06/08/2022
TAMBAYOYI 35 DA AKAIWA MALAN ABDULJABBAR KABARA AKOTU WANDA KUMA DASU AKA RUFE YIMASA TAMBAYAR
(T1) Azam da,akayi abaya ka fassara Kalmar fyade, kwace, auren dole, mu,amala tsakanin da namiji da mace, aharshen larabci inda kace fyade yana nufin (Al mubaja,ati ijbaran) auren dole kace (Azzawaju ijbaran) mu,amala tsakanin da namiji da mace kace (Atta,amuru bainarrujulu wal mir,ati) wadannan kalmomi kayi amfani dasu wajan fassara hadisai musamman hadisi Na 1365 amuslim Dana 5120 abikari hakane
(A) Eh hakane amma Na fassara da ma,ana ne bada lafaziba
(T2) Inaso anuna masa littafin danyaga hadisi 1365
(A) To ai wannan hadisin ba Wanda ake magana akansa bane lambardai dayace amma lafazin ba daya bane shi wannan yana maganane akan fitar annabi SWA kaibar
(T3) wato Ina nufin hdsn Nana safiya Wanda anass yarawato Wanda ka nasabtawa annabi SWA aikata wayancan kalmomi
(A) Ni bance hakaba cewa nai akwai ma,anar hakan inda anyi
(T4) To kawai inda aka rubuta Kalmar al mubaja,atu ijbaran nake so kanuna a hdsn
(A) Babu lafazin amma akwai ma,anar hakan
(T5) Acikin hdsn akwai inda aka ambaci azzawaju ijbaran
(A) A,a saidai ma,anar hakan
(T6) Duba wannan littafin sahihu bukari hds Na 5120 ka ganshi
(A) Eh Na ganshi
(T7) Shine hdsn dakace annabi SWA yabi wata mata kwararo ya biyamata bukata ta da namiji da mace
(A) Ni bance hakaba cewa nai mu,amalar da namiji da mace kuma ba abukari yakeba amuslim yake kuma iya binta kwararone aciki maganar mu,amala ta da namiji da mace bayanina ne danai bayan nagama karatu
(T8) Kamar yadda kasha fada cewa kai ma,ana kake fada nayi dai dai innace lafazin nakane
(A) A,a bakai dai dai ba
(T9) To lafazin nawaye
(A) Shi lafazin danai amfani dashi ba nawabane wani Na malaman Lugga ne wanikuma Na malaman sharhine
(T10) wadannan lafazan Na almubaja,atu ijbaran Dana azzawaju ijbaran ka tabbatar dacewa babusu acikin ruwayar hakane
(A) Eh amma akwai ma,anar su
(T11) To a ina kasamo lafazan
(A) To shidai almubaja,atu ijbaran ban nasabtawa waniba nace bayani nane
(T12) To sauranfa
(A) Duk suma ba lafazin saidai ma,anar
(T13) wadannan kalmomi dakai amfani dasu da Hausa fyade, kwace, auren dole, da mu,amala tsakanin da namiji da Mace hakane
(A) Bahaka bane kuma ni bance kwace ba cewa nai kwacewa dan da banbanci tsakanin kwace da kwacewa a Hausa duk dace alarabci sunansu daya
(T14) Ginshikim ilimin duk wani malami aduniya shine ilimin dayasamu agaban malaman dayai karatu agabansu Hakane
(A) Eh amma akwai kari Dan akwai ilimin da,ake samu ba takan malamaiba Dan Allah yanacewa و يعلمكم الله
(T15) to kana nufin wata baiwace akaima ko wahayi akema
(A) Wane wahayin kake nufi Dan shi wahayi nau,i biyune
(T16) Ni ilimina bai kai nanba ni bansan banbance banbance wahayiba
(A) To nidai ba aimim wahayi kuma banda yakinin Allah yana sanar dani ta wata hanya saidai abinda nasani shine Allah yaimin baiwar bahasi acikin littattafai kuma Allah ya horemim lafiyar yin batare da gajiyawaba saidai bacci ko yinwa
(T17) Malan nasiru kabara Babban malamine kowa ya shaida hakan masanine aharshen larabci ko akaratunsa Na Muslim antaba jin yace annabi SWA yayi fyade ko kwace ko auren dole ko mu,amala tsakanin da namiji da Mace da wata mata
