Komi Da Ruwanka

Komi Da Ruwanka Sharhi, Fashin baƙi, Mahaura da Nishaɗantarwa
(3)

DemokuraɗiyaAna kallon tsarin demokuraɗiya a matsayin tsari mafi dacewa da kowace al'umma.Saidai kash! Akwai lokacin da ...
16/11/2023

Demokuraɗiya
Ana kallon tsarin demokuraɗiya a matsayin tsari mafi dacewa da kowace al'umma.
Saidai kash! Akwai lokacin da demokuraɗiya take zama bala'i ga al'umma.
Wane amfani ƴan Nijar s**a samu a zamanin mulkin Mahamadou Issoufou idan masu hankali zasu duba ?
Akwai lokacin da za'a buƙaci wani sabon tsarin mulki da zai share hawayan ƴan ƙasa koda kuwa ya saɓa da abunda wasu ke kira da demokuraɗiya.
⭐KOMI DA RUWANKA ⭐

10/11/2023

Bayan tsanani akwai sauƙi da izinin Allah.
Alamomin sauƙi sun fara bayyana a Nijar 🇳🇪 idan aka kwatanta da makonin farko farkon juyin mulki.
Daga kiraye kirayen akawo harin soja, ƙasashen duniya sun sauya alkibla inda suke kira akawo sassauci akan takunkumai da aka garkamawa Nijar.
Masu goyan hambarrariyar gwamnati kuma tsuliya ta fara kwasar ruwa tunda sun ga ana neman juya shafin maganar Mohamed Bazoum.
Sanu sanu bata hana zuwa.
⭐ KOMI DA RUWANKA ⭐

A kafta kawai.
10/11/2023

A kafta kawai.

Muna Kira ga Yan'majalisar jaha da na tarayya da sanatoci da ministota Yan Arewa da su shiga duk inda ya dace su fada do...
04/11/2023

Muna Kira ga Yan'majalisar jaha da na tarayya da sanatoci da ministota Yan Arewa da su shiga duk inda ya dace su fada domin a bude bodar Nigeria-Niger.

Haka ma, Muna Kira ga Mai girma shugaban kasa da ya sa a bude Mana bododi Kamar yadda na kudu suke a bude, domin a halin yanzu Yan kasuwarmu na Arewa ke fuskantar kariyar tattalin arziki su Kuma na kudu a cikin walwala suke, yin haka shi ne adalci.

Rufe boda ba ra'ayin Yan kasa bane, an yi ne domin Kare muradun wata kasa da take ganin yin juyin mulki a wata kasa zai hana ta samun abunda ta Saba samu.
~ Inji Prof. Muhammad Sani Umar R/lemo.
Copied

Ƙasar Faransa zata ƙara tallafin da take baiwa ECOWAS domin tabbatar da demokaradiya a yankin mai fama da juyin mulki.To...
04/11/2023

Ƙasar Faransa zata ƙara tallafin da take baiwa ECOWAS domin tabbatar da demokaradiya a yankin mai fama da juyin mulki.
To ruwa dai baya tsami banza.
🔴Wace shawara zaku bada ga ƙasashen da akayi juyin mulki ? Kuna ganin cewa ƙasar Faransa ba zata iya ƙulla wani sabon makirci ba ta hanyar amfani da ECOWAS ?
⭐ KOMI DA RUWANKA ⭐

🔴 MAHAURAMinene amfani da kuma illolin auren mace mai tarin dukiya a wannan zamanin da muke ciki?⭐ KOMI DA RUWANKA ⭐
03/11/2023

🔴 MAHAURA
Minene amfani da kuma illolin auren mace mai tarin dukiya a wannan zamanin da muke ciki?
⭐ KOMI DA RUWANKA ⭐

