ma fitowar mu din nan, bai sake tasowa ba, amma ya rika tasowa (lokacin) muna tsare a hannun DSS. Har ma a Kaduna (lokacin ana wajen DSS) ya taso ya yi tsanani sosai. To dai kiyayen Allah ne kawai, mun godewa Allah bisa kiyayewar da ya mana da abin da yake bisa ka’idar dabi’a ba za a rayu da shi ba, kuma dai da yake Allah ne mai rayawa, shi ya raya mu din.”

Rubutawa: Saifullahi M. Kabir
03/10/2023

03/10/2023

Video

Ku kalli Jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) dangane da ba da Passport, a ranar Litinin 17 ga Rabiul Auwal 1445 (2/10/2023) a gidansa da ke Abuja.


❤️

Eid Maulud Mobarak 🌹 "Manzon Allah (S) da kyawawan ɗabi'unsa ne ya yi Nasara akan maƙiya, ba da yaƙi ba! Manzon Allah (S...
27/09/2023

Eid Maulud Mobarak 🌹

"Manzon Allah (S) da kyawawan ɗabi'unsa ne ya yi Nasara akan maƙiya, ba da yaƙi ba! Manzon Allah (S) ramzi ne na kyakkyawan ɗabi'a. Shi ne kamilin mutum, idan da akwai wanda za ka ce masa 'Perfect' a mutum, to shi ne! Shi ne 'perfect' ! Sai dai a kwaikwaye shi, shi ne samfur wanda Allah Ta'ala ya ajiye don mu koya "Walakum fi Rasulullah Uswatun Hasana" shine 'Uswa' (Abin da za a gani a kwafa). Baza a taɓa wuce shi ba, ba kuma za a taɓa dai-dai da shi ba. Shi ne abin kwafan mutum, da ɗabi'unsa kyawawa da shi ne ya yi galaba".

–Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)



12/RabiuAuwal/1445
27/09/2023

14/08/2023

Jawabin Jagora (H) na Makircin Makiya akan Harka Islamiyya da yayi jiya Lahadi 13/08/2023, yayin Ziyarar Daliban Hauza Ilmiyya.


14/08/2023

14/08/2023

IDAN AKA KAWO WA NIJERIYA HARI FARANSA CE BA NIJER BA! IN AKA KAI WA NIJAR HARI AMURKA CE BA NIJERIYA BA!

— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Jaddada Kasheji a yayin ganawarsa da Daliban Hauza a ranar Lahadi 13/8/2023 a gidansa da ke Abuja.

IDAN AKA KAWO WA NIJERIYA HARI FARANSA CE BA NIJER BA! IN AKA KAI WA NIJAR HARI AMURKA CE BA NIJERIYA BA!— Shaikh Ibrahe...
14/08/2023

IDAN AKA KAWO WA NIJERIYA HARI FARANSA CE BA NIJER BA! IN AKA KAI WA NIJAR HARI AMURKA CE BA NIJERIYA BA!

— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya Jaddada Kasheji a yayin ganawarsa da Daliban Hauza a ranar Lahadi 13/8/2023 a gidansa da ke Abuja.

Ga bangaren jawabinsa:

“Wannan yana da muhimmanci mutane su san cewa, ba yadda za a yi ace muna fada tsakaninmu da junanmu, da wai wata kasa sunanta Nijar, da wata kasa wai Nijeriya. Dama wa ya yi Nijar da Nijeriyan in ba su ba? Ba su s**a tsaga ba? S**a raba kan iyaka s**a ce nan Faransa nan Ingilishi? Mu ba mu muka yi ba, dama muna tare, sun gammu kuma a tare ne.

To, abin da nake jin tsoro shi ne, tana iya yiwuwa, tunda yanzu duk sun saka sojoji a kan iyaka, sun yi wata kalma da muka saba jin Amurka tana fada, “all options on the table”. Dama maganarsu ne in suna ma kasashe barazana. Tun Bush uba, da Bush da, da su Clinton da Obama da Trump duk kowannensu ya yi amfani da wannan Kalmar ta “all options on the table”. Sai gashi wannan kalmarsu ce. Wato yanzu ba su cire yiwuwan su kai yaki ba.