(A) Bai taba cewa ba saboda azamaninsa babu wadannan matsalolin na farmaki ga annabi SWA da,akeyinsu a social media
(T18) Acikin karatunka Na audio daka gabatarwa wannan kotun innak tisabu li safiyatu kanat ala darajatul ula kafadi haka ko Baka fadaba
(A) Eh na fada amma bance da lafaziba
(T19) Inna fahimceka shi wannan larabcin babu shi Acikin hdsn Muslim kenan
(A) Eh babu shi da lafazi amma akwai ma,ana
(T20) Ko zaka iya fassara wa kotu
(A) Eh
(T21) Kenan innace iktisabu safiya nayi daidai innace anyiwa safiya fyade
(A) Eh kayi dai dai
(T22) Asanda kake karatunka kafadawa dalibanka da ma,ana kake ruwaya
(A) Eh na fadamusu
(T23) To yanzu in akakunna karatunka akaji sabanin haka kayarda kotu ta daukeka Mara gaskiya
(A) To itadai maganar ruwaya da ma,ana k**ar yadda yazo a alfiya duk inda kace haisu sarraha ya wadatarmaka agane da ma,ana kake ruwaya
(T24) Da za,a samu mutun daya ya sabawa mutun 10 yazo da wata ma,ana sabanin tasu ta sun za,a dauka hakane
(A) A,a hujjarsa za,a kalla inyafisu to tasan za,adauka
(T25) Littafin algaya yana daya saga cikin littattafan da kagabatarwa kotu to acikin wannan littafin ashafi na 52 ance Duk abinda aka rubutashi yakasance acikin littafin bukari da Muslim dangane da abinda ya kunsa aciki ba,a rawaitarsa da ma,ana hakane
(A) akwai amma yayi raddinsa a littafin kuma ya koma kan nawa ra,ayin
(T26) Kayarada alkali iyad yace yin ruwaya da lafazi shiyafi akan yi da ma,ana
(A) Bahaka yaceba kuma wannan maganar ta Sakawice bata alkali iyad ba shi alkali iyad cewa yai yak**ata arufe kofar yin ruwaya da ma,ana Dan kar Wanda bazai iya yin hakanba yazace zai iya k**ar yadda yafaru dawasu malaman ada da yanzu
(T27) Akwai littafin al kifaya Wanda shima yana cikim Wanda ka gabatarwa wannan kotun shafi na 577 aciki an nuna cewa ruwaya bil ma,ana an takaitatane akan canza wata kalma da wadda zatai dai dai da ita sai s**a bada misali k**ar haka
Jalasa da ka,ada duk suna nufin ya zauna alima da arafa duk suna nufin yasani to idan muka bi wannan ka,idar wacce Kalmar kamusanya acikin hds na 1365 tabaka Kalmar fyade kalama day tak mukeso
(A) Amsata ta daya su wayanda s**a shimfida wannan ka,idar ta jalasa da ka,ada suna maganane akan hdsn annabi bata wani sahabiba shikuma wannan hadisin na 1365 nakawo littattafai daya das**ace ba hadisin annabi bane maganar anass ce amsa da 1 kenan amsa ta 2 ita Kalmar ja,ala itqaha saqiha banine na fassara ta ahaka ba malaman das**a girmi bukari da Muslim su s**a fassarata s**ace wannan aure bai halattaba annabi bazai yishiba maliku Dan anas shine yai mata wannan fassarar Dan haka inaga shi yak**ata aiwa wannan tambayar da sauran tsarekunsa irin su Abu hanifa da sauransu baniba Dan shi yadorani akan wannan fahimtar
(T28) Adai cikin wannan littafin na alkifaya ankawo cewa mafi yawan malamai damasu bin diddigin hadisi sunce ba,a ruwayar hadisi da ma,ana sai dai akawo asalin hadisin babu dadi babu kari akwai wannan maganar