Juyin mulki a Nijar 🇳🇪
02/11/2023

Juyin mulki a Nijar 🇳🇪

27/10/2023

Hausawa suna cewa Allah shi ya ke ciyar da maraye koda mai uwa bai so ba.
Duk da taron dangi da aka yi wa Nijar, Allah ne ya ke arzuta mu da mafita. Idan Allah yana tare da ƴan Nijar, duk wani ɗan gani kashenin Bazoum ko ECOWAS ko Faransa zasu yi munafurcinsu su ƙare ba tare wani abu ya same mu ba.
Tun kafin tafiya ta yi nisa, ya kamata waɗanda suke cikin yanayi na bijirewa su tuba su dawo kan hanya.
• Saƙo zuwa ga ƴan saï Bazoum
Ku san sa cewa ƙaddara ta rigayi fata. Shafin mulkin Bazoum saï wani jiƙon kuma. Ko ku rungumi ƙaddara ko kar ku yarda, Allah shi ne masani akan abunda ya fi zama alkairi ga ƙasarmu Nijar.
• Saƙon zuwa ga duk wani ɗan mai son Nijar da gaskiya.
Duk da yake kuna addu'oi dare da rana, kar ku gaji da yin addu'oi da fatan Allah ya kare ƙasar Nijar daga maƙiya na cikin gida da na waje, na nesa da na kusa. Muna son ƙasarmu Nijar. Kuma mun ɗauki wannan juyin mulki da takunkumin ECOWAS a matsayin jarabawa da Allah. Insha Allahu bayan wuya saï daɗi.
🔴 Shin abu ne mai sauƙi dawowar Bazoum akan karagar mulki ? Za'a yi mulki babu goyan bayan ƴan ƙasa da jami'an tsaro ?
Ku bayyana ra'ayinku akan wannan batun.
⭐ KOMI DA RUWANKA ⭐

27/10/2023

Barkanmu da zagayowar ranar Juma'atu babbar rana.
Ga wasu shawarwaru ga iyaye mata akan tarbiyar ƴaƴansu mata.
1. Ki gargadi 'yar ki kada ta kuskura ta
zauna a cinyar wani, koda kanin babanta ne ko Almajirin gidansu.

2. Kada ki dinga canja kaya a gaban
'ya'yanki wadanda s**a kai kamar shekara biyu, Ki dinga cewa su fita.

3. Kada ki yarda wani babban mutum ya
dinga kiran 'yar ki da "Mata ta" ko
"Amarya ta" dds.

4. Idan 'ya'yanki suna wasa da wasu yaran, ki dinga lura wane irin wasa sukeyi. Saboda wasu yaran suna wasa da al'aurar junansu.

5. Kada ki matsawa 'yar ki zuwa wajen
wanda ba ta so ta je wajensa. Kamar
wani me siyar da kayayyaki ko
makamancinsu.

6. Ki saka lura sosai idan kika ga dan ki ko
'yar ki suna shaqu da wani mutum a waje
kuma suna son zuwa wajensa.

7. Kada ki bari dan ki ko 'yarki su dinga
yawo ba riga ko wando a cikin gida b***e su fita waje.

8. Idan kin yiwa 'yar ki kwalliya, to ki gaya
mata iya gidajen da za ta shiga.
Kuma daga nan ta dawo gida. Kada ta zauna a rariya ko shige-shigen gidaje.

9. Idan ki ka ji an yiwa abokin dan ki ko
kawar 'yarki wani abu mara dadi, to kema ki binciki na ki sosai. Ki tuhume shi.

10. Idan 'ya'yanki mata sun fara girma, ki
koya musu yada ake kula da Alada. Da yadda ake kula da budurci da hadarin kawar da shi. In ba haka ba zata fara koyar munanan dabi'u a wajen kawaye.

11. Ki kula da irin kayan wasan da yaranki
suke amfani da su. Kamar yartsana me
hoton tsiraici da makamantansu.

12. Ki koyawa ƴarki me shekara uku yadda ake wanke muhimman gurare a jiki, har da kirji kuma ki gaya mata kada ta bari kowa ya ta6a mata nan wajen da nan wajen.

13. Ki tabbatar duk wani hoto ko abin
amfani wanda zai 6ata tarbiyyar yaro kin nisanta shi da inda yaranki za su gani.

14. Duk sanda ƴarki ko danki s**a kawo miki ƙarar wani babba ya cire masa kaza ko ya taɓa masa kaza, to kada ki ɗau
matsalar da wasa.

A bi duk matakan da s**a dace don
tabbatar da
abinda ya faru.

15. Ku tuna Tarbiyya tana farawa ne daga
gida.

Allah yasa mu dace ya kuma bamu abokan zama na gari da kuma yaya masu albarka Ameen. Mu huta lafiya.
⭐ KOMI DA RUWANKA ⭐

🔴 Anya Vlodimir Zelenski mutun ne basira ?Tun lokacin da yaƙi ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, alamomi sun nuna cewa ...
25/10/2023

🔴 Anya Vlodimir Zelenski mutun ne basira ?
Tun lokacin da yaƙi ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, alamomi sun nuna cewa Rasha ba abokiyar gamin Ukraine ba ce. Dalilin wannan furucin shi ne, Rasha tana amfani da ƙarfin sojanta da makamanta ne saɓanin Ukraine da ke samun taimakon wasu ƙasashen duniya.
Saidai ƙasashen da suke iƙirarin taimakawa Ukraine suna yiwa Ukraine ɗin ingiza mai kantu ruwa ne. Komin nisan dare Gari zai waye. Kuma shugaban ƙasar Ukraine zai gane cewar shayi ruwa ne. Yakamata Shugaban ƙasar Ukraine ya dawo cikin hayyacinsa kafin Amurka da wasu ƙasashen su dai taimaka masa da kayan yaƙi.
Rishin basirar Zelenski ya sa bai gane tarkon ƙasashen duniya s**a ɗana masa ba.
KOMI DA RUWANKA

