Dandalin damagarawa

Dandalin damagarawa Fasahar sadarwar zamani Domin yan'uwana su anfana da wannan DANDALIN DAMAGARAWA DOMIN FADAKARWA DA NISHADANTARWA DA KUMA KARANTARWA

A yanzu mutanen ƙasashen Ecowas za su iya shiga ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar su yi yawo ko su zauna a ciki ba ...
15/12/2024

A yanzu mutanen ƙasashen Ecowas za su iya shiga ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar su yi yawo ko su zauna a ciki ba tare da biza ba.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/49FknLo

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun kara tabbatar da yin hannun riga da kungiyar ECOWAS. Hakan na zuwa ne a daida...
14/12/2024

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun kara tabbatar da yin hannun riga da kungiyar ECOWAS. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ECOWAS din ke ci gaba da zawarcin kasashen uku na ci gaba da zama mambobinta.

A Nigeria Da dumi'dumi: Rundunar 'Yan sandan Jihar Kano ta k**a wasu da kudede har kimanin Bilyan dari 100bn.Rundunar 'Y...
10/12/2024

A Nigeria Da dumi'dumi: Rundunar 'Yan sandan Jihar Kano ta k**a wasu da kudede har kimanin Bilyan dari 100bn.

Rundunar 'Yan sandan Nigeriya Reshen Jihar Kano sun kwato kudaden jabu kwatankwacin jimillar Naira Bilyan Dari da Ashirin (N129,542,823,000:00) tare da Dalar Amurka ($3,366,000 da cefa (CFA51,970,000.

Sai kuɗin gaske Naira Dubu (N1,443,000 Rundunar 'Yan sandan ta bakin kakakinta na Jiha Abdullahi haruna Kiyawa Tace Za a Kai wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike domin karbar hukunci a gaban kuliya da zarar an kammala binciken.

Mulkin Jam’iyyar Baath ya kare Bayan shafe Shekaru 61 a kasar Syria. Bayan shekaru 61 da mulkin k**a-karya na jam’iyyar ...
10/12/2024

Mulkin Jam’iyyar Baath ya kare Bayan shafe Shekaru 61 a kasar Syria.

Bayan shekaru 61 da mulkin k**a-karya na jam’iyyar Baath, mulkin ya zo karshe, lamarin da ya jawo farin ciki da murna a fadin kasar Syria.

Wannan nasarar mai cike da tarihi ta haifar da dumbin farin ciki ga al’umman Syria inda su fito kan tituna don nuna jin dadinsu da fata mai kyau ga sabon babin da kasar Syria za ta shiga.

birnin Damaskus, babban birnin kasar, dubban mutane sun taru suna rera wakoki da shewa, suna nuna alamar karshen mulkin da ya dade yana takurawa rayuwar ’yan kasa.

’yan Syria da s**a yi hijira sun fito suna murna tare da fatan dawowar dimokuradiyya da zaman lafiya.

Wasu daga cikin masu magana da yawun jama’a sun bayyana cewa wannan nasarar ta kasance sak**akon juriya da hadin kan jama’ar Syria da s**a kwashe shekaru suna fafutukar ganin sauyi. Tuni shugabannin duniya s**a fara bayyana yabo da goyon bayan su ga sabon shugabanci da ake fatan zai ginu akan adalci da walwala ga kowa da kowa.

Sabuwar gwamnati da ake fatan kafa ta yanzu za ta fuskanci kalubale masu yawa, musamman maido da zaman lafiya, sake gina kasa, da tabbatar da jin dadin ’yan kasa. Sai dai, wannan nasarar ta kasance wani mataki na farko da ke nuna karfin ikon jama’a wajen kawo canji mai kyau Ga al’ummar Syria, wannan sabon babin na nufin damar sake gina kasa da tattalin arziki tare da dawo da martabar kasar a idon duniya.

Babbar Magana: Sojojin NIJAR sun kwace iko da kamfanin FARANSA da ke aikin hakar ma'adinar URANIUM a kasar.Sai dai kamfa...
04/12/2024

Babbar Magana: Sojojin NIJAR sun kwace iko da kamfanin FARANSA da ke aikin hakar ma'adinar URANIUM a kasar.

Sai dai kamfanin Orano ya ce sam ba za ta sabuna ya kyale a kwace reshensa da ke Nijar wato SOUMAIR wanda ke samar da kashi 20 cikin dari na maadinar URANIUM da kasar FARANSA ke amfani da shi.

NIJAR dai tana da jarin kaso 36.6 cikin 100 na jarin kamfanin na SOUMAIR

Hezbollah ta bayyana cewa ta kai hari kan wani sansanin sojin Isra’ila a matsayin martani na farko ga take dokar tsagait...
03/12/2024

Hezbollah ta bayyana cewa ta kai hari kan wani sansanin sojin Isra’ila a matsayin martani na farko ga take dokar tsagaita wuta da gwamnatin Isra’ila ta yi.