(A)Eh akwai ta amma tana maganane akan hdsn annabi shikuwa wannan hadisin 1365 nafada ba hds bane maganar anasce sannan kuma ya datse karashen maganar bai fadetaba Dan shi malamin aciketa dacewa kunzumin malamai sun tafi akan halaccin yin ruwaya da ma,ana
(T29) Malaman hds sunce abinda ake nufi da hadisi shine abinda aka jinganashi ga annabi nadaga zance ko aiki ko tabbatar da wani Abu da,akai agabansa ko suffa ta halitta ko ta dabi,a to abinda anas ya rawaita baya dagacikin haka
(A) Eh haka s**ace amma ai shi wannan hadisin na 1365 banine nace ba hadisin annabi bane malamai nakawo da s**a tabbatar ba hds bane maganar anass ce dagacikinsu akwai alkali iyad haka aini yafada haka ibn hajar yafada
(T30) Acikin shaidarka daka bayar agaban wannan kotu kace imamu malik yace wannan aure bai ingantaba kuma annabi bazaiyishiba sai kajinginawa imamu malik kace an rawaito acikin littafin Al mu,ulim ko hakane kafada
(A) Eh hakane nafada amma da kari ba,iya littafin Al mu,ulim nfadaba nakawo wasu littattafan amma idai maganar bai halattabane to tanacikin umdatul kari na Aini mujalladi na 20, har za,a wuce atafi tambaya ta gaba sai alkali yace yana bukatar adauko umdatul kari Dan akaranta duk dacewa shi lauya mai gabatar da tambaya have baya bukata amma kasancewar alkali ne yakeso yasa aka dauko littafin kuma kabawa Wanda ake kara yakaranto abinda akeso, aciki yake ashafi na 114 maliku yace wannan aure bai halatta ba
(T31) Adai cikin wannan littafin ashafin na 114 daga kasa cigaban maganar da kafara sai dashi malan dahawi yanancewa wannan Abu baya halatta gani inba annabi ba zai iya yin aure batare da sadaki ba sai dai yantawa sabosa Allah madaukakim sarki ya halatta masa aure batare da sadaki ba wannan itace cikon maganar daka fara Baka karasaba akwaita aciki ko babu
(A) inada amsa 2 tafarko ni cewa nai malik yace shikuma yatafi maganar dahawi kuma ni duk awayanda nace sunkore maganar nan ban ambaci sunan dahawi ba sannan shi aini bayan yakawo duk sabane sabanen akarshe ya rushe wanna auren na khaibar yakuma tabbatar da na banu kuraiza Wanda nakawo anan Wanda shine aure mai kyau da annabi SWA yaiwa Nana safiya kuma nima akansa nake
(T32) Akwai littafin Attaubih shafi na 228 Wanda shima wannan littafin ka dogara dashi agaban wannan kotun hakane
(A) Hakane
(T33) Ashi wannan littafin annuna karara ra,ayin imamu malik ne shi wannan aure kususiyace ta annabi akwai wannan maganar
(A) Wannan maganar akwaita saidai nafada wahami alkali iyad yasamu maganar dahawi ce dagacikin ikmalil mu,ulim ibn mulaqqib yadaukota kuma akarshe shima ya rushe auren khaibardin da aure razina yarufe Wanda nima akansa nake
(T34) Wannan ijaza da kake son kagabatar ta mahaifinkace sheikh nasiru kabara hakane
(A) A,a tawace
(T35) Ko zaka iya nuna mana inda aka ambaci sunanka aciki
(A) Amsa ita ijaza nau,i takwasce rawi ko sheyinka zai iya dauka yabaka batare da an fadi sunaka acikiba ita ake kira MUNAWALA Dan haka ba sharadine ba sai anga sunanka acikinta danhaka tinda ya dankamin ta tabbata tawa kuma dukkan yayansa ba Wanda yabawa maisuna acikinta yanda yabani haka yabasu
Da wannan tambayace lauyoyi masu gabatar da kara s**ace sun rufe yin wayannan tambayoyi nasu
# Dashi glee radio online