To wa zai yaki wani? Don Allah ina ruwan Nijeriya da wani abu wai shi ‘Democracy’ a Nijar? Ina ruwansu? Sau nawa ana juyin mulki a Nijar su koma kan farar hula? Ina ruwan Nijeriya? Nijeriya ta je ta yi musu? Sau nawa kuma ana juyin mulki a nan? Wa ya zo yace mana dole sai an koma farar hula? Na taba jin dirkaniya irin wannan? Haka kawai kace dole kai za ka je ka (yi yaki da sunan kai Damukuradiyya?).

To kuma a sarari yake wannan ba yakinmu ba ne, yakin Amurka da Faransa ne. To kuma Faransa duk da Nijar sun rufe sararin samaniyarsu, sun hana abi, amma Faransa tana bi da jiragenta. Kuma suna da sansanoni na ‘yan ta’adda, wanda har an k**a wasu sun je sun kwace su. Daga nan ake kawo hare-hare Nijeriya. Wadanda ake ce ma ‘yan boko Haram din nan, ai sansanoninsu na can ne. Za su zo su kawo hare-hare, su debi gwalagwalai a raba.

To yanzu abin da nake jin tsoro shi ne, suna iya su yi amfani da wadannan ‘yan ta’addan. Ko kuma su da kansu ma su kawo hari ta sama, su ce Nijar ta kawo harin. Sai a fake da wannan ace, ai gashi nan Nijar ta kawo mana hari, saboda haka yanzu Nijeriya ma ta mai da martini. Saboda haka randa duk aka ji ko an yi harbi a Nijeriya, ko an ‘crossing boarder’, to ka tabbatar su ne s**a yi; Faransa ce da Amurka s**a yi, ba Nijeriya ba, ba Nijar ba!

Ba yadda za a yi ma a yi fada babu ma gaba. Haka kawai? Na wani da nake ba da labarin wani abu da naji wani ya fada, k**ar karin magana ne. Yace, wai ko kauye ka je kaga wa da kani suna fada, to ka bincika, Baturen Ingila ya zo wurin. Ingilishi ya zo nan. Yace, saboda duk inda s**a je suna hada fada ne. Duk inda s**a je, dama salonsu ne, tuntuni haka s**a saba, duk inda s**a je su hada fada, shikenan, shi wannan ke basu dama su mallaka.

To yanzu, an taba hada fada, baa bin da ya hada mu, muna zaune kawai muna zumunci, mun zama abu daya ne, mu fa ba daban-daban ba ne, mu abu daya ne, kawai rana daya ace wai muna fada? Wannan hauka har ina? To amma suna iya yi, tunda su suke da bukatar yin fada din, su za su iya zuwa su hahharbi wurare, sai su ce kuma ana mai da martani. Sai mu wayi gari kawai ana rugurguza kauyukanmu da biranenmu, ba a san adadin mutanen da za a kashe ba, a kan abin da babu gaira babu dalili illa kawai za su debi arziki. Shikenan abin da ya kawo su, basu kuma damu ba, duk cikanmu gaba daya suna iya kashe kowa, basu kuma damu ba, ba mu ne ke da muhimmanci ba.

Dama da s**a fara yakin Ukrain, sun nuna a sarari basu damu da mutanen Ukrain ba, ko da duk za su halaka, suna son a yi ta yakin ne har Rasha ta durkushe. Abin da ya dame su kenan, in ya so duk mutanen Ukrain su halaka. Amma kuma suna takaicin cewa mutanen Ukrain fa Turawa ne, har suna fada, wannan fa ba mutanen wai Afganistan ne ko Iraq ba, mutane ne fa masu shudin ido. Kai ka ji irin wannan. Wato abin takaici, shine mutum mai shudin ido yake mutuwa, inda mutumin Afganistan ne ko mutumin Iraq ai ba damuwa, sai ya mutun kawai. To yanzu kuma ina ga mutumin Afirka, wanda shi basu dauke shi ma a bil’adama ba. Shi kaga shi za a iya kashe shi ba damuwa, in ya so duk gaba daya shi ya kare, tunda shi basu dauke shi ma a matsayin bil’adama ba ma, ballantana har su yi tunanin don me ba zai mutu ba.

