10/03/2024
Muhimmanci shan zobo a lokacin Azumin Ramadan.
Zobo na daya daga cikin abubuwan sha da ake anfani da su a cikin watan azumin Ramadan, wanda yake kunshi da muhimman sinadirai masu yawa wadanda ke ba shi fa'idodi iri-iri.
Daga cikin fa'idodin amfani da zobo ga mai azumi sun hada da.
β Saukar da hawan jini: Zobo yana taimakawa wajen magance cutar hawan jini, sannan kuma baya ga haka, yana aiki a matsayin diuretic.
β Rage matakin cholesterol na jini: musamman ga mutanen dake fama da ciwon s**ari wato diebetes.
β Rage s**arin jini: Zobo ana daukar sa daya daga cikin abin sha da ake amfani dashi a Ramadan mai matukar tasiri ga masu ciwon s**ari, amma yana da kyau a kula da amfani dashi idan kuna shan magungunan rage s**arin jini.
β Maganin Cushewar ciki: Bugu da kari, yana da tasiri sosai akan wasu matsalolin tsarin narkewar abinci kamar su rashin cin abinci da ciwon ciki, sannan kuma yana taimakawa wajen inganta narkewar abinci.
β Rage kiba: Zobo yana iya iya taimakawa wajen rage kiba ta hanyar rage adadin yawan s**ari da jiki ke diba daga ciki.
β Kula da lafiyar hanta: Zobo yana aiki don bada rigakafi da magance wasu cututtukan hanta saboda yana Ιauke da antioxidants properties.
β Rage ciwon haila: yana kuma taimakawa wajen sassaita hormonal balance a cikin jiki da kuma alamomin da ke da alaqa da haila.
β Rage kishirwa: Lokacin da mutum yasha zobo mai sanyi, yana taimakawa wajen rage Ζishirwa da kuma sanyaya jiki da hana shi bushewa.
Don shirya zobo, ana zuba shi rabin kofi a cikin kwanon da aka cika shi da tafasasshen ruwa, a jika shi na tsawon rabin sa'a, sannan a tace shi, sai a sha da zafin sa ko kuma a sanyaya shi, anso ayi amfani da zuma kadan wajen kara masa zaki.
Duk da fa'idodin da zobo yake dasu, ya kamata a yi taka tsantsan yayin amfani da shi a cikin waΙannan lokuta:
β Lokacin ciki da shayarwa
β Lokacin da ake shan magungunan masu saukar da s**arin jini
β Lokacin hormonal treatment
β Da wadanda idan sun sha zobon yake haifar musu da mats