02/02/2023
Kotu ta aike da tauraruwar TikTok, Murja Kunya gidan yari
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hockey, Kano, ta bayar da umarnin tsare shahararriyar mai yin TikTok ɗin nan, Murja Kunya, a gidan yari.
Ƴan sanda ne su ka k**a Murja a ranar Asabar a yayin da ta ke kokarin k**a wa bakinta da su ka zo daga nesa da kuma kusa domin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta da aka yi ta yaɗa wa.
A watan Satumban shekarar da ta gabata ne wata kotun shari’ar Musulunci da ke Bichi ta rubuta wa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano wasika da ya k**a Murja tare da wasu ƴan TikTok bisa laifin lalata tarbiyyar al’umma.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa an gurfanar da ita a ranar Alhamis a gaban kotu bisa zargin bata suna, kalaman batsa, takura wa al’umma da kuma ɓata zaman lafiya.
An kara zargin bata suna ne a kan shari’ar, biyo bayan korafin da wasu ‘yan TikTok biyu, Aisha Najamu da Idris Maiwushirya su ka yi, na cewa Murja ta bata sunan su a kan zargin su da laifin da ta aikata.
Lokacin da lauya mai shigar da kara, Lamido Sorondinki ya karanta mata tuhumar, Murja ta musanta aikata laifukan.
Bayan musanta laifukan, lauyanta, Yasir Musa ya gabatar da bukatar neman belin ta, wanda lauyan masu gabatar da kara ya yi s**a a kan haka.
Alkalin kotun, Abdullahi Halliru, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Murja a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci kan neman belin.