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa ba za a iya ɗaukar zagin Annabi Muhammad a matsayin 'yancin faɗin a...
03/12/2024

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa ba za a iya ɗaukar zagin Annabi Muhammad a matsayin 'yancin faɗin albarkacin baki ba.

Da yake magana kan batun mutunta ra'ayoyin addini, Putin ya jaddada muhimmancin daidaita 'yancin faɗin albarkacin baki da ɗabi'un al'adu da addini.

Kalaman na Putin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a duniya kan iyakokin 'yancin faɗin albarkacin baki wato (Freedom of speech) a turance.

Wani rahoto dake fitowa yanzu daga Siriya shi ne, rikici ya ɓarke tsakanin 'Ƴan taaddan akan shugabanci, k**ar yadda kaf...
02/12/2024

Wani rahoto dake fitowa yanzu daga Siriya shi ne, rikici ya ɓarke tsakanin 'Ƴan taaddan akan shugabanci, k**ar yadda kafar labaru ta Almayadeen ta ruwaito

An samu rabuwar kai tsakanin Ƴan taaddan masu kiransu kansu da sunan Hay-at Taharir da kuma Jaysh Al-Islam masu ikirarin Salafanci, akan wanda zai zama babban shugaban a Aleppo.

Sak**akon ɓarkewar rikici ya kai ga sun buɗewa kansu wuta, akwai tabbacin mutuwar shugaban Hay-At ɗin, da kuma raunata wasu da yawa a tsakanin 'Yan taaddan.

Almujtabah Abubakar

Pour tout vos travaux de peinture et décoration ou rénovation contactez notre page ou bien appeller ces numéros : 227 87...
24/11/2024

Pour tout vos travaux de peinture et décoration ou rénovation contactez notre page ou bien appeller ces numéros : 227 87913071-98904849-80458904

Zinder Niger 🇳🇪 🇳🇪 🇳🇪

Voici quelques photos de mon travail

👇👇👇👇

HIKAYA TA...!!!Tana kwance akan shimfiɗar ajali, ta cewa mijinta, ka gafarta mini...! Ya ce babu komai!Ta ce, dukkan rig...
24/11/2024

HIKAYA TA...!!!
Tana kwance akan shimfiɗar ajali, ta cewa mijinta, ka gafarta mini...! Ya ce babu komai!

Ta ce, dukkan rigimar da ta faru tsakanin Kai da Mahaifiyarka ni na kunnata. Ya ce, babu komai, na yafe miki...!

Ta ce, ƴan uwanka da s**a tsane ka, ba sa son ganinka duk ni na shiga tsakaninku. Ya ce, kar ki damu, duk na yafe...!

Ta ce, basuss**an da na jefa ka, da kuma faɗa tsakaninka da abokan aikinka ka yi haƙuri..!!! Ya ce, komai ya wuce, ki daina tunawa...!

Matarka daka rabu da ita ni na shiga tsakaninku kuma ni na saka Alƙali ya turaka gidan gyaran hali....! Ya ce, na yafe, Allah mai gafara ne kuma mai jin ƙai...!!!

Ya ce, nima ki yafe mini.....!!! Ta ce, baka yi mini komai, ai kai Waliyi ne, in ma akwai, sai dai bisa kuskure, kuma na yafe maka Duniya da Lahira.

Ya ce, na san duk abin da kika aikata, shi yasa na baki Shayi da GUBA a ciki.......!!!!!

🇳🇪🇳🇪Pour tout vos travaux de peinture et décoration ou rénovation contactez notre page ou bien appeller ces numéros : 22...
07/11/2024

🇳🇪🇳🇪Pour tout vos travaux de peinture et décoration ou rénovation contactez notre page ou bien appeller ces numéros : 227 87913071-98904849-80458904

Zinder Niger 🇳🇪 🇳🇪 🇳🇪

Voici quelques photos de mon travail

👇👇👇👇

Labari Da Ɗumi Ɗumi: Wanda baya Bibiyan abinda ke faruwa baze taɓa kallon hakan a Nasara ba.Banjamen Natanyaho Firaminis...
06/11/2024

Labari Da Ɗumi Ɗumi: Wanda baya Bibiyan abinda ke faruwa baze taɓa kallon hakan a Nasara ba.

Banjamen Natanyaho Firaministan ƙasar Haram Isra'ila ya kori ministan tsaron ƙasar Mr. Galant da yammacin yau Talata. Wannan gagarumin ɓaraka ce ga ƙasar zanyi bayanin hakan daga baya.