 'inShin kun gamsu da sakamakon Zaɓen jihar Alfawa Wanda hukumar zaɓen jihar ta Alfawa ta fitar inda tace jam iyyar Gugu...
22/10/2023

'in
Shin kun gamsu da sakamakon Zaɓen jihar Alfawa Wanda hukumar zaɓen jihar ta Alfawa ta fitar inda tace jam iyyar Guguwa Party ta Hajiya Rabi ita ta lashe zaben gwamna da akayi a jihar inda ta kayar da abokin hamayyar ta wato AVM Adnan na jam iyyar Haske Party?

Najeriya : Matsin tattalin arziƙi
21/10/2023

Najeriya : Matsin tattalin arziƙi

Haƙiƙa wanda Allah ya shiryar shi ne shiryayye. Duk wanda Allah ya ɓatar shi ne ɓatacce.Muna fatan Allah ya shiryar da ɓ...
21/10/2023

Haƙiƙa wanda Allah ya shiryar shi ne shiryayye. Duk wanda Allah ya ɓatar shi ne ɓatacce.
Muna fatan Allah ya shiryar da ɓatattu daga cikinmu ƴan Nijar. Allah ya haɗa kanmu. Allah ya kare ƙasar Nijar daga maƙiya na cikin gida da na waje.
Amin suma amin.
⭐KOMI DA RUWANKA⭐

19/10/2023

"Wasu sun so, wasu ko basu so ba"
A cikin birnin Tahoua muka ci karo da shi kenan jikin wata motar haya.
Kuma wannan rubutun yana a jikin wata takarda ne mai ɗauke da hoton janar Abdourahamane Tiani daga kowane gefen takardar daga tsakiyar takardar akwai wasu sojoji na majalisar ceton ƙasa (CNSP).
🔷A taku fahimta, wane saƙo hoton da rubutun su son isarwa?
⭐KOMI DA RUWANKA ⭐

15/10/2023

KwanaCasa'in zango na 10 kashi na 12 asha kallo Lafiya ❤️🙏
KOMI DA RUWANKA

13/10/2023

🔴Wane kalami ya fi burgeku?
😂😂😂😂😂

Muna sauraronku.
12/10/2023

Muna sauraronku.

To masu jin Faransanci gareku.
11/10/2023

To masu jin Faransanci gareku.

🔴 NijarBayan korar jakadan Faransa daga Nijar, yanzu luddai ya zo ga jakadiyar majalisar ɗinkin duniya.A wata sanarwa da...
11/10/2023

🔴 Nijar
Bayan korar jakadan Faransa daga Nijar, yanzu luddai ya zo ga jakadiyar majalisar ɗinkin duniya.
A wata sanarwa da offisoshin ministan harakokin ƙasashen wajen Nijar ya fitar, an sanar da bada wa'adin kwanaki 3 ga Madame Louise Aubin da ta tattara ƴan komatsanta ta fice daga ƙasar Nijar.
Madame Louise Aubin dai ita ce jakadiyar majalisar ɗinkin duniya ta dindindin kuma mai kula ayyukan agajin majalisar ɗinkin duniya a Nijar.
Sanarwar ta ce magatakardar majalisar ɗinkin duniya ya kasa riƙe matsayin sa tare da barin Faransa na amfani da shi wajen muzgunawa Nijar a tarrurukan ƙasa-da-ƙasa.
Hukumomin sojan Nijar sun ɗauki matakin ne domin rishin jin daɗin yadda babban magatakardar majalisar ɗinkin duniya ya ke yi wa Nijar soki burutsu alhali ba haka akeyi wa wasu ƙasashen ba.
An saka hannu a takardar sanarwar a ranar 10 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki.
🔴 Minene ra'ayinku akan wannan batun ?
⭐KOMI DA RUWANKA ⭐

🔴 Minene ra'ayinku akan furucin wannan ɗan siyasa ? Ko ku ƴan arewacin Najeriya zaku yi amfani da wannan shawarar?
10/10/2023

🔴 Minene ra'ayinku akan furucin wannan ɗan siyasa ? Ko ku ƴan arewacin Najeriya zaku yi amfani da wannan shawarar?

