21/11/2023
Labarin wani Inyamuri ne Mahaifiyarsa ta mutu, sai ya gayyato Abokansa domin ayi janazarta.
Bayan an gama sa Gawa a Akwati sai 'Yan Uwanta s**a sa Doya, Shinkafa da Nama, da dai sauran abubuwa na ampanin yau da kullum a cikin Akwatin.
Sai Bahaushe daya daga cikin Abokansa ya tambaya "Meyasa ake sa wadannan kayan?" Sai Inyamurin nan yayi Murmushi yace "Al'adarmu ce haka, Matacce yana yin doguwar tafia ne, Sbd haka yana buqatar kayan Abinci".
Sai Bayarabe daga cikin Abokansa shima ya saka N100,000 a cikin Akwatin yace "Idan Abincin ya qare sai ki sayi wani".
Sai wani Inyamuri daga Abokan nasa ya saka N50,000 yace "Ga wannan ki qara ko da wadancan ba zasu isheki ba".
Sai shikuma Bahaushen nan kawai yayi murmushi ya sa hannu a Aljihunsa ya dauko Cheque na banki ya rubuta N200,000 ya saka a Akwatin, sai ya dauke N150,000 din da Mutanen nan s**a saka a matsayin chanji, yace "Idan kin sauka kiyi withdrawing kudin nan sbd tafiya da Cash akwai hatsari ba za'a rasa Yan fashi a hanya ba" 🤒🤒🤒