Wannan ba shi ne ma babban labari ba, Babban Labarin shi ne yanda aka k**a wasu Jami'an Ofishin sa su biyu ciki harda ɗaya da yake zuwa ko ina tare da shi, amma aka k**a su da lefin tuhuma biyu.

Ta farko fidda bayanan sirri mafiya tsada da tsaro, da kuma zargin leken asiri me ƙarfi da ake zargin suna temakewa Dakarun HMS ko jam'iyun Adawa. Cikin abinda aka tabbatar sun fitar wanda ze iya jefa Natanyaho gagarumar matsalar tsigewa da kuma hukunci me tsauri.

Yanda aka fitar da Natanyaho ya tsara wasu abubuwa da gangan domin ya ja dogon yaƙin nan kuma ya haifar da matsala wajan yarjejeniyar zaman lafiya da tsagaita wuta.

Abubuwa sun rikicewa ƴan Mamaya, gaba tsanani ciki zafi waje wuta. Ko ina babu sauki. Ga Bala'in Luguden da suke sha a Arewacin Lebanon ga barazana da suke sha a Gaza hatta a Rafah da s**a ce sun kafa tutar su. Ga kuma rashin bacci na sauraron zuwan Azaba na TP3 daga Iran da ze iya zuwa kowane lokaci daga yanzu! Ga ƴan ƙasar kullum zanga-zanga sun gaji, ga babu kasuwa babu makaranta...ga.. ga...ga....ga..

"Lallai a  wannan karon ba za mu taɓa nuna tausayawa ga makiya ba".- Janar Shahram Irani, kwamandan sojojin ruwa na kasa...
04/11/2024

"Lallai a wannan karon ba za mu taɓa nuna tausayawa ga makiya ba".

- Janar Shahram Irani, kwamandan sojojin ruwa na kasar lɍañ, kuma ahlusunna.

Almujtabah Abubakar

Wasu rahotann dake fitowa, sun bayan cewa kasar lɍañ ta sanar da sauran kasashen yanki niyyar na kai wani gagarumin tunb...
04/11/2024

Wasu rahotann dake fitowa, sun bayan cewa kasar lɍañ ta sanar da sauran kasashen yanki niyyar na kai wani gagarumin tunbatsattsen farmaki mai sarkakiya kan lzɍal, wanda ya haɗa da wasu manyan mak**ai masu karfi sosai, da ma wasu na'u'in mak**an wanda bata bayyana ba.

Shafin labarun Tasnim News Agency dake kan Twitter, sun ruwaito wani babban Sojan kasar lɍañ na cewa, tabbas shirin farmakin kai lzɍal zai faru.

Yanzu dai za iya cewa kasar lɍan ta kammala shirin tsaf domin kai wannan farmakin na ramuwar gayya.

Jamhuriyar Nijar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya a yau Juma'a da Glavkosmos, wani reshen hukumar kula da sararin s...
01/11/2024

Jamhuriyar Nijar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya a yau Juma'a da Glavkosmos, wani reshen hukumar kula da sararin samaniyar kasar Rasha, wato Roscosmos, na sayen tauraron dan adam guda uku, domin inganta tsaro a yankin Sahel da makwabtanta, wadanda dukkansu ke fama da hare-haren masu da’awar jihadi.
Muna fatan Allah bawa kashenmu nasara

🔥🔥🔥🔥🔥Idan kayi Notcoin ko Dogs ko Hamster ko telegram din ka ya dan kwana biyu to zaka sami airdrop na PAW yanzu ba waha...
29/10/2024

🔥🔥🔥🔥🔥

Idan kayi Notcoin ko Dogs ko Hamster ko telegram din ka ya dan kwana biyu to zaka sami airdrop na PAW yanzu ba wahala.

Kawai zasu duba abubuwan sama da dadewar telegram din ka su baka PAW, ba abunda zaka kara yi k**ar dai dogs

Domin yin register: Link👇👇

👇https://t.me/PAWSOG_bot/PAWS?startapp=Fs7J7UXy

Shugaban kasar Senegal Basirou Diomaye Faye ya cacaki kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya dangane da kashe kashe d...
26/09/2024

Shugaban kasar Senegal Basirou Diomaye Faye ya cacaki kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya dangane da kashe kashe da kuma tabarbarewar zaman lafiya a yankin Sahel. Faye ya ce ba za su amince da bukatar wasu manyan kasashe na mayar da yankin Sahel abokan gaba da kuma ci gaba da haifar da tashin hankali a yankin. Shugaban ya bayyana cewar zaman lafiyar Afirka shi ne zaman lafiyar duniya.

📷 UN

Adresse

Zinder

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Dandalin damagarawa publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à Dandalin damagarawa:

Vidéos

Partager