To, banda dirkaniya, su wadanda s**a yi juyin mulkin nan a Nijar, basu kashe kowa ba, ko an kashe wani? Ko mutum daya. To amma yanzu ana barazanar za a yi amfani da karfin soja a je a yi fada a kashe mutane don a dawo da Bazoum. In mutum yana da hankali, Bazoum din nan yana hannun wane ne? Yana hannun soja. Bazoum din nan fa mutum ne ba tsauni ba ne, kasan in kana rigima kan tsauni idan ka kori mutum sai ka kwace tsaunin ko? Ba kogi ba ne, in kogi ne, idan ka kori mutum sai ka kwace kogin. To shi mutumin nan kuna tsammanin yana hannunsu, sai ku je ku yi musu luguden wuta, sai su ce muku ga Bazoum dinku?

To kuma mu kaddara, in banda wauta ma, idan misali kuka ce Bazoum za ku dawo da, a karagar mulki. To in abin ku je ne, tunda Bazoum din yana nan k**ar kila ba za a yi masa komai ba, yana hannunsu. Sai su sako Bazoum din, sai ku dora shi, to za ku dawo Nijeriya ne? Ko kuwa za ku zauna ne ku tabbatar mulkin ya cigaba? Ko kuma yanzu babu wani soja a Nijar kenan sai ku? Na tabbata ba Bazoum ya dame su ba. Abin da ya dame su kawai, su haddasa fitina, a rugurguza kasashen nan guda biyu a debi arzikin wurin. Illa iyaka.

To dama abin da nake jin mana tsoron, kar wata rana a wayi gari an kawo mana hari a ce Nijar ne. In aka kawo mana hari mun san wa ya kawo mana hari, Amerika da Faransa ne, ba Nijar ba! Haka kuma in an kai hari Nijar, to ba Nijeriya ce ta kai mata hari ba, Amurka da Faransa ne! Saboda mene? Ba mu suke bukata ba, basu bukatarmu, suna bukatan arzikin da ke karkashin kafafunmu ne, kuma abin da ya kawo su kenan. Amma muna fatan Allah Ya kiyaye.

Nace, har wala yau, ba kawai muna gargadin cewa suna iya zuwa su haddasa fada tsakanin abin da suke kira Nijar da abin da suke kira Nijeriya ba ne, suna iya haddasa fada kuma a cikin kowadanne. Yanzu ma suna iya haddasa fada na kabilanci a cikin ita Nijar din, su ce mutanen Bazoum yan kabila kaza ne, mutanen kuma kaza suma kaza, sai a yi fada, k**ar yadda s**a haddasa a Sudan ana yi tsakanin Dinka da Nuer. To suna iya haddasa wannan.

Kuma Nijeriya din ma, shima suna iya ba da dama ana cikin yin wannan, wani bangare yace shi ma ya b***e. An fahimta ai? Sai ya zama shima an koma ana fadan cikin gida a cikin Nijeriya din. Duk zai taimake su. Kowanne zai taimake su. Fadan cikin gida yana iya yiwuwa a cikin Nijeriya kanta, tsakanin Kudu da Arewa, ko Kudu maso Gabas yace ya b***e. An fahimta ai? Dama akwai masu kiran b***e-b***e. Kaga sai a ce a raba kasar gida uku ko hudu. Sannan kuma ko cikin Arewan ma suna iya haddasa rigima, s**e ai akwai Musulmi akwai Kirista, an fahimta? Duk suna iya haddawa wadannan, saboda haka a kiyaye.

Musamman ‘yan Nijar. Kar su yarda a jefa su a fadan kabilanci. Domin su al’umma guda ce, kuma kabila Allah ne dai ya yi kabila ba wani ya yi kabila ba. Ko akwai bambancin kabila tsakanin wasu da wasu, Allah ne ya yi kabilolin. Kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa, “Waja’alnaakum shu’uban wa qaba’ila lita’arafu.” Allah ne ya yi kabiloli daban-daban don su san juna, ba don su yi fada ba. Saboda haka yanzu ana iya haddasa wannan, a kiyaye, kar a yarda a fada rigimar cikin gida tsakanin mutumin Nijar da mutumin Nijar da sunan wannan dan kabila kaza ne, wancan dan kabila kaza ne.

