04/01/2021
ANYI ZAGAYEN FARKO NA ZABEN NIGER
A ZAGAYE NA BIYU ZA'A RABA GARDAMA
Ranar asabar 02 ga watan fari na shekarar 2021 meladiya, hukumar zabe Mai zaman kanta CENI ta sanar da sakamokon zagayen farko na zaben Niger a babban dakin taro na palais des congrès. shugaban CENI Maitre Issaka Sounna, shine ya karanta jadawalin 'yan takara daga farko har karshe tare da bayyana makin ko wanne daga ciki su.
Jam'iyar PNDS tarayya ce akan gaba da kaso 39 cikin dari, saï Jam'iyar RDR CANJI ke bi mata da kaso 17 cikin dari, saï kuma sauran jam'iyu da s**a hada da(MNSD, MPR,MPN PJP Da sauran su) Da jimmillar kaso 44 cikin dari.
Daga bisani malam Issaka Sounna ya sanar da ranar 21 ga watan februyaru mai zuwa a matsayin ranarda za'a gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin Elhadji Mahamane Ousmane na RDR CANJI da Elhadji Bazoum Mahamed na PNDS tarayya.
WANE NE OUSMANE/WANE NE BAZOUM:
(1) Ousmane musilmi ne, Bazoum ma musilmi ne
(2)An haifi Ousmane a Jihar Zinder, an haifi Bazoum a Jihar Diffa
(3) Ousmane ya girma a jihar Zinder, Bazoum shima ya girma a jihar Zinder.
(4) Ousmane yanada shekara 71, Bazoum kuma yanada shekara 61
(5)Ousmane bahaushe ne, Bazoum kuma balarabe ne
(6) Ousmane ya taba rike mukamin shugaban 'kasa, Bazoum bai taba rikewa ba
(7) Ousmane ya karanci kimiyar tattalin arziki, shi kuma Bazoum ya karanci kimiyar nazari( falsafa)
MANAZARTA A BANGARORI DABAN DABAN SUNA CIGABA DA TOFA ALBARKACIN BAKINSU:
Cikin 'yan gogormayar farar hula, malam Nouhou arzika ne ya fara magantuwa. Nouhou yace, a zagaye na biyu zabe ne za'ayi tsakanin mutum da mutum ba tsakanin jam'iyun siyasa ba. halayya, Nagarta da mutumcin 'dan takarar, sune zasu banbanta 'dan Duma da kabewa.
Su Kuma 'yan siyasa, na bangaren Mahamane Ousmane da na bangaren Mahamed Bazoum dukkansu, tunaninsu ya karkata kan yadda zasu Kulla kawance mafi girma da zimmar Samu Nasara a ranar 21 ga watan februyaru.
Masu fashin bakin siyasa kuma ga yadda suke kallon lamarin:
(1) Idan Bazoum ya samu Nasarar hawa karaga, mulki kawai zai fara ba tare da ya fuskanci hayaniyar siyasa ba, saboda jam'iyarshi tanada cikekken rinjaye a majalissa. amma kuma Akwai masu ganin, damace kawai Bazoum zai samu, yayi abunda yake so, da karfin mulkin shi hade da na majalissa.
(2) Idan Ousmane yaci mulki, zai fuskanci tangal_tangal k**ar yadda hakan ta kansance a mulkinshi na shekarar 1994 farkon zuwan democradia, saboda jam'iyarshi Batada karfi a majalissar dokoki. amma kuma Abun dubawa anan shine, ita kanta PNDS tarayya batada rinjaye a majalissa, saï ta gama da na abokan kawance. Kuma dai, dalilin da zaisa sauran subi Bazoum, shine kuma zaisa subi Ousmane massaman Idan ya zama shugaban 'kasa.
A yanzu haka, Bazoum da mutanenshi suna buga kirgi da maki 39 cikin dari da jam'iyarsu ta samu a zagaye na farko. tunaninsu, ai Goyon bayan jam'iyu biyu ko ukku ya ishesu suyi Nasara da babban tazara.
ABUN LURA: Shima Mahamane Ousmane na jam'iyar RDR CANJI, yana iya lashe zabe a zagaye na biyu, saboda dalilai k**ar haka:
(1) Nagartar 'dan takara, ita ce zata saka a zabeshi a wannan mataki na zabe, kuma mafi yawan 'yan Niger na kollon Ousmane a matsayin mafi Nagarta.
(2) Maki 39% na zagayen farko na tarayya ne, ba na Bazoum ba. Abunda wannan maki yake nufi shine: kaso 39 cikin dari na 'yan Niger sun gamsu da mulkin shugaba Issoufou Mahamadou ba wai sun yarda Bazoum ya shugabancesu ba. ma'ana dai, a zagaye na biyu sabon kokowa ne duk bangarori zasu tunkara.
(3) Ousmane da Bazoum zasu raba kuri'un gabascin Niger, yayin da a yammacin kuma Ousmane zai iya wawushewa saboda yanada Goyon bayan manyan 'yan siyasan yamma irinsu Hama Amadou, ladan Tchana, Amadou Boubacar Cisse, Djibo max, da sauransu.
(4) tazarar da Ousmane ya ba Bazoum a garin Niamey da ma sauran manyan birane na Niger, na nuni da cewar mafi yawan 'yan Niger wadanda s**a san abunda yake tafiya yana dawowa a 'kasar, suna sha'awar canji.
(5) Irin haka ta taba faruwa a shekarun Baya, kuma ko wancan lokaci, Ousmane shine ya kasance jagora. A shekarar 1993, anyi zabe, Ousmane ne na biyu a zagayen farko, amma kuma shi yayi Nasara a zagaye na biyu tare da taimakon jam'iyar PNDS tarayya a wancan lokaci.
ABUN JIRA A GANI SHINE: KO TARIHI ZAI MAIMAITA KANSHI, KO BAZAI MAIMAITA BA?