09/10/2023

KwanaCasa'in zango na 10 kashi na 11 asha kallo Lafiya ❤️🙏
KOMI DA RUWANKA

🔴 Matasan Nijar, mu farkaWani matashi ɗan Nijar mai ƙokarin zaburar da matasa ya yi kira ga wasu ƴan uwansa matasa da ya...
07/10/2023

🔴 Matasan Nijar, mu farka
Wani matashi ɗan Nijar mai ƙokarin zaburar da matasa ya yi kira ga wasu ƴan uwansa matasa da ya ke ganin sun fahimci rayuwa a kaikaice. Ga abunda matashin ya ke cewa:
"Koda Nijar zata zamo ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya, idan baka yi aiki ba to zaka dawwama cikin wahala kuma saï ka riƙa cewa hukumomi ne basuyi aikin komai. Saboda haka, aiki tuƙuru shi ne mafita" inji haziƙin matashin.
❗ Masu buƙatar a tallata musu wani abu ta wannan kafar zasu iya tintuɓar wannan lambar waya📱+22796606558
⭐KOMI DA RUWANKA ⭐

Har yanzu  ƙofofinmu a buɗe suke.
07/10/2023

Har yanzu ƙofofinmu a buɗe suke.

 Bari muga masu ƙokari.♦️Ga masu buƙatar tallace tallace, za'a iya lalibomu akan wannan lambar : +22796606558KOMI DA RUW...
07/10/2023


Bari muga masu ƙokari.
♦️Ga masu buƙatar tallace tallace, za'a iya lalibomu akan wannan lambar : +22796606558
KOMI DA RUWANKA

Idan haka ne minene ya sa wasu suke ganin har yanzu Bazoum zai iya dawowa akan karagar mulki ? Rishin tauhidi ne ko tosh...
06/10/2023

Idan haka ne minene ya sa wasu suke ganin har yanzu Bazoum zai iya dawowa akan karagar mulki ? Rishin tauhidi ne ko toshewar basira ce ke damun magoya bayan Mohamed Bazoum ?
♦️ Muna son jin ra'ayinku.

🔴 Tahoua: Komitin jaha mai goyan baya majalisar ceton ƙasa reshen jahar Tahoua ya fitar da sanarwa inda ake gayyatar ƴan...
06/10/2023

🔴 Tahoua:
Komitin jaha mai goyan baya majalisar ceton ƙasa reshen jahar Tahoua ya fitar da sanarwa inda ake gayyatar ƴan uwa musulmi wajen wata sabkar alƙur'ani mai girma da addu'oi.
A yayin wannan majalisi da zai gudana a babban masallacin Juma'a na garin Tahoua a yau ɗin nan da misalin ƙarfe 11 na safiya, za'ayi sabkar alƙur'ani mai girma da addu'oi ga ƙasar Nijar.
Bayan sabkar alƙur'ani, za'a yi addu'oi ga sojoji da s**a rasu a filin daga, da kuma Allah ya bada dawwamamen zaman lafiya cikin ƙasar Nijar.
Allah ya bada ikon halarta amin suma amin.
Sanarwar ta fito daga Komitin jahar Tahoua mai kawo goyan baya ga majalisar ceton ƙasa .
⭐KOMI DA RUWANKA ⭐

Barka da warahaka.
06/10/2023

Barka da warahaka.

🔴 Ko yanzu akwai wanda aka sanyawa takunkumin hana ƙara aure a Nijar kamar lokacin mulkin Mohamed Bazoum ?KOMI DA RUWANK...
03/10/2023

🔴 Ko yanzu akwai wanda aka sanyawa takunkumin hana ƙara aure a Nijar kamar lokacin mulkin Mohamed Bazoum ?
KOMI DA RUWANKA

Wai haka ne ? 😂😂😂😂
03/10/2023

Wai haka ne ? 😂😂😂😂

Barka da komawa cikin makarantu 🇳🇪
02/10/2023

Barka da komawa cikin makarantu 🇳🇪

01/10/2023

KwanaCasa'in zango na 10 kashi na 10 asha kallo Lafiya ❤️❤️🙏
KOMI DA RUWANKA

Daga sashen tallace tallace na Komi Da Ruwanka . Saï mun jiku.
01/10/2023

Daga sashen tallace tallace na Komi Da Ruwanka . Saï mun jiku.

Adresse

Tahoua

Téléphone

+22796606558

Site Web

Notifications

Soyez le premier à savoir et laissez-nous vous envoyer un courriel lorsque Komi Da Ruwanka publie des nouvelles et des promotions. Votre adresse e-mail ne sera pas utilisée à d'autres fins, et vous pouvez vous désabonner à tout moment.

Contacter L'entreprise

Envoyer un message à Komi Da Ruwanka:

Vidéos

Partager


Autres Site web d’actualités à Tahoua

Voir Toutes