Har wala yau, mu kuma nan, kar a haddasa mana rigimar cikin gida tsakanin Kudu da Arewa, ko tsakanin Musulmi da Kirista, ko tsakanin wasu kabila da wasu kabila. Allah dai ya kiyaye.

Abin da muka ce, muna da babban makami, wanda ya fi kowane irin makami, shi ne komawa ga Allah. A koma ga Allah da magiya da addu’a, don duk wata aniya ta makiya Allah Ta’ala ya fi karfinsu. Su karfin nasu na makami ne, amma karfin Allah Ya fi su. Aadawa sun ce “Man ashaddu minna quwwa?” Allah Ta’ala yace, to basu ga wanda ya halicce su ya fi su karfi ba? Yauwa. To Allah Ta’ala ya fi karfinsu. Muna fata Allah Ta’ala Ya kiyaye mu da kiyayewarsa. Insha Allahul Azeem.”

— Cibiyar Wallafa
Www.cibiyarwallafa.org

06/08/2023

Gargadi ga Masu Zumudin Kaiwa Jamhuriyar Nijar Hari.


06/08/2023

08/07/2023
Update:Yan uwa mata da s**a shirya tadrib sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa dake Abuja.  17/06/20...
18/06/2023

Update:

Yan uwa mata da s**a shirya tadrib sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa dake Abuja.


17/06/2022

Update: Leader Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) met with the brothers and sisters who were discharged and acquitted by the co...
04/06/2023

Update:

Leader Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) met with the brothers and sisters who were discharged and acquitted by the court after 4 years of illegal detention in Kaduna prison.


04/06/2023

Hausa:

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), ya gana da yan uwa maza da mata da kotu ta wankesu bayan shekaru 4, bisa zalunci a gidan yarin Kaduna.


04/06/2023

Update During 7-day programme to mark 2023 Imam Khomeini's Week, the representatives of the Academic Forum of the Islami...
04/06/2023

Update

During 7-day programme to mark 2023 Imam Khomeini's Week, the representatives of the Academic Forum of the Islamic movement in Nigeria, pay a visit to leader, Sheikh Ibraheem Zakzaky today at his Abuja residence.



03/06/2023

Hausa:

Yayin da ake gudanar da tarukan makon Imam Khomeini (QS) na shekarar 2023, wakilai daga dandalin daliban harka islamiyya (Academic Forum), sun ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a gidansa dake Abuja.



03/06/2023

20/05/2023

JAWABIN JAGORA SAYYID ZAKZAKY [H] NA RUFE MAKON MUJADDADI SHEIKH USMAN BN FODIYE [RA] A SAKKWATO

Cikakken Jawabin jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky [H] wanad ya gabatar na rufe makon Sheikh Usman Bn Fodiye [RA] da bangaren ACADAMIC FORUM s**a gabatar a Sakkwato.

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi bakuncin dalibaidaga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin saukar...
17/05/2023

Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi bakuncin dalibai
daga makarantun fudiyya daban daban dake shirin bikin saukar Alkur’ani, yau Laraba a gidansa dake Abuja.


17/05/2022

SANARWA: Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H). بسم الله الرحمن الرحيم وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ الَّذِينَ إِذَا أَصَاب...
07/05/2023

SANARWA:

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).

بسم الله الرحمن الرحيم

وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُواْ *إِنَّا لِلّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعونَ* ، أُولَئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ وَأُولَئِكَ هُمُ الْمُهْتَدُونَ!!

Ana sanar da ƴan'uwa rasuwa Ɗan"uwa Malam Jamilu Ya'qub, hadimin gidan Jagora (H), a sak**akon hadarin mota a hanyarsa ta dawowa Abuja daga Kaduna.
Jana'iza: Gobe Litini 8/5/2023
Waje: Gidan Marafa, Matazu Road , Sabo Gari, Tudun Wada, Kaduna.
Lokaci = Karfe 2:00 na Rana

Allah Ya amshi uzirinsa, Ya yafe masa, Ya saka shi cikin ceton Annabi da iyalan gidansa tsarkaka. Mu kuma Allah Ya tabbatar da mu bisa tafarkin addinin Musulunci har karshen rayuwarmu.


-Fatiha🙏
7/5/2023

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jawaban Sheikh Zakzaky posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jawaban Sheikh Zakzaky:

Videos

Share

Category