27/01/2025
ASH-SHEIKH ALQASIM HOTORO YA TAIMAKA MA 'DIYAR MALLAM ALBANIY ZARIA (RH) DA KUDADE MASU YAWA. MUNA ROKON ALLAH YA SAKA MISHI DA ALKHAIRI. (CIKAKKEN LABARIN YANA CIKIN WANNAN RUBUTUN NA 'KASA)
ALLAH YA SANI BA MU MUFIN KOWA DA BATANCI
Ni Datti Assalafiy da Engr Abu-Ameena Bn Khamis duk wanda ya san mu a kafar Facebook tun daga lokacin da aka harbe Sheikh Albaniy Zaria ya san cewa mun yi kaurin suna wajen yada da'awar Marigayi Sheikh Albaniy Zaria da kare kyawawan manufofinsa
Don haka idan kun ga mun damu da bayyana halin da iyalansa suke ciki a yanzu sai ku mana uzuri, an kai wani matakin da ya zama bamu da wani zabi sama da mu bayyana ne
Muna cikin hali na nema wa Aisha 'yar Marigayi Malam Albaniy Zaria tallafi akan jarrabawan da ya sameta, kuma wadanda ya kamata su taimaka mata sun yi watsi da ita, sai kuma aka ankarar damu cewa akwai Fatima ita ma 'yar Marigayi Malam Albaniy Zaria tana fama da ciwon hanta kamar yadda zaku gani a wannan hoto na screenshot
Akwai daya daga cikin manyan Daliban Albaniy wanda suke rike da Darul Hadith ya taba auren Fatima, harma ta haifa masa yaro, amma ya saketa, yanzu da take fama da cutar hanta ai ko don albarkacin Mahaifinta ya kamata ace ya tallafa mata, amma yayi watsi da ita
Na samu labari akwai Babban Malami Sheikh Al-Qasim Hotoro ya gudanar da bincike akan ciwon hanta da yake damun Fatima, bayan ya samu tabbaci har ya tura wa Fatima da tallafin kudi Naira dubu dari domin taje a sibiti ta fara jinyar hanta
Wallahi naji dadin abinda Sheikh Al-Qasim Hotoro yayi, na san Malam ba zai so a bayyana ba, muna fatan zai yi hakuri, mun bayyana wannan abinda yayi na alkhairi ne domin ya zama abin koyi garemu gaba daya
Har ila yau muna cigaba da nemawa Aisha taimako, zuwa yanzu an tara mata kudin da ya haura Naira dubu dari biyar, ga account number dinta
0035200236
Stanbic IBTC
Aisha Muhammad
Mai neman karin bayani ya kira kaninta Ustaz Abdul-Haleem Muhammad Auwal Albaniy Zaria ta nambar wayansa 09016808281
Kamar yadda na fada bama nufin kowa da batanci ko sharri, amma ba mu ji dadin yadda aka juya wa iyalan Malam Albaniy Zaria baya ba, idan wadanda ya kamata su gyara sun gyara shikenan, idan kuma basu gyara ba duniya ce, duk abinda mutum ya shuka shi zai girba
Muna rokon Allah Ya jikan Malam Albaniy Zaria, Ya kula masa da iyalansa